HausaTv:
2025-05-04@17:42:05 GMT

Kissoshin Rayuwa : Imam Al-Hassan (a)

Published: 4th, May 2025 GMT

117-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Mutahhari ko cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Romi ko kuma cikin wasu littafan, da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a wannan shirin.

//… Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin kissa ko sirar Imam Al-Hassan Al-mujtaba limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) kuma da na farko ga Fatimah (S) diyar manzon All..(s) kuma jakansa(s) na farko da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun tsaya inda muka bayyana aka kashe Khalifa na uku wato Uthman bin Affan, bayan da yan tawaye daga kasashen Masar da Kufa da Basra na kasar Iraki suna shigo Madina, mun kuma bayyana yadda, Khalifa Uthman ya sabawa Alkawalin da ya rubutawa mutanen kasar Masar kan cewa zai yi aiki da littafin All..da kuma sannar manzon All…(s), a lokacinda yah au membari ya fadawa mutanen, mutanen Masar sun koma kasarsu ne bayan sun fahinci cewa abubuwan da suke tuhumarda da shi ba gaskiya bane. Munji yadda muryoyi suka yi ta tashi a mallacin yana ce masa Uthman ka ji tsoron All… daga nan sai ya tsorata a sauri ya shiga gidansa.

A nan ne ya rabutawa Mu’awiya dan Abusufyan wasika yana bukatar taimakon sojojin da zasu kare shi, mu’a wi ya ki, sannan ya tuwa walinsa mai suna Yaziz Alkasri a sham din, amma karkashin ikon Ma’wiya, sai mu’awiya ya bashi umurnin ya je da rundunar sa ya tsaya a wani wuri da ake kira Zi-Khashab kusa da madina sai ya sami umurninsa. Alkasri ya je ya tsaya da rundunarsa a wajen madina har aka kashe Khalifa Uthman.

Sannan munji cewa Muhammad dan Abubakar yana daga cikin wadanda suka shiga gidan Uthman suka kashe shi. Sannan sun haka a bisneshi sai a hashu Kaukab, wata makanartan yahudawa, don basu dauke shi musulmi ba. Amma a lokacinda Mu’awiya ya kwace Khalifanci daga Imam Al-Hasan(a) ne ya hada makabartan Hashu-Kaukab cikin Bakiyya.

Daga karshe mun musanta wasu abubuwan da wasu malaman tarihi daga cikin har da Taha Hussain wadanda suke ganin Imam Alhassan dan Aliyu dan Abitlib (a) ya na matukar somn khalifa Uthman kuma ya ci gaba da kareshi kafin mutuwarsa har bayan an kashe shi.  Mun bayyana cewa wannan karya ce bai faruba. 

Ammam me ya faru bayana an kashe Khalifa Uthman? Musulmi suna bukatar sabon Khalifa wanda zai jagoranceta, Khalifa na farko ya rubuta takarda a matsayin wasiya ga musulmi kan cewa ya nada Umar sannan Umar ya kafa shuran mutane 6 da su zabi daya daga cikinsu a matsayin Khalifa sai suka zabi Uthman, amma shi Khalifa Uthman kasheshi aka yi, bai sami damar yin wasiyya ko kuma kafa shura ba.

Don haka kwanaki suna tafiya, duk duniya ta ji an kashu shugaban musulmi amma bata ji an nada wani ba. Wannan halin yana da hatsari, don makiya suna iya amfani da wannan damar su farwa daular musulunci.

Sai dai musulmi musamman wadanda suka ga yadda khalifofin da suka gabata suka yi ma’amala da Imam Ali (a), sun ga irin matsayin da yake da shi, musamman abinda ya shafi ilmi da shawarori, dukkan khalifofi sai da sun bukhaci tallafin imam Ali a duk lokacinda al-amura suka rikici masa. Sai dai ba ko yaushe ne suke karban nisaharsa ba. Musamman sun san yadda Khalifa Uthman ya sha kiransa don ya kubutar da shi daga matsalolin da ya sa kansa.

Kafin a kasha shi, khalifa Uthman ya kirashi, ya taimaka masa y araba shi da yan tawaye, ba bashi shawara, yayi aiki da shi sannan ya sake warware, alkawalinsa. Har sai ya kai ga, Imam Ali (a) yace masa daga yau ba zan sake amsa kiranka ba. A cikin wannan halin ne aka kashe Uthman.

Don haka bayan kashe Khalifa Uthman sahabban manzon All..(s) Muhajirun  da Ansar da kuma bakin da suka zo daga masar, Kufa da sauransu,  daga cikinsu har da Talha da Zubair, sun taru sun je gidan Imam Ali (a) suna cewa: Ya baban ! an kashe wannan mutum (suna nufin Uthman) kuma dole ne mu sami shugaba, a yau bamu ga wanda ya cancanci wannan matsayin ba sai kai. Sun ambatun falalolinsa, wadanda suka hada da sabikansa a addinin musulunci, da kusancinka ga manzon All..(s)….

