Aminiya:
2025-06-20@10:03:34 GMT

Ghana ta ci tarar ministoci saboda rashin bayyana kadarorin da suka mallaka

Published: 6th, May 2025 GMT

Shugaban Ghana a wannan Litinin ɗin ya bayyana ɗaukar mataki kan ministoci da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa fiye da 40 da suka gaza bayyana kadarorin da suka mallaka.

Wannan na zuwa ne a yayin da Shugaba John Mahama ke ci gaba da zage dantse wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar da ke yammacin Afirka.

’Yan bindiga sun kashe matar aure bayan karɓar N10m kuɗin fansa ’Yan fashi sun kashe matashi a Kano

A yayin karɓar rantsuwar kama aiki a watan Janairun bana ne Shugaban Ghana ya sha alwashin yaƙi da rashawa domin fitar da ƙasar daga ƙangin matsalar tattalin arziki

A watan Afrilun da ya gabata ne mahukunta suka gurfanar da wani babban jami’in tsaro kan wawure miliyoyin daloli daga wata kwangilar tsaron yanar gizo.

Sai dai ana ganin matakin da Shugaba Mahama ya ɗauka wani babban yunƙuri ne na ladabtar da jami’an gwamnati.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa muƙarraban gwamnatin da aka samu da laifin rashin bayyana kadarorin da suka mallaka ba za a biya su albashi ba har na tsawon watanni huɗu.

Bayanai sun ce a ranar 31 ga watan Maris ne wa’adin bayyana kadarorin da muƙarraban gwamnatin suka mallaka ya cika, inda za a hana su albashinsu na watanni huɗu.

Sai dai za a riƙe albashinsu na watanni uku a matsayin ladabtarwa yayin da albashin wata ɗaya zai zama gudunmawar da aka tilasta musu domin kafa sabuwar Hukumar Kula da Asusun Lafiya ta Ghana Medical Trust Fund da ake laƙabi fa “Mahama Cares”.

“Ya zuwa rufe aiki a ranar Laraba, 7 ga watan Mayun 2025, duk wanda ya gaza bayyana kadarorin da ya mallaka ya sallami kansa daga nan take” a cewar wata sanarwa da Shugaba Mahama ya yi a birnin Accra.

Sabuwar dokar ta shafi dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa da suka haɗa da ministoci, hadimin shugaban ƙasa da shi kansa shugaban ƙasar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kadarori bayyana kadarorin da

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Yadda Tsarin Ilimi Ke Karya Gwiwar ’Yan Najeriya

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Yan Najeriya da dama ne dai da suka yi ilimin zamani dole ta sa suka rungumi sana’o’in da a baya ake ganin na kaskantattu ne don su samu na sakawa a bakin salati.

Mai yiwuwa hakan ne ya sa wasu, musamman matasa, suka yanke kauna da cewa shafe lokaci ana karatun kan iya taimaka wa mutum magance bukatunsa nay au da kullum.

NAJERIYA A YAU: Yadda Cutar Amosanin Jini Ta Hana Ni Cimma Buri Na DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro?

Wannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • 2027: ‘Sai bayan babban taron APC Tinubu zai bayyana wanda za su yi takara tare’
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Tsarin Ilimi Ke Karya Gwiwar ’Yan Najeriya
  • Kar a kuskura a shiga cikin yaƙin Iran da Isra’ila — MDD
  • Wang Yi Ya Yi Tsokaci Kan Sakamakon Ziyarar Shugaba Xi A Kazakhstan
  • Hare-haren Benuwe: Tinubu ya ziyarci waɗanda suka jikkata a asibiti 
  • Litar fetur za ta iya komawa N1,000 a Najeriya saboda yakin Isra’ila-Iran – Masana
  • Ma’aikatan Kwalejin Ilimi ta jihar Kaduna za su tsunduma yajin aiki
  • Wani Matashi Ya Ƙone Kansa A Kano Saboda Yana Son Zuwa Aljanna 
  • DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro?
  • Yaƙin Iran da Isra’ila: Amurka za ta tura jami’anta don tattaunawa da Tehran