More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

A ko’ina a Nahiyar Afirka za a iya samun ɗan Najeriya da ya bar ƙasarsa domin rayuwa a wata ƙasa.

A yau ba sai an je Turai ko Amurka ba — kasashe irin su Mali, Ghana, Libya, Sudan da sauran su, cike suke da matasa ’yan Najeriya waɗanda suka je ci-rani.

Shin me ya sa waɗannan matasa suke barin Najeriya – uwa ga Afirka, mai albarkatu da dama?

Me suke samu a waje da ba za su iya samu a gida Najeriya ba?

NAJERIYA A YAU: Yadda naira biliyan ɗaya ta salwanta a gobarar Kasuwar Jos DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya

Wannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai duba.

Domin sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ci rani Ƙasashen Afirka Najeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya mayar wa da Shugaban Amurka, Donald Trump martani cewa Najeriya ba ta yadda da duk wani nau’in zarafin addini.

Tinubu, ya yi wannan bayani ne bayan Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kiran “Ƙasashen da ke da Babbar Matsala wajen ’Yancin Addini.”

PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa

Trump ya yi iƙirarin cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazana, amma ya sha alwashin cewa Amurka za ta kare su.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Trump ya rubuta cewa: “Addinin Kirista yana fuskantar babbar barazana a Najeriya. Ana kashe dubban Kiristoci.”

A ranar Asabar, Tinubu ya mayar da martani ta kafar sada zumunta, inda ya ce Najeriya ƙasa ce mai dimokuraɗiyya wadda kundinta ya tabbatar da ’yancin yin addini.

“Najeriya tana da cikakken tanadi a kundinta da ya tabbatar da ’yancin yin addini,” in ji Tinubu.

“Tun daga shekarar 2023, gwamnatina na aiki tare da shugabannin Kiristoci da Musulmai don magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga kowane ɓangare da addini.”

Ya ƙara da cewa, kiran Najeriya ƙasa mai matsala wajen gudanar addini ba gaskiya ba ne.

“Za mu ci gaba da kare ’yancin kowane ɗan ƙasa na yin addininsa cikin walwala. Najeriya ba ta goyon bayan zaluncin addini ko kaɗan,” in ji Tinubu.

Ya kuma ce Najeriya za ta ci gaba da haɗa kai da Amurka da sauran ƙasashe domin inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi
  • A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?
  • Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka
  • Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka
  • Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
  • Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
  • Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
  • Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
  • Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar
  • Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai