Iragchi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Babban Sakataren MDD Antonio Guterres
Published: 4th, May 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Argchi ya zanta ta wayar tarho da babban sakataren MDD Antonio Guterres inda ya fada masa inda aka kwana a tattaunawar da kasarsa take da Amurka ba kai tsaye ba.
Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya nakalto Arigchi yana fadawa babban sakatarin kan cewa akwai bukatar bangarorin biyu su yi gaske don cimma yarjeniya wacce kowa ya amince da ita.
Tattaunawar dai tana nuna irin yadda Iran ta fifita tattaunawa da kuma hanayr diblomasiyya kan shiga wasu rigingimu wadanda basa da amfani.
Aragchi ya fadawa Goterres kan cewa Iran tana bukatar ta ci gaba shirinta na makamashin nukliya ta zaman lafiya. Sannan a dauke mata takunkuman zaluncin da aka daura mata.
Ya kuma kara da cewa Iran tana daga cikin kasashen da suka sanya hannu a yarjeniyar NPT wacce ta bata samar amfanin da makamacin nukliya ta zaman lafiya. Banda haka irana tana son ta shiga tattaunawa da kasashen Turai don warware matsalar shirin makamashin nukliya ta kasar ba tare da an harba harsashi go guda ba.
Ana bangare babban sakataren MDD ya yaba da tunanin tattaunawa ba kai tsaye ba , sannan ya taya kasar bakin ciki kan gobarara da ta tashi a tashar jiragen ruwa ta Ali Ra’ei a bandar Abbas.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce Kasar Oman Ce Ta Bukaci Dage Zaman Tattaunawan Iran Da Amurka
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: An dage zaman tattaunawan Iran da Amurka ne bisa shawarar kasar Oman
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi nuni da cewa: Ministan harkokin wajen kasar Oman ne ya sanar da sauyin lokacin zaman tattaunawan ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, yana mai bayanin cewa, dage shawarwarin ya zo ne bisa shawarar ministan harkokin wajen kasar, kuma za a sanar da wata sabuwar rana daga baya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da manema labarai cewa: An canja ranar da za a gudanar da zaman shawarwarin ba na kai tsaye ba na gaba tsakanin Iran da Amurka, wanda aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 3 ga watan Mayu a birnin Roma na kasar Italiya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya yi nuni da cewa: Ministan harkokin wajen kasar Oman ne ya sanar da wannan sauyi, yana mai bayanin cewa, dage shawarwarin ya zo ne bisa shawarar ministan harkokin wajen kasar, kuma za a sanar da wata sabuwar rana daga baya.