Leadership News Hausa:
2025-05-04@22:40:54 GMT

Cutar Mashaƙo Ta Kashe Yara Biyu A Kaduna

Published: 4th, May 2025 GMT

Cutar Mashaƙo Ta Kashe Yara Biyu A Kaduna

Cutar Mashaƙo ta ɓarke a unguwar Tukur-Tukur da ke garin Zaria ta jihar Kaduna, inda ta yi sanadiyar mutuwar yara biyu. Wannan ɓarkewar ta haifar da damuwa game da shirye-shiryen kiwon lafiya a Nijeriya. Abdulazeez Suleiman daga ƙungiyar Northern Elders Forum ya tabbatar cewa mutuwar ta faru cikin sa’o’i 48 bayan bayyanar alamun cutar.

“Wannan ɓarkewar da ta biyo bayan wata irinta ‘yan watannin da suka gabata – inda ta kashe mutane huɗu – yana nuna gazawar tsarin kiwon lafiya da rashin isasshiyar allurar rigakafi a yankunan karkara,” in ji Suleiman. Cutar Diphtheria cuta ce mai saurin yaɗuwa wacce ke haifar da kumburin maƙogwaro da wahalar numfashi.

Cutar Mashako Ta Yi Sanadin Mutuwar Yara 520 — Gwamnatin Kano Kisan Mummuken Cutar Mashako A Nijeriya Da Sassan Duniya

Suleiman ya yi kira da a ɗauki mataki nan take: “Muna bukatar gaggawar yin allurar rigakafi, da wayar da kan jama’a, da inganta kayan aiki.

Hukumar kula da lafiya ta jihar Kaduna ta tura tawaga cikin sauri don kai ɗauki yayin da take binciken yiwuwar alaƙa da wasu lokuta na baya-bayan nan a jihohin makwabta. Ana shawarartar iyaye da su tabbatar da cewa yara sun sami allurar rigakafi da kuma sanar da alamun cutar nan da nan.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Cutar Mashako

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Nijeriya Ta Goyi Bayan Amfani Da Ƙirƙirarrar Basira Cikin Ɗa’a A Aikin Jarida – Minista

A cikin jawabin sa a taron, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana wasu manyan fa’idoji da kuma irin barazanar da ke tattare wajen amfani da AI a cikin ɗakunan buga labarai.

 

Ya ce duk da cewa AI na taimaka wa ‘yan jarida a Nijeriya wajen saurin bayar da rahoto, da nazarin bayanai da gudanar da bincike, yana da matuƙar muhimmanci a yi amfani da wannan sabuwar fasahar cikin hankali da bin ƙa’idoji.

 

Ya ce: “A yayin da muke rungumar aikin jarida da fasahar AI, dole ne mu tabbatar da cewa ba za a tauye ‘yancin jarida ba, illa ma a ƙara ƙarfafa shi.”

 

Ministan ya kuma ba da sanarwar cewa Nijeriya za ta kafa Cibiyar Ilimin Kafafen Watsa Labarai ta UNESCO a Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN), inda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya riga ya amince da kuɗin kafa cibiyar.

 

Ana sa ran wannan cibiyar za ta kasance cibiyar ƙasa da ƙasa da za ta inganta aikace-aikacen kafafen watsa labarai cikin gaskiya da tunani mai zurfi a fannin dijital.

 

Haka kuma, ya bayyana cewa Nijeriya tana kan hanyar ƙaddamar da tsarin dokar ƙasa kan amfani da AI a cikin aikin jarida.

 

Wannan tsari zai ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire amma ba tare da tauye ‘yancin jarida ko karya ƙa’idojin aikin ba.

 

Idris ya buƙaci haɗin gwiwa tsakanin ‘yan jarida, da masana fasaha, da kafafen yaɗa labarai, da ‘yan siyasa da ƙungiyoyin farar hula domin samar da ƙa’idojin amfani da AI, da koyar da sababbin dabaru, da tabbatar da gaskiya, da kuma faɗakar da al’umma.

 

A nata jawabin, Marija Peran, wakiliyar KAS a Nijeriya, ta jaddada irin damar da AI ke bayarwa ga aikin jarida, tare da yin kashedi kan haɗurran da ke tattare da hakan.

 

Ta ce: “Yana da muhimmanci mu kare ‘yancin kafafen yaɗa labarai a duk duniya, musamman yanzu da AI ke ƙara shiga aikin jarida.

 

“A matsayin ta na ƙungiya mai kishin dimokiraɗiyya da doka da oda, KAS tana tare da kafafen yaɗa labarai wajen fuskantar wannan sabon yanayi.”

 

Taron ya samu halartar mutane daban-daban, ciki har da Shugaban Kwamitin Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Majalisar Wakilai, Honarable Akintunde Rotimi Jr.; da wakilan kafafen yaɗa labarai, da ƙungiyoyin farar hula da kuma abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ƴansanda Sun Kashe Ƴan Bindiga 3, Sun Ceto Waɗanda Aka Sace
  • Boko Haram ta kashe sojoji 4 a Yobe
  • Ko Kin San… Yadda Ake Nagartaccen Tsumi?
  • Kiwon Lafiya: Jihar Kwara Ta Bayyana Yadda Karancin Likitoci Ke Kawo Mata Cikas
  • Ma’aikatar Lafiya Ta Falasdinu Ta Tabbatar Da Karuwan Falasdinawan Da Suka Yi Shahada
  • Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sun Kashe Fararen Hula Kusan 300 A Hare-Haren Baya-Bayan Nan A Sudan
  • Gwamnatin Nijeriya Ta Goyi Bayan Amfani Da Ƙirƙirarrar Basira Cikin Ɗa’a A Aikin Jarida – Minista
  • Dakataccen Gwamnan Ribas Ya Dawo Daga Hutun Makonni Biyu A Kasar Waje
  • Ranar Maleriya Ta Duniya: ‘Yan Nijeriya Na Kashe Naira Tiriliyan 1.156 Duk Shekara Wajen Sayen Magunguna