’Yan PDP 6 a Majalisar Tarayya sun koma APC
Published: 6th, May 2025 GMT
Mambobin Jam’iyyar PDP shida a Majlisar Wakilai daga Jihar Delta sun sauya sheka zuwa Jam’iyya APC.
Kazalika wasu biyu daga Jihar Enugu sun sauya sheka daga Jam’iyyar adawa ta LP zuwa PDP.
Shugaban Majalisar Wakiliai, Abbas Tajuddeen, ne ya sanar da hakan bayan dawowar majalisar daga hutu a ranar Talata.
Shugaban Majalisar ya bayyana cewa ’yan majalisar sun yanke shawarar sauya sheka ne sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyun nasu a matakin jiha da kuma kasa.
Wadanda sauka sauya sheka zuwa APC su ne: Victor Nwokolo, Julius Pondi, Thomas Ereyitomi, Nicholas Mutu, Okodiko Jonathan, da kuma Nnamdi Ezechi. Wadanda suka bar LP zuwa PPD su ne Mark Obetta da kuma Dennis Nnamdi.
Idan ba ma manta ba a kwanakin baya ne Gwamnan Delta, Sheriff Francis Orohwedor Oborevwori, da tsohon gwamnan jihar kumwa tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa Ifeanyi Okowa, da wasu kusoshin PDP suka sauya sheka zuwa APC.
Ana yawan samun sauya sheka a Majalisar Wakilai daga jam’iyyun adawa zuwa APC mai mulki, a wannan majalisa ta 10.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Wakilai sauya sheka daga PDP sauya sheka
এছাড়াও পড়ুন:
Trump Na Shan Suka Kan Wallafa Hotonsa Na AI Sanye Da Kayan Fafaroma
Shugaban Amurka, Donald Trump na shan suka daga wasu jagororin mabiya ɗarikar Katolika, saboda wallafa hotonsa da ya samo daga manhajar ƙirƙirarriyar basira ta AI, sanye da kayan fafaroma.
Mista Trump ya wallafa hoton ne a shafukan sada zumunta na fadar White House.
Matakin na zuwa ne yayin da mabiyar ɗarikar Katolika, ke shirin zaɓen sabon fafaroma, bayan alhinin da suke ciki na rasuwar jagoran ɗarikar, Fafaroma Francis, wanda ya mutu ranar 21 ga watan Afrilu.
Taron mabiya ɗarikar Katorlika na birnin New York ya zargi Shugaba Trump da zolayar Addininsu.
Wallafa hoton na zuwa ne kwanaki bayan da shugaban ya zolayi wani mai bayar da rahotonni da cewa ”ina son zama fafaroma”
Ba Trump ne shugaban Amurka na farko da aka taɓa zarga da zolayar mabiya ɗariƙar Katolika ba.
A shekarar da ta gabata ma an zargi tsohon shugaban Amurka, Joe Biden lokacin da ya sanya hannu kan alamar kuros a lokacin wani gangamin masu goyon bayan zubar da cikin a Tampa da ke jihar Florida
A ranar Laraba mai zuwa ne fadar Vatican za ta fara shirye-shiryen zaɓen sabon fafaroma.