An Kammala Zaben Kananan Hukumomi A Kasar Lebanon A Yau Lahadi
Published: 4th, May 2025 GMT
An kamala gudanar da zabe a yankin jabal Lebanon na kasar Lebanon a safiyar yau Lahadi har an kuma an fara irge.
Tashar talabijin ta Almanar ta kasar ta bayyana cewa an bude rumfunan zabe tun karfe 7 na safe, kuma an kamala zaben da yamma.
Sannan ma’aikatar cikin gida da kuma kananan hukumomi ta bayyana cewa mutanen da suka fito don kana kuri’insu ya kai kimani kashi 45.
Yankin Jabal Lobnon dais hi ne yanki mafi yawan mutane a kasar kuma yanki ne wanda hizbullah take da masu goyon baya da dama.
Matsalolin daya dayan daya, wadanda suka hada da rashin kudade da rashin gwamnati ya hana a gudanar da zabubbuka kananan hukumomin wanda yakamata a gudanar tun shekara ta 2016.
Har’ila yau yakin tsakanin kungiyar Hizbullah da kuma HKI suna daga cikin al-amura da suka kawo jinkirin zaben.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Fim Mai Taken 731 Na Tunatar Da Jama’a Muhimmancin Kiyaye Zaman Lafiya
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya amsa tambayar da aka yi masa game da fara nuna fim din kasar Sin mai taken 731 a sassan kasar, inda ya ce, irin wannan fim na tunatar da jama’a muhimmancin koyon darussa daga tarihi, da kokarin wanzar da zaman lafiya.
Kakakin ya ce, Sin kasa ce dake bude kofa ga kasashe waje, kuma mai hakuri da tsaro. Ana maraba da jama’ar sassan kasa da kasa, ciki har da na Japan, su shigo kasar Sin don yin yawon bude ido, da karatu, da kasuwanci da kuma rayuwa. Haka kuma, Sin za ta ci gaba da tabbatar da tsaron baki ’yan kasashen waje dake zaune a sassanta. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp