Abin da ya hana ni cika alƙawarin da na yi wa ma’aikata — Gwamnan Sakkwato
Published: 4th, May 2025 GMT
Gwamnan Sakkwato, Dokta Ahmad Aliyu ya bayyana ƙarara cewa gwamnatinsa ta kasa cika alƙawarin da ta yi wa ma’aikatan gwamnatin jihar kusan shekara ɗaya kenan.
Gwamnan ya bayyana hakan a yayin bikin Ranar Ma’aikata da aka gudanar a makon da ya gabata.
Lakurawa sun kashe ’yan bijilanti 11 a Sakkwato Ya kamata a zuba jari a harkar noman rani — ZulumYa bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a biya kuɗin goron sallah babba na naira dubu talatin-talatin da ya ba da umarnin a bai wa ma’aikatan ƙananan hukumomi amma wasu suka yi sama da faɗi da kuɗin.
Gwamna ya bai wa ma’aikata tabbacin nan ba da jimawa ba za raba kuɗin ga waɗanda ke da haƙƙi kamar yadda tsarin biyan kuɗin sallah ya kasance a shekarar da ta gabata.
A yayin bikin sallah babba na shekarar da ta gabata ce gwamnan ya amince a baiw a kowane ma’aikaci a jihar naira dubu 30 don sauƙaƙa musu bukin sallah babba, sai dai har zuwa yanzu da yawan ma’aikatan da malaman firamare ba su samu nasu ba.
Sai dai baya aka sanar da ma’aikata da malaman ƙananan hukumomin cewa an yi sama da faɗi da kuɗin da aka ce a ba su.
Gwamna ya bayyana cewa ya ba da umarnin a fitar da miliyan 500 duk wata haɗi da wasu naira miliyan 300 domin biyan waɗanda suka yi ritaya daga shekarar 2023 zuwa yanzu.
Ya ba da sanarwar ƙaddamar da shagon sauki na Amadun Alu domin sayar da kayan masarufi a cikin sauƙi ga ma’aikata.
Ya yi kira ga ma’aikata su zama masu kula da aiki da sadaukarwa domin ci gaban jihar.
A jawabinsa, shugaban ƙungiyar ƙwadago ta jihar, Abdullahi Aliyu ya yaba wa gwamnan kan fifita walwalar ma’aikata.
Shugaban ya gode wa gwamna kan biyan mafi ƙarancin albashi na naira dubu 70 ga ma’aikata.
“Mun samu farin ciki ƙwarai musamman yadda na jagoranci tantance ma’aikata domin fitar da na bogi a tsarin biyan ma’aikata.”
A cewarsa, kwamitin ya samu ci gaba sosai, inda aka cire ma’aikatan bogi da ke cin kuɗin mutane ba da haƙƙi ba.
Ya ce ƙungiyarsu za ta ci gaba da taimakon gwamnati don samun nasara.
Masana a jihar suna ganin gwamna bai da wani dalilin rashin biyan kuɗin ga ma’aikata, lamarin da suka bayyana a matsayin kasawa ce ƙarara daga ɓangaren gwamnatinsa.
Sun bayyana cewa “gwamnati ta kasa ne kawai ba don haka ba umarnin gwamna ba wasa ba ne da har wani zai kasa biyayya gare shi, hakan ya sa gwamnan da kansa bai bayar da wani dalili ba saboda ya kasa ga cika alƙawarin da ya ɗauka.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Sakkwato wa ma aikata
এছাড়াও পড়ুন:
HOTUNA: Yadda aka yi Jana’izar Sarkin Gudi na Yobe bayan rasuwarsa a Abuja
An yi jana’izar Marigayi Sarkin Gudi da ke Jihar Yobe, Alhaji Isa Bunuwa Madugu Ibn Khaji, ranar Juma’a a Abuja, inda ya rasu a wani asibiti bayan fama da jinya.
Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya ranar Juma’a ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar wajen hakartar taron.
Sanarwar da Mamman Mohammad daraktan yada labarai na gwamna Buni ya fitar ta ce, gwamnan da ke halartar wani taro a Abuja ya yanke ziyarar tasa domin halartar jana’izar marigayi Sarkin da kansa.
Gwamna Buni ya samu rakiyar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Alhaji Chiroma Buba Mashio, Sanata Ibrahim Mohammed Bomoi, Sanata Musa Mustapha, da ’yan Majalisar Wakilai.
Sauran sun haɗa da sakataren gwamnatin jihar, Baba Malam Wali, ’yan majalisar dokokin jihar, da kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, shugabannin kananan hukumomi, Sarakuna, Malamai, sauran jama’a.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma yi kira ga al’umma da su tsaya tsayin daka, kuma su yafe wa juna.
Gwamna Buni ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin babban rashi ga dangi, Masarautar Gudi, Jihar Yobe da kuma Najeriya baki xaya.