Hajj 2025: Maniyyatan Kaduna za su fara tashi ranar 14 ga watan Mayu
Published: 6th, May 2025 GMT
Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna za ta fara jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya a ranar 14 ga watan Mayu, 2025.
Shugaban hukumar, Malam Salihu S. Abubakar, ne ya bayyana hakan a wani shirin rediyo kai tsaye da aka watsa daga Kaduna, inda ya bayyana shirye-shiryen da jihar ta kammala domin aikin Hajjin bana.
Ya bayyana cewa maniyyata 4,060 daga jihar Kaduna za su sauke farali a bana, kuma kamfanin jirgin sama na UMZA ne zai yi jigilarsu.
Shugaban hukumar ya bayyana cewa domin kammala matakan da ake bi kafin tafiya, za a yi duk maniyya cikakken gwajin lafiya a sansanin alhazai da ke Mando.
Wata mata ta auri maza biyu a lokaci guda a Kano NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ‘Yan Gwagwarmaya Ke Shiga Tasku A Najeriya?Ka’idodin lafiya na ƙasa da ƙasa da kuma na Saudiyya sun shardan cewa dukkan mata maniyyata za su yi gwajin daukar ciki kafin tafiya.
Malam Salihu ya bukaci maniyyata su kiyaye dokoki da ƙa’idojin da hukumomin Saudiyya suka gindaya, yana mai jaddada muhimmancin ladabi, haɗin kai da kuma kiyaye tsaron kai a lokacin aikin Hajji.
Ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da sadaukar da kai don ganin maniyyata sun sami sauƙin tafiya tare da samun damar ibada cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi
“A lokacin, mun yi lissafin adadi a Babban Bankin. Na tashi na kafa sharuda bisa ga ka’idodi, inda na ce a cire tallafin yau. Farashin kaya zai tashi daga kashi 11 zuwa kashi 13, zan rage shi a cikin shekara guda. Ba za mu samu hauhawar farashin kaya na kusan kashi 30 ba,” in ji shi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA