2025-07-06@22:32:07 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5335

«Okowa»:

    Tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Nijeriya ta fara gasar ƙwallon ƙafa ta mata ta ƙasashen Afirika da kafar dama, bayan lallasa ƙasar Tunisia da ci 3-0 a wasan farko da suka buga yau Lahadi a filin wasa na Prince Moulay Abdellah. Asisat Oshoala da Rinsola Babajide da Chinwendy Ihezuo ne suka jefa kwallayen da suka...
    Wani bincike da Cibiyar Bincike ta Africa Polling Institute (API), ta gudanar ya nuna cewa yawancin ’yan Najeriya ba su da ƙwarin gwiwa game da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Majalisar Dokoki da kuma ɓangaren shari’a. An bayyana sakamakon Binciken Haɗin Kan Al’ummar Najeriya na 2025, a wani taron ƙasa da aka gudanar a Abuja....
    “Na yi Allah- wadai da amfani da madafun iko da tsara sakamakon zabe kafin zabe ta hanyar amfani da karfin mulki da hukumomin gwamnati.” “Wajibi ne Hukumar Zabe ta samu hanyoyin magance wadannan matsalolin a wajen jefa kuri’a maimakon neman hakki a bangaren shari’a wanda daga karshe kotu za ta sanya wasu dubaru ta kori...
    A cikin ‘yan kwanakin nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mayar da jawabi ga malamai da daliban tawagar musayar al’adu ta matasan Amurka masu buga wasan kwallon pickle daga gundumar Montgomery ta jihar Maryland, wadanda suka ziyarci kasar Sin a karkashin shirin gayyatar matasan Amurkawa 50,000 zuwa kasar Sin domin yin musaya da...
    Elon Musk, wanda ya taɓa zama mashawarcin Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa mai suna America Party. Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (Twitter), makonni bayan wata taƙaddama da ta ɓarke tsakaninsa da Shugaban Amurka. Tinubu ya umarci sojoji su murƙushe ’yan ta’adda a faɗin Najeriya  Mutum 21...
    Kungiyoyi farar da jam’iyyun adawar  siyasa a kasar Togo, sun sake yin kira da a gudanar da Zanga-zanga a ranar 16 da 17 ga watan nan na Yuli da ake ciki. Masu Zanga-zangar dai suna son nuna kin amincewa ne da siyasar hukumar kasar da suke bayyanawa da ta kama-karya, haka nan kuma kashe wasu...
    Raundunar sojan jamhuriyar Nijar sun sanar da cewa, an kashe  sojoji 10 da kuma jikkata wasu 15 a wasu hare-hare biyu da masu dauke da makamai su ka kai a yankin Telaberi da kudu masu yammacin kasar. Yankin Telaberi dai yana cikin yankunan da masu dauke da makamai su ka fara kai hare-hare saboda kusancinta...
    Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’ima Kassim ya bayyana cewa; Dakarun Hizbullah mazajen fagen daga ne da ba su karbar kankanci. Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a wurin babban taron Ashura a ungiyar Dhahiya dake birnin Beirut, ya bayyana cew; Yaki na tsaron kasa zai ci gaba saboda mun yi Imani da...
    Sanatan ya bayyana cewa gwamnonin yankin na farko sun ba da gagarumar gudunmuwa wajen jagorantar hadin kai wajen cimma muradun yankin daga kan ikon sarrafa albarkatun kasa zuwa matsalolin muhalli da sauransu. A kan wannan ya yi kira ga gwamnoni.masu ci a yanzu da su ci gaba da wannan al’adar, kuma su kara kokari kan...
    Ɗaya daga cikin hadiman gwamnan jihar Yobe, Hon. Babagana Yakubu Mohammed, ya ajiye muƙaminsa na mai taimakawa gwamna na musamman ya kuma fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADC. Babagana, ya sanar da ajiye aikin nasa ne cikin wata wasiƙa da ya aikewa Sakataren Gwamnatin Jihar, Baba Malam Wali. Ba Ni Da Niyyar Barin APC...
    Masanin Kenya kan huldar kasa da kasa mai suna Cavince Adhere, ya bayyana a yayin zantawarsa da dan jarida na kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan nan cewa, a matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, hadin gwiwar Sin da kasashe masu tasowa ya jaddada daidaito da samun albarkatu, inda hakan ya samu...
    Zalum ya kuma shawarci gidajen jaridu da su dinga tantance labarai kafin su yaɗa shi domin kaucewa labaran ƙanzon kuregen da wasu suke yaɗawa. A ƙarshe gwamnan ya ce ya duƙufa wajen hidimtawa al’ummar jihar Borno a ƙarƙashin jam’iyar mai albarka ta APC . Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Labarin da dan jarida ya samu daga ma’aikatar tsaron jama’a ta kasar Sin a yau Lahadi ya nuna cewa, a kwanan baya kasashen Sin da Myanmar da Thailand sun gudanar da taron ministoci karo na biyu don yaki da laifukan zambar da ake aikatawa ta hanyar sadarwar waya. A gun taron, sassan da abin ya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Aƙalla mutum 21 ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Zariya zuwa Kano. Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), reshen jihar ce ta tabbatar aukuwar hatsarin. Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:23 na safe a unguwar Kasuwar Dogo da ke yankin Dakatsalle. Zulum ya musanta...
    Aƙalla mutum 21 ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Zariya zuwa Kano, kamar yadda Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta tabbatar. Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:23 na safe a unguwar Kasuwar Dogo da ke yankin Dakatsalle. Zulum ya musanta shirin ficewa daga...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa zai bar jam’iyyar APC zuwa ADC tare da wasu gwamnoni biyar. A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dauda Iliya, ya fitar, Zulum ya ce wannan labari ƙarya ne, kuma wasu ne kawai ke ƙirƙirarsa domin cimma...
    Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gargaɗi sarakunan gargajiya a faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar kan zargin hannu a mamaye hanyoyin kiwo da filayen kiwo, abin da ke haddasa rikici tsakanin makiyaya da manoma. Gwamnan ya nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa wasu sarakuna na karɓar cin hanci suna kuma ba da damar...
    Gangamin Ashura ya zama lamarin mafi girma da cunkoson jama’a inda tattakiin Tuwairij yake gudana tare da faɗaɗa da ba a taɓa ganin irinsa ba Tattakin Tuwairij na bana zuwa birnin Karbala na fuskantar hallara da cunkoson jama’a da ba a taba ganin irinsa ba, inda dimbin masu ziyara  daga sassan duniya ke tururuwa zuwa...
    An sake gudanar da wani sabuwar zanga-zanga a manyan biranen duniya domin neman kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza A jiya asabar ne aka sake gudanar da wata sabuwar zanga-zanga a kasashe da dama na duniya domin nuna adawa da hare-haren da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ke ci gaba da kai wa kan...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya tafi kasar Brazil don halartar taron BRICS karo na 17 Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya sanar da isar ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi a birnin Rio de Janeiro domin halartar taron kasashe mambobi a kungiyar BRICS karo na 17. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen...
    Babban Mufti na masarautar Oman ya yi kakkausar suka kan kasashen da ke neman kulla alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila Babban Mufti na masarautar Oman, Sheikh Ahmed bin Hamad Al-Khalili, ya bayyana mamakinsa kan yadda wasu kasashe ke son kulla                     alaka da makiya yahudawan sahayoniyya, wata kasa ‘yar mamaya maras tushe. A cikin wani bayani...
    Aƙalla mutane takwas ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Atura Bus Stop, hanyar Lagos-Badagry, lokacin da wata motar haya ƙirar Mazda mai ɗaukar fasinjoji 16 ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota ƙirar DAF. Hukumar LASTMA ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce sa’a da rashin...
    A ranar Asabar, ƙungiyar PSG ta doke Bayer Munich da ci 2-0 a wasan zagayen kusa da na ƙarshe na gasar Kofin Duniya na Kungiyoyi, wanda aka buga a filin wasa na Mercedes Benz, Atlanta, Amurka. Duk da samun katin kora guda biyu, PSG ta nuna kwarewa da jajircewa wajen zura ƙwallaye masu kyau a...
    Hukumomi a Jihar Texas ta Amurka sun ce gomman mutane sun riga mu gidan gaskiya ciki har da kananan yara sakamakon wata mummunar ambaliyar ruwa a ranar Asabar. Sai dai ya zuwa yau Lahadi, adadin wadanda suka mutu sun kai 50 ciki har da kananan yara 15 yayin da ake ci gaba da aikin ceto...
    Lamarin da ya haddasa daya daga cikin bala’i da mutane suka taba fadawa, inda sama da mutum miliyan 12 suka tsere daga gidajensu. Darfur ta kasance yankin da nan da nan rikici kan tashi, inda RSF ke iko da yawancin yankin, in banda birnin el-Fasher wanda ya ci gaba da kasancewa a hannun rundunar sojin...
    Sojojin Ukraine sun kama wani ɗan Nijeriya da ke taimaka wa Rasha a yaƙin da suke gwabzawa sama da shekaru biyu biyo bayan mamayar ƙasarsu. Wani bangaren sojin da ke ƙunshe da mayaƙan Rasha da ke goyon bayan Ukraine a wannan yakin, wanda ake kira ‘Freedom Of Russia Legion ne ya kama Kehinde Oluwagbemileke mai...
    Rashford dai ya fi son komawa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona domin yana ganin zai iya buga abin a zo a gani a kakar wasa mai zuwa sai dai ita kuma Barcelona ta fi son dan wasa Nico Williams na kungiyar Athletico Bilbao ta kasar Spaniya, wanda shima yake son komawa Bardelona da buga wasa...
    Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya halarci zaman makokin da aka gudanar a hussainiyar Imam Khomaini (q) da cikin gidansa a nan birnin Tehran a daren Ashoorah a jiya Asabar da yamma. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hujjatul Islam Masaoud Ali wanda ya karanta makokin yana fadar...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da ci gaba da riki jami’an diblomasiyyar kasar 4 wanda HKI take yi tun shekaru 43 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar tana fadar haka a wata sanarwa da ta fitar shekaru 43 cur da sacewar wadanda...
    Majiyar kafafen yada labarai na Amurka sun bayyana cewa akalla mutane 52 suka rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwan sama a jihar Texas. Jaridar US Today ta bayyana cewa an kubutar da daruruwan mutane daga halaka, amma kuma har yanzun ba san makamon daruruwan mutane ba. Sannan kungiyoyin bada agaji suna ci gaba da neman masu...
    Kamfanin jiragen sama na UAE airlines ko emirate ya sake farfado da zirga zirga zuwa kasar Iran bayan da aka rufe sararin samaniyar kasar Iran a ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata. Jaridar National ta kasar Amurka ta bayyana cewa kasashe da dama a duniya sun dakatar da zirga zirga zuwa JMI saboda...
    Dakarun sojin Nijar sun samu nasarar kashe ’yan ta’adda 41 a yayin wasu tagwayen hare-hare da aka kai musu ranar Juma’a a yammacin ƙasar. A cikin wata sanarwa, Ministan Tsaron Nijar, Janar Salifou Modi ya ce hare-haren ta’addancin da ɗaruruwan ’yan ta’adda suka kai a lokaci guda, sun auku ne a yankunan Bouloundjounga da Samira...
      Rukunin farko: Morocco da Zambiya da Senegal da kuma Jamhuriyar Congo Rukuni na biyu: Nijeriya da Tunisia da Algeria da kuma Botswana. Rukuni na uku: Afirka ta Kudu da Ghana da Mali da kuma Tanzania. Bayan karawar bude labulen gasar, akalla za a rika buga wasanni bibiyu kowacce rana a fafatawar cikin rukuni har...
    Ibrahim ya bayyana cewa, sun rarraba mukamai na rikon jam’iyyar a tsakaninsu, kafin babban taro na kasa a nan gaba. Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya tabbatar cewa; hadakar ta ADC, ta zabi Aregbesola a matsayin sakatarenta na kasa na riko, har ma ya wallafa a jawabin karbar mukamin da ya yi a shafukan sada...
    Zaunannen wakilin Sin dake ofishin MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa a birnin Geneva Che Xu, ya yi jawabi a gun taron tattaunawa na shekara-shekara, kan gudummawar fasahohi karo na 59, na majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD a jiya Juma’a, a madadin walikan kasashe fiye da 70, game da raya hidimomi ga...
    Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya tunasar da karamar hukumar Roni game da bukatar gina wani rukuni mai dauke da ajujuwa guda biyu ga makarantun ‘ya’yan Fulani makiyaya domin inganta rayuwar su. Shugaban kwamatin, Alhaji Aminu Zakari, ya yi wannan kiran a karshen ziyarar kwanaki biyu da kwamatin ya yi a karamar...
    Jita-jita ta fara ƙarfi cewar Sanata Ibrahim Lamiɗo da ke wakiltar Sakkwato ta Gabas a Majalisar Dattawa, na shirin ficewa jam’iyyar APC zuwa ADC. Wannan jita-jita ta fara ƙarfi ne bayan da wasu ‘yan siyasa suka haɗu don kafa sabuwar jam’iyya mai suna ADC da nufin kayar da APC a zaɓen 2027. Gonakin Koko: Mata...
