Aminiya:
2025-05-05@14:22:27 GMT

Umaru ’Yar’adua da shugabannin Najeriya da suka rasu a kan mulki

Published: 5th, May 2025 GMT

A yau 5 ga watan Mayu 2025 tsohon Shugaban Kasa Marigayi Umaru Musa ’Yar’adua ya cika shekaru 10 da rasuwa.

’Yar’Adua wanda ya rasu a bayan dogaruwar jinya yana daga cikin daidaikun zaɓaɓɓun shugabannin Najeriya da talakawa ke kewar su, saboda kyakkyawan kamun ludayin mulkinsa.

Sai dai kuma an lura cewa shugabannin da suka fi samun irin wannan yabo daga talakawan Najeriya, ba su fiye yin tsawon kwana ba, a kan mulki suka rasu.

Zuwa yanzu, shugabannin Najeriya huɗu ne suka mutu a kan mulki, kuma dukkansu daga yankin Arewa.

Lakurawa: Yadda mafarauta 13 suka gamu da ajalinsu a Sakkwato NAJERIYA A YAU: Abin da ke kai matasan Najeriya ci-rani wasu ƙasashen Afirka Ya kamata a zuba jari a harkar noman rani — Zulum

Biyu daga cikinsu zaɓaɓɓun shugabanni ne — Marigayi Sa Abubakar Radawa Ɓalewa, wanda shi ne Fira Ministan kasar na farko, sai kuma Marigayi Umaru Musa ’Yar’adua.

Ragowar biyu kuma shugabannin mulkin soja ne — Janar Murtala Ramat Muhammad da kuma Janar Sani Abacha, waɗanda su ma suke shan ya yabo.

Zababbun shugabanni 1- Abubakar Tafawa Ɓalewa

Rasuwar Marigayi Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa na daga cikin abubuwan da suka fi girgiza Najeriya bayan samun ’yancin kanta.

Sojoji ƙarƙashin Janar Aguiyi Ironsi ne suka yi wa Tafawa Ɓalewa juyin mulki a karon farko a tarihin Najeriya

A juyin mulkin na ranar 15 ga watan Janairu, 1966, sojoji suka sace shi daga gidansa da ke Legas, inda bayan kwanaki aka tsinci gawarsa a gefen hanya.

Juyin mulkin da irin kisan gilla da masu juyin mulkin suka yi masa da wasu mnyan amuƙarraban gwamnatinsa irin su Firimiyan Jihar Arewa, Alhaji Sa Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, ya bar babban tabo a a tarihin Najeriya, wanda daga bisani ya haifar da yaƙin basasa.

Tsare-tsaren Fira Minista Tafawa Balewa wanda zamanin ya ratsa mulkin mallakan turawa zuwa bayan samun mulkin kan Njaeriya ya mayar da hankali ne wajen gina kasa da kuma daga darajar Najeriya a idon dunya.

Gwamnatinsa ce ta samar da kundin tsarin mulkin kasa da ya mayar da Najeriya Jamhuriya a 1963 sabbab ta soke tsarin sarautu da kuma ofishin Gwamna-Janar a tsarin shugabancin Najeriya.

Ta bayar da fifiko ga hadin kan al’ummar kasa ba tare da la’akari da bambancin kabila ko yanki ba. Haka kuma, kasancewarsa malamin makaranta, ya mayar da hankali ga inganta ilimi da fadada samuwar sa ga ’yan Najeriya.

Domin bunkasa tattalin arziki da ci gaban kasa, Tafawa Balewa ya ba da muhimmanci ga fannin noma da kasuwanci da masana’antu da kuma jawo masu zuba jari daga ketare, inda ta gina matatar mai ta farko a shekarar 1966 sannann ta samar da Madatsar Ruwa ta Kainji, domin noman rani da samar da wutar lantarki, da kuma samar da matatar mai da kuma kamfanin sarrafa tama da dai sauransu.

2- Umaru Musa ’Yar Aduwa

A ranar 5 ga watan Mayun shekarar 2010 Najeriya ta girgiza da labarin rasuwar shugaban kasarta, Alhaji Umaru Musa ‘Yar’Adua bayan fama da jinya.

Tun kafin zamansa shugaban an yi masa dashen koda, lamarin da ya zama abin ce-ce-kuce a lokacin mulkinsa, inda a watan Satumban 2009 ya tafi kasar Saudiyya domin duba lafiyarsa, daga bisani aka sanar cewa yana fama da ciwon zuciya.

Dadewarsa yana jinya a kasar wace ta tare ya mika mulki ga mataimakinsa a matsayin mukaddashin shugaban kasa ba ta haifar da rudani inda watan Fabrairun 2010 Majalisar Dokokin Najeriya ta yi amfani da karfinta ta ayyana mataimakinsa, Goodluck Jonathan a matsayin mukaddashin Shugaban Kasa.

A ranar 24 ga watan Fabarairu aka dawo da shi gida, amma Mukaddashin Shugaban kasa ya ci gaba da jan ragamar gwamnati.

Bayan watanni biyu, a ranar 5 ha watan Mayu Allah Ya yi masa cikawa, wanda haka ya ba damar rantsar da Jonathan a matsayin shugaban kasa.

Duk da rashin lafiyar Shugaba Yar’Adua ya samu farin jini a wurin al’ummar Najeriya musamman saboda manufofin gwamnatinsa 7 na 7 point Agenda, wadda ta mayar da hankali wajen inganta makamashi da wadata kasa da abinci da samar da arziki da inganta ilimi da tsaro da sufuri da mallakar kasa.

Ya yi zarra a dabi’arsa ta bin doka inda ya zaman shugaban kasa na farko da ya bayyana kadarorinsa ga al’ummar kasa. Uwa uba ya ba da umarnin sakin kudaden Gwamnatin Jihar Legas da gwamnatin Obasanjo ta ki saki daga Asusun Gwamnatin Tarayya

Haka kuma kokarinsa wajen magance matsalar rashin tsaro da fasa bututun mai a yankin Neja Delta, inda ya bullo da shirin afuwa da tallafi tubabbun tsagerun yankin da suka ajiye makamai, har ya samar da ma’aikatar Neja Delta domin bunkasa yankunan da ayyukan hakar danyen mai suka lalata.

Wani abin da ya fi daukar hankali shi ne yadda ya amince da cewa akwai kura-kurai a zaben da ya kawo shi kan mulki, inda ya dauki gabarar yin gagarumin garambawul ga tsarin zaben Najeriya karkashin jagorancin mai shari’a Muhammad Lawal Uwais.

Kazalika gwamnatinsa na dauki gabatar kare martaba da tallata Najeriya a idon duniya da kuma ba da muhimmanci ga kula da jin dadin al’ummar kasar.

Shugabannin mulkin soji 3-Janar Murtala Muhammad

Wanda ya hau mulki a shekarar 1975 bayan kifar da mulkin Janar Yakubu Gowon ya rasu a wani kazamin hari da aka kai wa ayarin motocinsa a ranar 13 ga Fabrairu, 1976.

Mayan abubuwan da ake tuna gwamantin Murtala da su sun hada da shirin dauke Babban Birnin Tarayya Abuja daga Legas kuma kirkirar sabbin jihohi daga 12 zuwa 19 da nufin share hawayen kananan kabilu da kuma samar da daidaito.

Ya kuma kaddamar da shirin noma na Operation Feed the Nation domin habaka samar da abinci a kasa da rage dogaro da kasashen waje.

Kazalika ya dauki matakai domin magance cin hanci da rashawa inda da kafa hukumar karbar korafe-korafen jama’a. Haka kuma ta yi gagarumin garambawul da nufin tsarkake aikin gwamnati inda sallami dubbabn ma’aikata a kokarinta na kawar da cin hanci a tsarin aikin gwamnati.

Gwamnatin Murtala ta bullo da tsarin da  ya ba wa ’yan Najeriya damar mallaka da shiga a dama da su a harkokin tattalin arziki, wanda ya ba su samar mallakar kamfanoni da a baya baki ke mallaka.

Ya kuma taka rawar gani wajen gani kasashen Kudancin Afirka irin su Angola sun samu ’yancin kai, kamar yadda ta yi fito-na-fito da wariyar launin fata a kasar Afirka ta Kudu.

4- Janar Sani Abacha

Rasuwar tsohon shugaban kasa na mulkin soji, Janar Sani Abacha ta girgiza Najeriya, inda aka dauki tsawon shekaru ana tababa game da ainihin musababbin mutuwarsa, inda wasu ke zargin kashe shi aka yi ta hanyar guba, wasu ke ganin jinya ce, wasu kuma na ganin salim-alim ya rasu.

Rasuwar Abacha a ranar 8 ga watan Yuni 1998 ta zi a wani lokaci mai muhimmanci a tarihin Najeriya, inda kasar ke shirin komawa tsarin dimokuradiyya, bayan sama da shekaru 10 a hannun gwamnatocin sojoji. Hasali ma, a wannan lokaci, shi kansa Abacha yana shirin ajiye kaki ya shiga a fafata da shi a zaben da ke tafe.

Gwamnatin Abacha ta bar tahirin da ba zai gogu a zukatan ’yan Najeriya a sakamakon kafa Asusun Man Fetur (PTF) da ta kafa, bayan karin farashin man fetur, inda aka kafa hukumar domin yin amfani da kudin a aka samu wajen ayyukan raya kasa.

Ayyukan da hukumar PTF ta gudanar a daukacin jihohin Najeriya, birni da karkara, an dade ana cin moriyar su bayan rasuwar Abacha.

Daga fannin kiwon lafiya zuwa fannin ilimi zuwa samar da ruwan sha zuwa ginawa da gyaran tituna da sauransu, ayyukan PTF sun kasance masu inganci kuma bin guba misa.

Kazalika a zamaninsa, duk da takunkumin da manyan kasashe suka kakaba wa Najeriya, amma ya rage hauhawar farashin kayayyaki a cikin gida, da kuma basukan da ake bin Najeriya a kashen waje daga dala biliyan 36 zuwa biliyan 27. Ya ninninka yawan kudaden da ke asusun ajiyar kasashen waje na kasar daga dala miliyan 494 zuwa biliyan 9.6 sannan ya daidaita farashin canjin dala na tsawon lokaci a kan N80.

Gwamnatinsa ya murkushe masu tayar da kayar baya a cikin gida da kuma barazanar kasashen waje, sannan ta kama tare da tatsar wasu manyan mutane da suka durkusar da wasu bankunan kasuwanci.

Abacha ya kara yawan jihohi daga 30 zuwa 36, baya ga shirinsa na Vision 2010 mai nufin sanya Najeriya a sahun manyan kasashe a shekarar ta 2010.

A zamanin mulkinsa, ya takaita tafiye-tafiyensa ne zuwa kasashen Afirka, sannan ya yi tsayuwar daka wajen samar da tsaro a kasashen nahiyar da ke fama da yakin basasa, musamman a kasashen Laberiya da kuma Saliyo inda ya murkushe juyin mulki tare da dawo da zababben shugaban kasar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Najeriya Yar adua

এছাড়াও পড়ুন:

Rudiger Zai Yi Jinyar Watanni Biyu

Barcelona ce ta yi nasara a wasan na El Clasico da cin 3-2, sannan ta lashe Copa Del Rey na 32 jimilla ranar Asabar. Daga baya Rudiger ya nemi afuwa, sai dai hukuncin laifin da dan wasan tawagar Jamus ya aikata, za a iya dakatar da shi daga buga wasa hudu zuwa 12, amma sakamakon hakurin da ya bayar aka rage hukuncin zuwa wasanni hudu. Real Madrid, wadda take ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki hudu tsakani da Barcelona mai jan ragama, za ta karbi bakuncin Celta Bigo ranar Lahadi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Trump Na Shan Suka Kan Wallafa Hotonsa Na AI Sanye Da Kayan Fafaroma
  • Kiwon Lafiya: Jihar Kwara Ta Bayyana Yadda Karancin Likitoci Ke Kawo Mata Cikas
  • ISWAP sun kai wa sojoji hari a Yobe 
  • Tinubu Ya Yi Alƙawarin Kwato Dazuzzuka Daga Hannun Ƴan Bindiga
  • Bankin AfDB zai zuba jarin $650m a Nijeriya a duk shekara
  • Rudiger Zai Yi Jinyar Watanni Biyu
  • Tinubu zai yi shekara takwas yana mulki – Afenifere
  • HKI Ta Kai Hari Kan Jirgin Ruwan Tawagar Masu Rajin Kare Hakin Bil’adama Dauke Da Agaji Zuwa Gaza
  • An Kama Wani Babban Jami’in Sojan Kasar Burtaniya A Najeriya Tare Da Zarginsa Da Shigo Da Makamai