Boko Haram ta kashe sojoji huɗu a Yobe
Published: 4th, May 2025 GMT
’Yan ta’addan Boko Haram da suka kai hari kan rundunar soji ta 27 da ke Buni Yadi a jihar Yobe, sun kashe akalla sojoji hudu tare da lalata kayan aiki da dama na soji.
An kai harin ne kafin wayewar garin Asabar, jim kaɗan bayan da Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas ta gana a Damaturu domin tattauna hanyoyin haɗin gwiwa wajen yaki da ta’addanci.
Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa maharan sun kai mummunan hari suna harbul kan mai da harbe-harbe.
Hedikwatar sojojin Najeriya ta tabbatar da harin inda ta bayyana cewa sojoji na fafatawa da ISWAP a Buni Gari.
ISWAP sun kai wa sojoji hari a Yobe Rashin tsaro: ‘Ba za mu miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba’Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakkun bayanai kan asarar rayuka ba.
Mazauna garin Buni Yadi, mahaifar Gwamna Mai Mala Buni, sun tsere zuwa wurare masu aminci, kuma sojoji sun rufe babbar hanyar da ta hada Yobe da kudancin Borno.
Wannan harin ya biyo bayan wani irin harin da aka kai makonni biyu da suka gabata a yankin Chalie na Buni Yadi inda aka ce an kashe sojoji uku.
Hare-haren ’yan ta’adda sun karu a yankunan Borno, inda suke kai hari kan kauyuka da sansanonin soji.
Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum da sauran shugabanni sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki mataki, suna masu nuni da cewa wasu ƙananan hukumomi na karkashin ikon Boko Haram tare da nuna damuwa game da shigowar ’yan ta’adda daga kasashe makwabta.
Sun yi kira da a kai farmaki a yankin tafkin Chadi da dajin Sambisa.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
MDD: HKI Ta Kashe Falasdinawa 1 Fiye Da 100 A Cikin Kwanaki 2 A Lokacinda Suka Karban Abinci
Hukumar kula da samar da agaji ta MDD OCHA ta bada sanarwan kissan Falasdinawa fiye da 100 a lokacinda suke kokarin neman abincin da zasu ci.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mataimakin shugaban kungiyar ta OCHA Farhan Haq yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa bai kamata mutane sum utu a wajen neman abinci ba. Dokokin kasa da kasa sun tabbatar da cewa, mutum ko menene laifinsa bai kamata a hana shi abinci ba, kuma bai kamata yam utu saboda neman abinci ba.
Farhan Haq ya yi gargadin cewa idan wannan halin ya ci gaba, to dukkan duniya sun ji kunya, idan suna da shi, suna ganin Falasdinawa suna mutuwa a lokacinda kowa a duniya yana kallo, amma ba wanda ya isa ya hana hakan faruwa.
Yace kofar ragon da HKI ta yiwa Gaza, ya kai ga a halin nyanzu yunwa ta yi tsanani a gaza ta yadda yuwan tana kashesu a mazauninsu a cikin gaza. Kuma maganin shi ne dole ne a cika gaza da kayakin abinci.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Mutanen Kasar Siriya Sun Fito Zanga-Zanga Yin Allawadai Da Kissan Alawiyya A Kasar August 2, 2025 Shugaban Ansarullah: Amurka Tana Da Hannu A Ta’asar Da HKI Take Aikatawa A Gaza August 2, 2025 Kungiyar Wasan Taekwondo Ta Guragu Ta Iran Ta Zama Zakara A Asiya Karo Na 10 A Jere August 2, 2025 Iran ta yi gargadi game da makircin Isra’ila na kawo cikas ga tsaron yankin August 2, 2025 Firayim Ministan Senegal Ya Bayyana Sabon Shirin Farfado Da Tattalin Arzikin Kasar August 2, 2025 Gaza: Witfkoff ya yi rangadi a wuraren da Amurka ta kafa domin tallafi August 2, 2025 ‘Yan Sudan dama na komawa gida bayan gudun hijira na tsawon shekaru a Masar August 2, 2025 Iran Ta Ce Batun Neman Dakatar Da Tace Uranium Zai Rusa Duk Wata Jarjejeniya Da Ake Son Cimmawa August 1, 2025 Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Watsi Da Duk Wani Zarge-Zargen Neman Bata Mata Suna August 1, 2025 Limamin Sallar Juma’a Ya Ce; Iran Zata Mayar Da Isra’ila Kufai Idan Ta Sake Kai Hari Kan Kasarta August 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci