AU, ta yi tir da harin baya bayan nan a tashar ruwan Sudan
Published: 6th, May 2025 GMT
Kungiyar Tarayyar Afrika (AU), ta yi tir da hari na baya-bayan nan da aka kai Port Sudan, muhimmin birni a kasar Sudan dake cikin ’yan kalilan da yakin da ake yi a kasar bai shafa ba.
Port Sudan ya taka muhimmiyar rawa a matsayin cibiyar jigila da ayyukan agaji, yayin da ake ci gaba da gwabza fada a Sudan.
Kungiyar AU mai mambobi 55 ta yi gargadin cewa, kai hari birnin zai kawo tsaiko ga kokarin da ake yi na wanzar da zaman lafiya a kasar.
Rahotanni daga kafafen yada labarai na cewa, kungiyar RSF ta kai hari da jirgi mara matuki zuwa filin jirgin sama na sojoji, da sauran wuraren dake filin jirgin sama na kasa da kasa na Port Sudan, a ranar Lahadi.
An ce harin shi ne irinsa na farko da RSF din ta kai Port Sudan
Kafafen watsa labaran cikin gida sun ba da rahoton kai hari tashar jiragen ruwa da wasu gine-ginen gwamnati.
An ji tare da ganin fashewar bama-bamai da wuta nan da can a birnin na Port Sudan, wanda wannan shi ne kwana na uku a jere da birnin ke shan ruwan bama-bamai da ake kai harin ta hanyar kananan jiragen sama marassa matuka, kamar yadda wasu kafofin watsa labarai na kasar ke bayyanawa.
Su ma makwabtan kasar ta Sudan, Masar da Saudiyya sun yi Alllwadarai da hare haren , ita ma majaliasar dinkin duniya ta nuna damuwa a kai.
Tun watan Afirilu na 2023 Sudan ta fada wannan mummuna yakin basasa tsakanin kungiyar ta RSF da kuma rundunar sojin kasar wadanda a da suke tare – rikici kann sabanin mayar da mulki tsarin farar hula ya raba kansu.
Rikicin ya raba mutum ,iliyan 12 da muhallinsu kuma ya jefa rabin yawan alummar kasar cikin matsananciyar yunwa, kamar yadda majalaisar dinkin duniya ta ce.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce alkaluman baya bayan nan da aka fitar cikin Mujallar Economist, sun shaida yadda hada-hadar cinikayyar fitar da hajoji ta kasar Sin ke kara bunkasa cikin sauri a shekarar nan ta bana, inda fannin ke samun karuwar abokan hulda, da daidaiton matsayi cikin tsarin samar da hajojin masana’antu na kasa da kasa.
Kakakin ya kara da cewa, kasashen duniya suna maraba da hajojin kasar Sin, kuma yakin ciniki da haraji ba su yi wani babban tasiri kan kasar Sin ba. A fannin hada-hadar cinikayya, sanya shinge ba alama ce ta karfin gwiwa ba, kuma katangar da Amurka ke ginawa kanta, daga karshe za ta illata karfinta ne.
Lin Jian, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa a yau Laraba, ya ce yayin da ake fama da yanayi mai sarkakiya, da sauye-sauye masu maimaituwa daga ketare, cinikayyar waje ta Sin na gudana lami lafiya, cike da karfin juriya da babban karsashi.
Hakan a cewarsa, ya shaida gazawar yakin haraji da cinikayya wajen girgiza fifikon da Sin ke da shi, a fannin raya masana’antun sarrafa hajoji da kasar ta gina a tsawon lokaci. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp