Wata mata ta auri maza biyu a lokaci guda a Kano
Published: 6th, May 2025 GMT
An gurfanar da wata matar aure a gaban kotun Musulunci kan zargin ta da auren maza biyu a lokaci guda a Jihar Kano.
Wannan lamari ya faru ne wata shida bayan auren matar mai suna Harira Muhammad Tudun Murtala da mijinta na farko mai suna Sagiru Shu’aibu Tudun Murtala.
A yayin zaman Kotun Musulunci da ke zamanta a Post Office Malam Sagiru ya shaida wa alkali cewa kasncewar ba tare suke zaune da matar tasa ba, wata rana ya je gidanta sai kawai ya iske ta tare da wani mutum a gan gadon aurensu, lamarin da ya sa ya sanar da makwabta abin da ke faruwa.                
      
				
Bayan gurfana da ita a gaban kotu, Harira ta musanta cewa akwai aure tsakaninta da mijin nata na farko, lamarin da ya sa alkali ya umarce ta da yin rantsuwa da Alkur’ani, amma sai ta janye kalamanta.
NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ‘Yan Gwagwarmaya Ke Shiga Tasku A Najeriya? ’Yan bindiga sun kashe matar aure bayan karɓar N10m kuɗin fansaA nasa bangaren, mijinta na biyu, mai suna Bello Abdullahi ’Yankaba ya shaida wa kotun cewa aurenta ya yi a kan sadaki naira dubu dari kuma wani kawunta mai suna Abdullahi Umar ne waliyyin aurensu.
Bayan sauraron bayanansu, alkalin kotun, Khadi Munzali Tanko Soron-Dinki, ya ba da umarnin a zurfafa bincike kan lamarin sa’annan a tsare matar da mijin nata na biyu a gidan yari, zuwar ranar 16 ga watan Mayu da za a ci gaba da sauraron shari’ar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: mijinta na farko
এছাড়াও পড়ুন:
Abba ya umarci a riƙa gudanar da taron tsaro a ƙananan hukumomin Kano
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci shugabannin dukkan ƙananan hukumomin jihar da su riƙa gudanar da tarukan tsaro akai-akai domin ƙarfafa zaman lafiya da kariyar rayuka da dukiyoyin al’umma.
A cewar wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Abba ya jaddada muhimmancin tattara bayanan sirri da musayar su a tsakanin al’umma da jami’an tsaro domin magance matsalolin da ke addabar yankuna.
Barazanar kawo hari abin ɗaga hankali ne ga duk ’yan Nijeriya — Peter Obi Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a KanoMatakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin rahotannin hare-haren ’yan bindiga a wasu ƙananan hukumomin da ke kan iyaka da Jihar Katsina da sauran yankunan da ke fama da matsalar tsaro.
Gwamnan ya bayyana ƙananan hukumomin Shanono, Tsanyawa, Tudun Wada, Doguwa da Gwarzo a matsayin wuraren da ke buƙatar kulawa ta musamman saboda barazanar tsaro da ke ci gaba da tasowa a can.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin Kano za ta ci gaba da haɗin gwiwa da jami’an tsaro domin tabbatar da cewa an hana ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifi samun mafaka a cikin jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne dakarun Rundunar Sojin Najeriya suka daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Shanono da ke Jihar Kano, inda suka yi nasarar hallaka 19 daga cikin ’yan ta’addan.
Bayanai sun ce sojojin ƙarƙashin rundunar haɗin gwiwa ta Operation MESA sun fafata da ‘yan bindigar ne da yammacin ranar Asabar, bayan samun bayanan sirri kan ayyukansu a yankunan Unguwar Tudu da Unguwar Tsamiya da Goron Dutse.