Imam Ali (a) ya ki amsa bukatarsu, ya ce, bana bukatar shugabancinku, duk wanda kuka zaman a yarda da shi. Sai suka fada da babban murya: Ba ma son wani ba kai ba.

Sun yi kokari sun gamsar da shi sun kasa, daga nan sai suka tafi. Amma jami’an tsaro wadanda ake kira shurda, sun gudanar da taro na musamman don tattauna matsalar rashin shugabanci a cikin musulmi bayan labarin kashe Khalifa ya wastu. Daga karshe sun tsa kan cewa dole ne sai raguwar majalisar shura wacce Umar ya kafa, kuma ta zabi Uthman su fitar da khalifa a tsakaninsu ko kuma su kashesu gaba daya.

Kuma wadanda suka rage a majalisar sun hada da Imam Aliyu dan Abitalib, Talha dan Ubaidullahi, Zubair dan awwam da kuma Sa’ad dan Abiwakkas. Shugaban shoran Abdurrahman dan Rasu a zamanin khalifancin Uthman.

A lokacinda mutane suga haka sai suka sake zuwa wajen Imam Ali (a) suka bayyana masu ga halin da ake ciki, ga kuma abinda shudah ko kuma jami’an tsaro suka fada na cewa dole ku fitar da khalifa a tsakaninsu ko kuma su kasheku.

Amma sai Imam ya ce masu:

Ku barni ku zabi wani ba ni ba. Sannan ya ku mutane ku san cewa muna fuskantar wani al-amari mai fuskoki da dama, kuma masu launuka daban daban, (al-amari wanda zukata ba zasu sami nutsuwa bam, kuma hankula ba zasu tabbata a kansu ba.

Sannan ya yi shiru na wani lokaci sai ya ce: Ku sani idan na amsa bukatarku, zai dora ku a kan abinda na sani ne, kuma b azan saurari zancen wani mai zance ba, ko zargin mai zargi ba, amma idan kun barni ta ni daya ne daga cikinu, mai yuwa zan zama mai biyyanku ga wanda kuka zaba.

Sai suka fada da babban sauka ba zamu rabu da kaiba sai mun yi maka bai’a. Sai yace masu, to ku bani wannan daren inyi tunani kan bukatarku zuwa gobe zan baku amsa. Da haka suka tafi.

A lokacinda garin ya waye sai mutane suka taru a cikin masallacin manzon All..(s), a lokacin da Imam (a) ya karaso masallaci, ya hau kan mimbarin Manzon All…(a) yayi khuduba wacce a cikin say a bayyana cewa, zai tabbatar da adalci a cikinsu zai kuma raba dukiyar al-ummah a tsakaninsu ba tare da nuna fifiko tsakanin mutane ba…. Har zuwa karshen sa.

Farkin wanda ya fara masa bai’a shine talha dan ubaidullah, wanda yake da hannu wacce ta shanye, sannan Zubair dan Awwam. Sannan sauran sahabban manzonAll..(S).

Haka ma banu umayya wadanda suka rage a Madina sun yi masa bai’a, tare da sharari wadanda bai amince da su ba.

Walid dan Utbah ne ya jagoranci banu umayya suka yai masa bai’a sannan ya shardantawa Imam Ali (a) kan cewa ya barmasu dokokin da suke hannunsu, ya kuma nemo wanda ya kashe Uthman ya daukam masu kisasi, Imam bai amsa masa ee ba, sai dai yace idan yaga lazimi ne yayi haka zai yi. Batun dukiyoyin da suka sata kuma ya bayyana cewa sai ya karbo hakkin All..hallin musulmi daga wadanda suka sace kudadensu.

Dukkan sahabban manzon All..(s) a madina sun basa bai’a suna kuma farin ciki da kasancewarsa shugabansu. Farin cikin da ya bayyana a fili wasu daga cikinsu sun rera wakokin suna yabonsa suna kuma bayyana falalolinsa.

Akwai wasu sabban da basu yi masa bai’a ba, amma kuma bai tilasta masu yin haka ba, ba kamar yadda shi akeson a tilasta masa bai’a a lokacinda ya yi jayayya da khalifa na farko ba. Har ya kai ga ana barazanar za’a kasheshi ba.

Sannan mun san cewa khalifa na biyu Khalifa na farko ne ya rubuta takarda kafin ya yi wafati inda ya ambaci Umar a matsayin Khalifansa. Duk da cewa da dama daga cikin sahabban sun yikari amma ya ki sauyawa har ya mutu.

Sannan khalifa na biyu ya kafa shura na mutane 6 da umurnin su zabi daya daga cikinsu, wanda ya raba kan musulmi. Amma Imam Ali (a) shi kadai ne mutane suka zama a matsayin Khalifa, bisa kuma yardarsa ba wanda ya tilsta masu.

Bil’hasali ma shi yi ki amincewa da zama khalifa, amma suka takura masa har sai da ya amince, shi ne ya kafa  masu sharuddan sa na khalifanci suka yarda sannan ya amince ya karbi jagoranci  sabanin duk wadanda suka zo gabaninsa.

Banda haka, duk da cewa akwai sauran mambobi na shura Al-umariyya da suka rashe a bayan kissan Khalifa Uthman kamar yadda muka bayyana a baya, amma sais hi suke so. Su hudu ne suka rasge, wato shi amirul Muminin, Talha, Zubai da kuma Sa’a dan Abi wakkas. Biyu daga cikinsu sun rasu, wato Abdurrahman dan Awf da kuma Uthman dan Affan.

Kuma dukkan wadanda suke rage cikin shoran sun masa mubaya’a sai Sa’adu dan Abi wakkas, wanda wasu da dama suna ganin hasada ce, tasa hakan, saboda yana ganin kansa ya cancanci khalifancin, amma mutane basu zo wajensa ba, basu neme shi.  Wasu suka ce da aka tambaye shi me yasa yaki bai’a ga Aliyu sai yace, ba zai yi bai’a ga wanda aka yi sabani a kansa ba.

Zamu ga wayi aka yi sabani a kansa nan gaba tsakanin Khalifofin da suka gaba ceshi.

Sai dai duk da haka a lokacinda Sa’adu dan Abiwakkas ya hadu da Muawiya dan Abi sufyan, sannan ya umurceshi da ya zagi Imam Ali (a) ya ki yin haka, sai mu’awiya ya tambaye shi dalili, ya kawo dalilai uk da ya say a ki zaginsa, daga cikin ya kawo cewa, abinda ya faru a yakin khaibara inda manzon All..(s) yace: Zan bada gobe ga wanda yake son All..da manzonsa (s) sannan All..da manzonsa suke sonshi sai da gari ya waye sai ya bawa Ali(a)  tutar.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: wadanda suka

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Yi Alƙawarin Kwato Dazuzzuka Daga Hannun Ƴan Bindiga

Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin ƙwato dazuzzuka da sauran yankuna a Arewa-Maso-Yamma da sauran sassan Nijeriya, yayin da yake jawabi a wata liyafa da tsofaffin shugabannin Katsina suka shirya. Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ƙara amfani da fasahar sa ido don yaƙar ta’addanci da ƴan fashi.

A cewar sanarwar kakakin shugaban ƙasa, Tinubu ya ce: “Za mu zuba hannun jari a fasaha domin kwato dazuzzuka. Tsaro batu ne na ƙasa baki ɗaya, ba na yanki ko gunduma kawai ba.” Shugaban ya kuma yi alƙawarin inganta filin jirgin sama na Katsina domin samar da ayyukan yi.

Gidauniyar TY Buratai Ta Yi Kira Ga Tinubu Ya Ƙarawa Ma’aikata Albashi Kasar Sin Ta Goyi Bayan Rawar Da Hukumar IAEA Ke Takawa Wajen Warware Batun Nukiliyar Iran Ta Hanyar Diflomasiyya

Gwamna Dikko Radda na Katsina ya bayyana cewa jihar ta kafa wani tsarin tsaro na musamman don tattara bayanan sirri, yana mai cewa inganta filin jirgin saman zai samar da ayyukan yi ga mutane 2,700. Tsohon gwamna Aminu Masari ya yaba wa shugaban saboda naɗa ‘yan asalin jihar a muƙamai mabambanta a gwamnatin tarayya.

Tinubu ya kuma yi godiya ga gwamnonin jihohin Kaduna, Jigawa, Borno, Benue, Yobe, Sokoto da Kwara da suka halarci bikin auren ‘yarsa da ƙaddamar da ayyukan gwamnati a Katsina. Ya kuma yaba wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin mutum mai gaskiya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kissoshin Rayuwa : Imam Al-Hassan (a) 113
  • Kissoshin Rayuwa Imam Alhassan (a) 118
  • Maniyyata Daga Turai Akan Dawakai Sun Isa Kasar Saudiyya Domin Yin Aikin Hajjin 2025
  • Dakataccen Gwamnan Ribas Ya Dawo Daga Hutun Makonni Biyu A Kasar Waje
  • Tinubu Ya Yi Alƙawarin Kwato Dazuzzuka Daga Hannun Ƴan Bindiga
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 116
  • Gobarar rumbum makamai Maiduguri da Matakan da ya kamata a ɗauka — Ƙwararru
  • Atiku Ne Rikitacce Ba Tinubu Ba
  • Gobarar rumbum makamai a Borno: Abin da ya kamata a yi