Aminiya:
2025-05-05@10:46:58 GMT

Lakurawa: Yadda mafarauta 13 suka gamu da ajalinsu a Sakkwato

Published: 5th, May 2025 GMT

Tawagar haɗin gwiwar jami’an tsaro na aikin gano gawarwakin wasu mafarauta da mayaƙan Lakurawa suka kashe a yankin Ƙaramar Hukumar Tangaza da ke Jihar Sakkwato.

Ana fargabar Lakurawa sun yi garkuwa da wasu daga cikin mafarautan da suka fito daga ƙananan hukumomin Tangaza da Gwadabawa, bayan sun faɗa tarkon ’yan ta’addan

Aminiya ta ruwaito cewa mayaƙan Lakurawa sun kashe mafarauta 13 a wani harin kwanton ɓauna tare da tayar da bom a wani turken sadarwa a Jihar Sakkwato.

’Yan ta’addan sun kai wa mafarautan farmaki ne a yayin a yayin da suka fita farautar shekara-shekara a Dajin Hurumi da ke Ƙaramar Hukumar Ta gama, wanda ya samu halartar mafarauta daga sassa daban-daban.

Aminiya ta samu labarin cewa mafarautan sun yi arba da ’yan ta’addan ne da misalin Azahar na ranar Alhamis, duk da cewa hukumomi sun gargaɗe su, gane da barazana rashin tsaro da ake fama da shi a yankin.

Majiyoyi sun bayyana cewa farautan da ake ɗauke da bindigogi harbi-ruga, tare da rakiyar karnukansu sun tafi kai-tsaye ga maɓoyar ’yan ta’addan da ke cikin dajin.

Zuwa lokacin da muka samu wannan labari, wani mazaunin garin Tangaza da ya ki bayyana sunansa saboda tsaro ya ce, an gano gawarwaki uku, saura 10, wasu da suka tsallake rijiya da baya sun dawo gida.

Mazauna yankin sun bayyana cewa mamatan sun haɗabda mafarauta biyar daga ƙauyen Kangiye da biyu daga Chancha da wasu biyu daga Rantijadi da biyu daga Gandaba Gabasa sai mutum ɗai-ɗai daga Gidan Kaji da kuma Gandaba Yamma.

Sojoji sun fatattaki Lakurawa

A ranar Juma’a Lakurawa suka kai wani hari na daban a ƙauyen Magonho da ke Laramar Hukumar Tangaza, amma sojoji suka kai ɗauki inda suka fatattaki ’yan ta’affam suka ƙwato shanun jama’and suka sace.

Cikin ƙasa da awa biyu maharan suka kai wani harin bom, inda inda suka tarwatsa turken sadarwa mallakin Kamfanin MTN, lamarin da ya yi sanadin yankewar layin sadarwa a yankin.

Ana neman mafarautan da suka ɓace

Da yake tabbatar da kisan mafarauta a Tangaza, Mashawarci na Musamman kan Sha’anin Tsaro ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza, Ghazzali Aliyu Rakah, ya ce rundunar haɗin gwiwar jami’an tsaro da ’yan banga sun shiga dajin domin gano mafarautan da ban su ba.

Ya ce, “Tun ranar Asabar muke aiki, amma ƙarancin jami’an tsaro da motocin aiki sun kawo cikas. Amma mun samu ƙarin jami’an tsaro daga yankunan Raka, Tsauna, and Binji domin taimakawa.”

Ya ƙara da cewa mafarautan da tsautsayin ya rutsa da su ba aikin yaƙi da ta’addanci suka je ba, farautar shekara-shekara da suka saba yi suka je.

Rakah ya ce, “Suna sane da haɗarin amma suka zaɓi su shiga jeji farautar. Kaddara ce ta same su.

‘’Yan ta’adda sun dasa nakiyoyi’

Jami’in ya yi gargaɗi cewa ’yan ta’addan sun tsananta amfani nahiyoyi da sauran abubuwan fashewa.

Ya bayyana cewa “A watan juya wasu sojoji sun mutu bayan da motarsu ta taka wata nakiya. Wannan ya sa yanayin matsalar tsaronmu ya fi ma Isa da Sabon Birni muni.”

