Sojojin Sudan Da ‘Yan Tawayen Kasar Suna Ci Gaba Da Gwabza Fada A Wasu Saasan Kasar
Published: 5th, May 2025 GMT
Ana ci gaba da gwabza kazamin fada a yammacin Sudan tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na kasar
Jiragen saman yaki marasa matuki ciki na dakarun kai daukin gaggawa sun kai hare-hare kan sansanin sojin sama na Osman Digna da ke gabashin Sudan, inda suka janyo bullar gobara a ma’ajiyar harsasai.
A yammacin Sudan na ci da wuta tare da hare-haren jiragen saman yaki marasa matuka ciki da kuma luguden harsasai, kuma sojojin sun janye daga yankin Nahud da ke yammacin Kordofan, kafin nan gaba su sake dawowa, kamar dai yadda suka yi a jihar Al-Jazirah da ke tsakiyar Sudan, a cewar wata majiyar soji.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
HKI Ta Tabbatar Da Halakar Sojojinta 2 A Yankin Rafa Na Zirin Gaza
Gwamnatin HKI ta bada sanarwan halakar sojojinta biyu da kuma jikatan wasu alokacinda suke bincike da kuma kokarin shiga wani rami na karkashin kasa a inda wani bom ya tashi ya kashe su ya kuma raunata wasu.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakafen yana labaran yahudawan na fadar haka a safiyar yau kuma wadanda aka rutsa da su sun hada da Captain Noam Ravid, dan shekara 23 a duniya da kuma Staff Sergeant Yaly Seror, dan shekara 20 a duniya.
Labarin ya kara da cewa hatsarin ya faru ne a jiya asabar, sannan wasu sojoji biyu daga rundunar Yahalom sun ji rauni.
Tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ne aka fara yakin tufanul Aksa, inda sojojin yahudawan tare da taimakon kasashen yamma suka fara kisan kiyashi ga Falasdinawa a yankin, wanda ya kaiga shahadar mutane 52,495 ya zuwa yanzu. Sannan wasu 118,366 suka ji rauni.
An dan tsaida yaki daga ranar 19 ga watan Jenerun wannan shekara har aka kai wata marhala sai HKI ta tsaida aiwatarda yarjeniyar. Sannan ta sake komawa yaki.
An kashe sojojin yahudawa fiye da 850 daga ciki har da sojojin kasa 414 a yankin na Gaza.