PTAD Ta Dora Laifin Jinkirin Biyan Fansho Kan CBN, Ta Bukaci Hakuri
Published: 5th, May 2025 GMT
Hukumar Tsare-Tsaren Biyan Fansho PTAD ta nesanta jami’anta daga laifin jinkirin biyan hakkokin tsofaffin ma’aikata masu ritaya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja, hukumar ta bayyana cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ne ke da alhakin kai tsaye wajen tura kudaden fansho zuwa asusun tsofaffin ’yan kasa.
PTAD ta roƙi afuwa kan jinkirin da aka samu, tana mai kira ga masu karban gansho da su jira shigowar kudi daga CBN, tana mai jaddada cewa an kammala dukkan shirye shirye da suka wajaba tun da farko.
Wasu daga cikin tsofaffin ma’aikatan FRCN da NTA Kaduna sun bayyana bacin ransu kan ci gaba da jinkirin biyan hakkokinsu, musamman ganin cewa tsofaffin sojoji sun riga sun karɓi nasu hakkokin tun watannin baya, abin da suka kira abin takaici.
Wadanda abin ya shafa sun kuma jaddada goyon bayansu ga zanga-zangar da aka shirya gudanarwa mako mai zuwa, idan Ma’aikatar Kudi ta Tarayya ta kasa shawo kan matsalar cikin gaggawa.
SULEIMAN KAURA
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
HOTUNA: Yadda aka baje kolin kayan laifin da ’yan sanda suka kama a Abuja
Kalli ya da Kwamishinan ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya, Ajao Saka Adewale, ya yi hole ababen hawa da sauran kayan laifi da rundunarsa ta kama a gaban ’yan jarida a ranar Juma’a.
Hotuna: Abubakar Sadiq Isah.