Sojoji sun kama jami’an tsaro da ke haɗa baki da ’yan ta’adda
Published: 4th, May 2025 GMT
Hedikwatar tsaro ta tabbatar da kama wasu jami’an tsaro huɗu da ke taimakawa ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da wasu jami’ai biyu na rundunar haɗin gwiwa da ke aiki tare da sojoji domin yaƙar ’yan ta’addar.
ISWAP sun kai wa sojoji hari a Yobe An kama masu garkuwa da mutane 3 da kuɓutar da wasuA cewar Darakta mai kula da harkokin yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, an kame sojojin ne a wani samame da aka yi tsakanin ranakun 26 zuwa 29 ga watan Afrilu a cikin ƙananan hukumomin Bama, Kukawa, da Madagali.
Ya ce, suna daga cikin waɗanda suke taimakawa ’yan ta’adda huɗu da sojojin suka kama.
Kangye ya nuna damuwarsa kan cin amanar da suke yi, ya kuma gargaɗi kwamandojin da su wayar da kan jami’ansu kan ayyukan da za su kawo cikas ga ƙoƙarin da sojoji ke yi.
“A wani samame da aka gudanar tsakanin ranakun 26-29 ga Afrilu, 2025 a ƙananan hukumomin Bama, Kukawa, da Madagali na Jihohin Borno da Adamawa, sojoji sun kama wasu ’yan ta’adda guda huɗu da ke kai kayan aikin ga mahara, abin baƙin ciki, an tabbatar da cewa biyu daga cikinsu na cikin rundunar haɗin gwiwa.”
Don haka dole ne kwamandoji su wayar da kan jami’an rundunar haɗin gwiwa da su daina haɗa kai da wasu ko ƙarfafa ayyukan ta’addanci da ke da ikon yi wa ayyukanmu zagon ƙasa,” in ji Kangye.
A wani samame kuma, Kangye ya ce sojoji tare da haɗin gwiwar dakarun haɗin gwiwa sun kai farmakin da suka haɗa da sintiri na yaƙi, samame, da aikin share fage a ƙananan hukumomin Gwoza da Dikwa da Bama da Chibok da Gujba da Geidam da kuma Yunusari.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Adamawa Kukawa rewa maso Gabas haɗin gwiwa
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda sojoji suka kashe manyan ’yan bindiga 5 a Zamfara
Sojoji sun hallaka wasu manyan ’yan ta’adda tare da yaransu masu yawan gaske a wata arangama a Ƙaramar Hukumar Talata Mafara da ke Jihar Zamfara.
Shugabannin ’yan bindiga da suka haɗa da Auta Jijji da Dankali da Sagidi da Kachallah Rijaji da kuma Kachallah Suza sun sheƙa lahira ne a yayin musayar wuta da sojojin a ranar Alhamis.
Kakakin Birget na 1 ta Sojin Ƙasa ta Najeriya, Kyaftin Suleiman Omale, ya ce sojojin sun ƙaddamar da aikin ne bayan samun rahoton cewa ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Mai Kwanugga inda suke ta ƙone gidajen al’umma.
Ya bayyana cewa, “dakarun da ke sintiri suka yi artabu da dandazon ’yan bindiga, inda a yayin musayar wuta suka kashe shugabannin ’yan bindiga biyar da wasu da dama.”
Yadda aka yi bikin yaye sabbin matuƙa jiragen Rundunar Sojin Saman Najeriya Ra’ayin Jama’a kan ziyarar Tinubu Katsina Sarki Sanusi II ya naɗa sabon Galadiman Kano da wasu 4Ya ƙara da cewa sojojin sun bi sawun ’yan bindigar da suka tsere inda suka ƙwato manyan bindigogi guda shida da bama-bamai da kuma harsasai iri-iri.
Washegari kuma a yayin da sojojin ke ci gaba aiki, mazauna yankin sun mika musu wasu ƙarin makaman da ’yan bindigar suka tsere suka bari.
Kyaftin Omale ya bayyana cewa fararen hula biyu sun samu raunin harbi a yayin musayar wuta amma suna samun kulawa a asibiti, a yayin da ake ci gaba a aikin gamawa da ragowar ’yan ta’addan.