’Yan fashi sun yi wa mafarauta kisan gilla a Bauchi
Published: 5th, May 2025 GMT
’Yan fashi sun harbe mafarauta da fararen hula kimanin 19 har lahira a Karamar Hukumar Alƙaleri ta Jihar Bauchi.
A yayin ziyarar da ya kai wurin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya ba da umarnin yin cikakken bincike da kuma tura karin jami’an tsaro yankin.
Mazauna kauyen Mansur sun ce an kashe ’yan farauta guda tara da kuma fararen hula guda goma, kuma an yi jana’izar ’yan bangar a kauyen Mansur kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Kakakin ’yan sanda na jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce kwamishinan ya tattauna da masu ruwa da tsaki a yankin, inda ya buƙaci jama’a kwantar da hankalinsa, ya kuma kasance a cikin shiri, tare da bai wa ’yan sanda goyon baya wajen gudanar da binciken su.
Kwankwaso: Abba ya mayar wa Baffa Bichi martani Umaru ’Yar’adua da shugabannin Najeriya da suka rasu a kan mulki NAJERIYA A YAU: Abin da ke kai matasan Najeriya ci-rani wasu ƙasashen AfirkaWakil ya ce, “A ranar 4 ga watan Mayu, 2025 mun samu rahoto cewa tawagar hadin gwiwar mafarauta daga Duguri da Gundumar Gwana, da ke sintiri a kan hanyar Duguri, Mansur, da dajin Madam da ke kan iyakar jihar Bauchi da Filato, sun yi araba da ’yan fashi, inda a arangamar aka kashe mutane da dama daga bangarorin biyu.
“Mun tura tawagar jami’an tsaro wurin, inda suka gano gawarwakin jami’an tsaro da fararen hula daga kauyen Sabuwar Sara, wadanda ’yan fashin suka harbe su a yayin da suke kokarin tserewa daga harin suka mutu.
“Rundunar ta tura tawaga ta musamman domin kamo duk masu alaƙa da wannan aika-aika.”
Ya kuma ba da tabbacin cewa za a yi bincike cikin gaskiya da adalci domin gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban ƙuliya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda yan fashi mafarauta
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Kadu Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Wa Hukumomi Da Jami’an Falasdinu
Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum.
Dangane da sanarwar da Amurka ta fitar ta kakaba takunkumi kan jami’an hukumar kare hakkin Falasdinawa da mambobin kungiyar ‘yantar da Falasdinu, Guo Jiakun ya bayyana cewa, Sin ta kadu da hakan, kuma tana nuna takaici da rashin fahimta cewa, Amurka ta yi watsi da kokarin da kasashen duniya ke yi na samar da zaman lafiya ga Falasdinu. Kuma kasar Sin ta dage wajen goyon bayan tsari mai adalci ta al’ummar Falasdinu don maido da halastaccen hakkin al’ummar, kuma za ta ci gaba da yin namijin kokari a wannan fanni tare da sauran kasashen duniya.
Dangane da umarnin da shugaban Amurka Trump ya bayar na kara haraji kan kasashen duniya, Guo Jiakun ya bayyana cewa, matsayin kasar Sin na adawa da cin zarafi na kudaden haraji ba zai canza ba, domin babu wanda zai yi nasara a yakin haraji, kuma ra’ayin amfani da kariyar cinikayya yana cutar da muradun kowane bangare.
Dangane da rahotannin da ke nuni da cewa Amurka ta kaddamar da hare-hare ta yanar gizo kan kasar Sin, Guo Jiakun ya ce, wannan ya fallasa munafuncin Amurkan na koken “kama barawo” a fannin tsaron intanet. Kuma kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace don kare tsaron intanet.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp