“Mun rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira da ke cikin Maiduguri. Yanzu haka saura biyu da ba na hukuma ba. Mun riga mun dawo da kashi 75 na ‘yan sansanin Muna gida, saura kashi 25 za su koma cikin kwanaki masu zuwa.”

Kowane iyali sun samu tallafin abinci, kayan gini da kulawar lafiya.

Haka kuma, kowane magidanci mace ko namiji za a ba shi Naira 100,000, yayin da matan gidan za su ƙara samun Naira 50,000 don taimaka musu da buƙatunsu na yau da kullum.

Za a Ƙara Inganta Cibiyar Koyo Sana’o’i a Gidan Gyaran Hali

Tun da safiyar ranar Litinin, Gwamna Zulum ya kai ziyara gidan gyaran hali na manyan laifuka da ke Maiduguri.

Ya ce za a inganta cibiyar koyar da sana’o’i da ke gidan don taimaka wa fursunoni su koyi sana’a da za su yi amfani da ita bayan an sake su.

“Manufar ɗaure mutum a gidan gyaran hali ita ce gyara halayensa, ba wai tsare shi kawai ba. Wannan ba zai yiwu ba sai akwai kayan aikin koyarwa da ake buƙata” in ji Zulum.

“Za mu duba wasu daga cikin fursunonin da ke da ƙananan laifuka, mu gani ko akwai yiwuwar a sake su bisa doka.”

Zulum ya samu rakiyar ɗan Majalisar Tarayya, Bukar Talba, shugaban ma’aikatansa na riƙon ƙwarya, mai ba shi kan harkokin addini da wasu jami’an gwamnati.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Yan Gudun Hijira Boko Haram Hari

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta a Borno

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ta kai hare-hare ta sama a yankin Rann, wani gari da ke Jihar Borno, wanda ake zargin ya zama mafakar ’yan ta’adda.

Wannan aiki na cikin shirin Operation Haɗin Kai, kuma ya yi sanadin hallaka ’yan ta’adda da dama.

’Yan damfara 2 sun shiga hannun ’yan sanda a Yobe PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa ’yan ta’addan sun fara guduws bayan yunƙurinsu na kai hari sansanin sojoji ya ci tura.

Da suka hangi jiragen yaƙi na sojojin sama, sai suka fara tserewa daga maɓoyarsu, amma an kashe da yawa daga cikinsu ta hanyar ɓarin wuta.

Wani mazaunin Rann ya ce da farko sun yi zaton cewa ’yan ta’addan ne za su kai musu hari saboda ƙarar da suka ji kamar ta bindiga.

Daga baya ne suka fahimci cewa sojoji ne ke gudanar da aiki.

Mai magana da yawun Rundunar Sojin Sama, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya tabbatar da harin a cikin wata sanarwa.

Ya ce sun samu bayanan sirri da suka tabbatar da inda ’yan ta’addan suke, kuma bayan sojojin ƙasa sun gano su suna guduwa, sai aka aike jiragen yaƙi da suka kai musu farmaki.

Harin ya daƙile barazanar ’yan ta’addan, kuma ya dawo da zaman lafiya a yankin.

Ejodame, ya ƙara da cewa wannan aiki ya nuna irin sadaukarwar da Rundunar Sojin Sama ke yi wajen kare dakarunta da kuma daƙile duk wata barazanar ’yan ta’adda.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Nazari Kan Dalilin Da Ya Sa Kajin Gidan Gona Ke Samar Da Ƙananan Ƙwai 
  • ASUU na shirin sake tsunduma yajin aiki
  • Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram a Borno
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Mayar Da Dalibai 184 Da Suka Zo Hutu Daga Cyprus
  • Sojojin Sama Sun Yi Lugudan Wuta, Sun Kashe Ƴan Ta’adda A Borno
  • Sojoji sun yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta a Borno
  • Tashin Gurneti Ya Hallaka Yara Uku A Borno
  • Yara Uku Sun Gamu Da Ajalinsu A Wani Tafki A Borno
  • An Biya Diyyar Naira Miliyan 277 Ga Wadanda Aikin Ginin Masallacin Gumel Ya Shafa
  • Jami’an Tsaro Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara, Sun Ƙwato Bindigogi