    Taron farko na tsarin hadin gwiwar kungiyar BRICS, tun bayan shigar Indonesia da sauran abokan huldar kungiyar 10, ya ja hankulan sassan kasa da kasa. Har ma wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta nuna cewa kaso 91.2 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi na ganin hadin gwiwa...
    “Ni na san fina-finan da aka haska a gidajen Gala da aka samu fiye da Naira miliyan daya a rana daya, wasu kuma har miliyan biyu, yanzu idan ka duba tun daga Kano har Nijar za ka dinga ganin gidajen Gala, haka zalika daga nan Kano har zuwa birnin Legas ma akwai su, saboda haka;...
    Rahotanni daga kudanci Lebanon sun ce, sau uku jiragen yakin HKI su ka kai hare-hare a kan gidajen mutane da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya da kuma jikkatar wasu da dama. A garin Shaqra’dake yankin Bint-jubail, jiragen sama marasa matuki sun kai hare-hare da ya yi sanadiyyar jikkatar mutane biyu da raunuka, kamar...
    Dakarun kare juyin musulunci na Iran sun fitar da bayani a lokacin tunawa da sace jami;an diplomasiyyar Iran 4 a birnin Beirut, wanda ya kunshi cewa: Ya zama wajibi ‘yan sahayoniya su kwana da sanin cewa; Duk laifukan da su ka aikata a baya za a yi musu sakamako a kansa,kuma duk wani sabon wuce...
    Wasu ƙungiyoyin mata a ƙauyukan Bendeghe-Ekiem da Abiya da ke Ƙaramar Hukumar Etung, a Jihar Kuros Riba, sun yi  barazanar gudanar da zanga-zangar tsirara idan gwamnati ba ta janye ƙudirin sayar da gonakin koko ba. Matan sun ce wannan shawara da gwamnati ta ɗauka ba su aminta da ita ba, domin gonakin koko su ne...
    Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim  ya mayar da martani ga wadanda suke son, kungiyar ta mika makamanta, yana mai cewa; Ku fara da neman makiya su fice daga cikin Lebanon, domin babu hankali ace ba ku cewa komai akan ‘yan mamaya,ya zamana kuna neman wanda yake gwgawarmaya ya ajiye makamansa.”...
    A yau Asabar ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaran aikinsa na kasar Ghana Samuel Okudzeto Ablakwa, suka aikewa juna sakon murnar cika shekaru 65, da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu. A cikin sakonsa Wang Yi ya bayyana cewa, cikin shekaru 65, an raya dangantaka tsakanin Sin da Ghana yadda...
    Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga Jihar Kano: Gani suke ai in su nuna suna samu kamar matan nasu za su dora musu hidima da yawa, sun gwamma ce su bar matansu da wahala. Wani ma dan rashin imani kokari yake ita matar ta ciyar da shi alhalin yana da damar sa, shi ya...
    Jam’iyyar NNPP, ta bayyana cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya yi mata takarar shugaban ƙasa a 2023, ba zai tsaya takara a 2027 ba. Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dokta Agbo Major, ne ya bayyana haka a wata sanarwa, inda ya mayar da martani kan wata magana da Buba Galadima ya yi. Tinubu ko ɗansa...
    Yadda za’a hada: Asamu biredi mai yanka-yanka a shafe shi da bota a ajiye a gefe. Sai a zuba mai a cikin karamin kaskon miya sai a zuba yankakkiyar albasa a dan soya na minti biyu, sai a zuba jajjagagen su attaruhu din nan a ci gaba da soyawa. A zuba kayan kamshi da kayan...
    Idan ko tana wannan kazar-kazar din to dukkanin jikinta budewa yake yi. Don haka idan budurwa ta yi aure kuma ta kasance mai irin wannan dabi’a shi ne sai ki ga an sami matsala da miji yana zarginta da ko tana yawon banza tun da bai same ta a matsayin wacce ba ta taba aure...
    Kungiyar Kananan Hukumomin Nijeriya (ALGON) reshen Jihar Kaduna, ta mika sakon taya murna ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa lambar karramawa ta CON da shugaban kasa ya yi masa ado da ita, wacce ke matsayin wata alamar girmamawa a Jamhuriyyar Nijeriya ta Hudu. Wannan karramawar, wata alama ce a sarari ga sadaukarwar mai...