Ba a samu jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kaduna (PPRO), DSP Mansir Hassan ba da aka tuntube shi har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda ’yan Boko Haram suka sha da ƙyar a hannun tawagar Gwamna Zulum

Jami’an tsaro da ke rakiyar tawagar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun daƙile wani harin Boko Haram a kusa da garin Gujba a Jihar Yobe.

Gwamnan da tawagarsa na kan hanyarsu ta komawa Maiduguri daga Biu lokacin da suka haɗu da ’yan ta’addan, wanda hakan ya tilasta musu tserewa bayan musayar wuta.

Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga ƙara kuɗin cajin ATM Ba abin da zai faru idan aka tsige Fubara – Wike

Bayanai sun ce dakarun tawagar sun ƙwato bindigogi, harsasai, babur, tare da ceto wasu fasinjoji da aka sace.

Wani direba da aka ceto, Malum Ari, ya bayyana yadda maharan suka tare hanyar: “Sun karɓe motata suka tilasta mana kwanciya a ƙasa.

“Amma da suka hango tawagar gwamna, sai suka firgita suka tsere. Wani daga cikinsu ya faɗi a kasa sau biyu kafin ya tsere saboda tsananin firgici.”

Wani fasinja da aka ceto ya koka kan yadda hare-haren suka zama ruwan dare: “Boko Haram na tare hanya da tsakar rana. Ba mu da kwanciyar hankali kwata-kwata.”

Wannan na zuwa ne kwana uku bayan da ’yan ta’adda suka kai hari gari Gujba, inda suka kashe wani ɗan sa-kai mai suna Modu Bulama, tare da ƙone gidaje da shaguna.

Wani jami’in tsaro da ya shaida lamarin ya ce, “Waɗannan ’yan ta’adda sun ƙara samun ƙarfi sosai. Suna kai hare-hare ba tare da tsoro ba. Dole a ɗauki ƙwararan matakai don tabbatar da tsaro.”

A baya-bayan nan ne mayaƙan Boko Haram suka sace wani Farfesan Jami’ar Soji ta BIU da ke Jihar Borno (NAUB) da wasu fasinjoji.

Haka kuma sun sace wani alƙalin kotun Borno, wanda daga baya suka sako shi bayan biyan kuɗin fansa mai yawa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Pakistan Ta Zargi Kasashen Afghanistan Da India Da Hannu A Garkuwa Da Jirgin Kasa Na Sojoji
  • ‘An Kwashe Shekaru Ana Kashe Kudaden Yaran da ba a ma Haife su ba a Nijeriya’
  • Sama da ‘Yan Mata 74,000 Suka Amfana Shirin AGILE Cash A Kano
  • ’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Kaduna, sun sace matasa 3
  • Yadda Azumi Yake Sa Tsoron Allah
  • Muƙarraban Uba Sani ne suka sace tsohon Kwamishina na – El-Rufai
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 10 da raunata 2 a Kaduna
  • ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga a Abuja
  • Yadda ’yan Boko Haram suka sha da ƙyar a hannun tawagar Gwamna Zulum
  • Iran da Belarus sun rattaba hannu kan daftarin bunkasa hadin gwiwar tsaro