HausaTv:
2025-08-02@17:59:41 GMT

 Iran Ta Yi Allawadai Da Hare-haren HKI Akan Syria Da Nufin Rusa Kasar

Published: 3rd, May 2025 GMT

 Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Manufar HKI akan Syria a fili take ba a boye ba.”

Baka’i ya ci gaba da cewa; Manufar HKI  ita ce rusa duk wani karfi da Syria take da shi na yaki, da kuma lalata tattalin arzikinta, domin share fagen shimfida iko a kasar da kuma a cikin wannan yankin.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya kuma ci gaba da cewa; matsayin jamhuriyar musulunci ta Iran akan kasar Syria, a fili yake wanda shi ne kare hadin kan wannan kasa da hana ta tarwatsewa da kare daukakarta a matsayinta na kasa mai ‘yanci da kuma al’umma mai tsawo tarihi na ci gaba,sannan kuma mai tasiri a cikin wannan yanki na yammacin Asiya.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya dora alhakin abinda yake faruwa a Syria, akan dukkanin wadanda su ka taka rawa wajen jefa kasar cikin halin da take a  yanzu.

Wuraren da HKI ta kai wa hare-hare a daren jiya sun hada da sansanin sojan runduna ta 47 da sojoji Syria dake yankin Humah ta yamma, haka nan kuma rumbun ajiyar makamai na sojan sama a kusa da garub shahdaha, da ya jikkata mutane 4,kamar yadda kamfanin dillancin labaurn “SANA” na kasar ta Syria ya nakalto.

A birnin Damascuss ma sojojin HKI sun kai wasu hare-haren da su ka hada da kusa da fadar shugaban kasa. Kafafen watsa labaru sun ambci shahadar mutum daya, da kuma jikkatar wasu.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Amurka Dangane Da Batun Ukraine

Kasar Sin ta sake neman Amurka, da ta daina zarginta, da dora mata laifi, ya kamata kasar Amurka ta taka rawa wajen tsagaita bude wuta, da kara azama ga gudanar da shawarwarin shimfida zaman lafiya. Jami’in ya ce, ana bukatar hadin kai wajen warware rikicin Ukraine, a maimakon rarrabuwar kawuna da yin fito-na-fito. (Tasallah Yuan)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutanen Kasar Siriya Sun Fito Zanga-Zanga Yin Allawadai Da Kissan Alawiyya A Kasar
  • Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Amurka Dangane Da Batun Ukraine
  • Iran Ta Ce Batun Neman Dakatar Da Tace Uranium Zai Rusa Duk Wata Jarjejeniya Da Ake Son Cimmawa
  • Shugaban Kasar Iran Zai Ziyarci Pakistan A Gobe Asabar
  •  Shugaban Kasar Lebanon Aun Ya Ce Mun Aike Wa  Amurka Sakwanni Akan Dakatar Da Hare-haren HKI
  • Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Mata
  • Kasar Iran Ta Bayyana Gushewar Hasashen Raunin Karfin Sojinta Kuma Ba Zai Dawo Ba
  • Sojojin Yemen Sun Kai Zafafan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Guda Uku  
  • Ma’aikatar Bunƙasa Harkar Kiwo Za Ta Taimaka Wajen Magance Rikicin Manoma Da Makiyaya — Jega