Rakah ya kuma koka game da matsalar da akae6fama da ita ta masu kai wa ’yan ta’adda bayanai, har ta kai ga “sojoji sun taɓa barazanar yin watsi da sansaninsu a yankin saboda wannan cin amanar.” Ya ce ’yan ta’addan suka yi shigar burtu su saje a cikin jama’a, wanda ke sa da wuya a gane su.

Za mu ɗauki mataki —Gwamnati

Da yake tabbatar da harin turken sadarwa na MTN, Rakah ya bayar ta tabbacin cewa gwamnatin jihar da ƙaramar hukumar suna aiki haiƙan domin ganin am samu wanzuwar tsaro a Tangaza.

Mashawarci kan sha’anin Tsaro ga Gwmnan Ahmad Aliyu, Kamar Ahmed Usman (Murabus) ya bayyana cewa gwamnatin jihar tana aiki kafaɗa-da–kafaɗa da hukumomin tsaro domin kare al’ummomin jihar.

“Gwamna ya ba da muhimmanci ga sha’anin tsaro kuma yana ɗaukar mataki nan take a duk lokacin da muka tuntuɓe shi. Amma duk da haka muna buƙatar samun goyon baya daga jama’a, su daina bayar da mafaka ga masu aikata laifi,” in ji Kamar Usman.

Kakakin ’yan sandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da hare-haren tare da cewa an gano gawarwakin mafarauta biyu kuma ’yan uwansu sun riga sun yi jana’izar su.

DSP Rufa’i ya kuma tabbatar cewa jami’an tsaro na ci gaba da aikin gano ragowar mafarautan da ba a gani ba.

Miyagun hare-haren Lakurawa

Wannan hari ƙari ne a kan matsalar tsaron da ke ci wa yankin Ƙaramar Hukumar Tangaza tuwo a ƙwarya.

A watan Afrilu Lakurawa sun kashe masunta biyu da wani manomi suka yi wa kwanton ɓauna a yayin da suke yin su a ƙauyen Sanyinna

Kafin nan a watan Maris ’yan ta’addan su kai farmaki ƙauyen Baidi, inda suka kashe mutum ɗaya tare da jikkata wani soja da Daren hula uku, sannan suka sace dabbobi, ciki har da raƙuma.

A yayin arangamarsu da sojoji daga baya an samu asarar rayuka daga ɓangarorin biyu.

Duk da wannan ƙalubale Babban Kwamandan Rundunar ta ita Sojin Ƙasa ta Najeriya, Manjo-Janar Ibikunle Ajose, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa sojoji za su yi nasara.

A jawabinsa ga dakarunsa a watan Janairu a yayin bikin Wasanni na Ƙasashen Afirka (WASA) na 2025, Ajose ya bayyana cewa “ana samu tsayayyar nasara akai-akai a yaki da ta’addanci.

“Sojojinmu sun kashe shugabannin ’yan ta’adda da dama da kuma mayaƙansu, wanda hakan ya sa aka ci ga da ayyukan noma da sauran harkokin tattalin arziki a jihar,” yana mai alaƙanta nasarar da sabbin kayan yaki da jiragen da rundunar ke amfani da su.

Ya kuma ba da tabbacin cewa sojoji za su ci gaba da aiki ba dare, babu rana domin kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya a kowane lokaci har sai zaman lafiya ta wanzu a ƙasar.

‘Sun so fakewa da mafarauta don kai wa sojoj hari’

Wani jami’in ƙaramar hukumar da ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana cewa ’yan ta’addan sun so su yi amfani da mafarautan a matsayin farkon da za su yi amfani da su wajen yi wa sojoji kwanton ɓauna.

Ya ce, “Lakurawa sun so ne su yi amfani da mafarautan domin su faruwa sojoji, amma ba mafarautan ba ne ainihin hadafinsu.”

Ya ce amma sojoji sun farga bayan samun bayanan sirri a yankin, saboda, “muna musayar bayanai da sojoji shi ya sa ba su faɗa a tarkon zuwa yankin ba.”

Ya bayyana cewa mafarautan sun fito ne daga ƙananan hukumomin Gwada awa da Tangaza, yana mai cewa, “mun samu labarin an yi garkuwa da wasubdaga cikinsu, kuma muna ƙoƙarin gano ko suna da rai ko an kashe su.”

Lakurawa sun sauya salo —Jami’in gwamnati

Ya ƙara da cewa Lakurawa sun sauya salo a cikin ’yan watannin da suka gabata.

Ya ce, “Yanzu sun dai ƙaƙaba wa mutanen ƙauyuka dokokinsu yadda suke yi a baya. Sun fi mayar da hankali kan satar dabbobi da kai wa jami’an tsaro hari, domin ƙwace makamansu.”

Aminiya ta samu labarin cewa ƙungiyar ta zagaye maɓoyar mayaƙansu da nakiyoyi da suka bibbinne a kan hanyar zuwa sansanin nasu.

“Kusan babu wani yanki a Tangaza da ba su shiga ba, in banda Masallaci and Rakah da ke da sansanonin soji. Amma gundumar Salewa gaba ɗayanta a ƙarƙashin ikonsu take,” a cewar jami’in.

Ya bayyana cewa yanayin ya jefa mazauna cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.

“Ƙaramar Hukumarma na fama matsananciyar matsalar kuɗaɗe. Muna tallafa wa ayyukan samar da tsaro, har ta kai ga yanzu bashi ya yi mana jariri,” a cewar majiyar.

Wani mazaunin Tangaza ya bayyana damuwa bisa yadda Lakurawa ke cin karensu babu babbaka a yankunan karkara.

Ya ce, “Su ba kamar sauran ’yan bindiga masu garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa suke ba. Sun mayar da hankali ne a kan jami’an gwamnati da jami’an tsaro da satar shanu. Sukan far wa fararen ne kawai idan an take su ko aka yi musu Turkiya.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Lakurawa mafarauta Sakkwato Tsaro jami an tsaro da Ƙaramar Hukumar yan ta addan su ya bayyana cewa Hukumar Tangaza Ya bayyana cewa wa mafarautan mafarautan da da mafarauta Lakurawa sun

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda aka yi bikin yaye sabbin matuƙa jiragen Rundunar Sojin Saman Najeriya

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta yaye sabbin matuƙa jiragen sama 35 bayan sun kammala samun horo.

Babban Hafsan Rundunar, Iya Mashal Hassan Abubakar, ne ya sanya sabbin matuƙa jiragen anini a yayin bikin da aka gudanar a Makarantar Tukin Jirgi na rundunar (401 FTS) da ke Kaduna.

Yayen nasu ya zo ne watanni kaɗan bayan rundunar ta mallaki sabbin jiragen yaki guda 12, waɗanda suka ƙara mata ƙaimi wajen ayyukan samar da tsaro da kuma ta’addanci.

A wani taro da ya gudanar da tsofaffin sojojin rundunar a Kaduna, Iya Marshal Hassan Abubakar ya shaida musu cewa rundunar tana jiran karin jiragen yaƙi guda 34.

Ya buƙaci waɗanda aka yayen nasu da su yi amfani da wannan dama wajen cika burin ’yan Najeriya da ke da kyakkyawan fata a kansu.

Rundunar na da nufin amfani da sabbin matuƙan jiragen nata a ayyukanta na tabbatar da tsaro a sassan kasar nan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Abin da ya hana ni cika alƙawarin da na yi wa ma’aikata — Gwamnan Sakkwato
  • Lakurawa sun kashe ’yan bijilanti 11 a Sakkwato
  • Maniyyata Daga Turai Akan Dawakai Sun Isa Kasar Saudiyya Domin Yin Aikin Hajjin 2025
  • An kammala Bada Horo Ga Matan Sojojin Runduna Ta 8 Da Ke Sakkwato
  • An gano shanu 25 da suka ɓace a dajin Sakkwato
  • Masana Sun Bayyana Yadda Yakin Neman Zaben 2027 Ke Barazana Ga Harkokin Tafiyar Da Gwamnati
  • Yadda aka yi bikin yaye sabbin matuƙa jiragen Rundunar Sojin Saman Najeriya
  • Gobarar rumbum makamai Maiduguri da Matakan da ya kamata a ɗauka — Ƙwararru
  • Gobarar rumbum makamai a Borno: Abin da ya kamata a yi