Aminiya:
2025-08-04@20:00:24 GMT

NAJERIYA A YAU: Me Yake Kai ‘Yan Gwagwarmaya Shiga Tasku A Najeriya?

Published: 6th, May 2025 GMT

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Yin gwagwarmaya ko fafutuka wani abu ne da ke cikin jinin dan Adam, musamman idan yana kokarin ganin an samu sauyi ko cigaba a al’umma.

Sai dai a Najeriya, sau da yawa ana danganta kalmar “gwagwarmaya” da rikici ko sabani da gwamnati.

NAJERIYA A YAU: Abin da ke kai matasan Najeriya ci-rani wasu ƙasashen Afirka DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya

Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan yadda za a yi gwagwarmaya ba tare da an taka doka ba.

Domin Sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwagwarmaya Fafutuka

এছাড়াও পড়ুন:

Ma’aikatan jinya sun dakatar da yajin aiki a faɗin Najeriya

Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya ta Najeriya (NANNM), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ta fara a faɗin ƙasar nan.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata takarda da shugabanta ƙasa, Haruna Mamman, da sakatarenta, T.A. Shettima, suka sanya wa hannu.

Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja Jami’ar Umaru Yar’adua ta kori ɗalibai 57 kan satar jarabawa

Sun fara yajin aikin ya fara ne a ranar Laraba tare da niyyar shafe kwanaki bakwai suna yin sa.

Ma’aikatan jinyar sun shiga yajin aikin ne saboda ƙarancin albashi, ƙarancin ma’aikata, da kuma rashin ingantattun wuraren aiki.

Wannan yajin aiki na zuwa ne a daidai lokacin da likitoci ke takun saƙa da gwamnati kan batutuwan suka shafi jin daɗin aikinsu.

Aminiya ta ruwaito yadda yajin aikin ya janyo ya haifar da tsaiko ga ayyukan lafiya a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Sun fara yajin ne bayan ƙarewar wa’adin kwana 15 da ƙungiyarsu ta bai wa Gwamnatin Tarayya.

A ranar Asabar ne ƙungiyar ta dakatar da yajin aikin bayan wani taro ta Intanet da shugabanninta suka gudanar.

A ranar Juma’a, ƙungiyar ta gana da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da Ma’aikatar Ƙwadago, Ofishin Shugaban Ma’aikata, Ofishin Akanta-Janar, da Hukumar Albashi da Alawus da wasu ɓangarori na masu ruwa da tsaki domin tattauna buƙatunsu.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, NANNM ta ce ta dakatar da yajin aikin ne bayan duba yarjejeniyar da suka cimma da gwamnati.

Sanarwar, ta ce gwamnati ta ɗauki matakai masu muhimmanci kuma ta bayar da jadawalin lokacin da za ta cika alƙawuran.

Saboda wannan yarjejeniya da kuma samun masalaha, ƙungiyar ta dakatar da yajin aikin nan take.

Ta kuma umarci dukkanin ma’aikatan jinya da su koma bakin aiki, tare da gargaɗin cewa ba za ta amince a hukunta kowa ba saboda shiga yajin aikin.

Ƙungiyar ta gode wa mambobinta bisa goyon baya da haɗin kai, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da kare haƙƙinsu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Malamai A Najeriya Suna Goyon Bayan Iran A Yadda Take Fuskantar HKI
  • Ƴan matan Najeriya Sun Lashe Gasar Kwallon Kwando Ta Afirka
  • Najeriya na hasashen samun N300bn a shekara daga noman dabino
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Talauci Ke Hana Shayar Da Yara Nonon Uwa Zalla A Najeriya
  • Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Najeriya — El-Rufai 
  • Sojoji sun ceto malamin Jami’a da aka sace a Taraba
  • Ma’aikatan jinya sun dakatar da yajin aiki a faɗin Najeriya
  • Jihar Sakkwato ta ciyo bashin N70.4bn domin inganta kiwon lafiya
  • Jihar Sakkwato ta ciyo bashin N70.4bn N70.4bn domin inganta kiwon lafiya
  • Har yanzu ana fama da cutar kwalara a Najeriya – UNICEF