Bisa kididdigar da kamfanin layin dogo na kasar Sin ya fitar, daga fara zirga-zirgar hutun ranar ma’aikata a ranar 29 ga Afrilu zuwa ranar 4 ga Mayu, jiragen kasa na kasar Sin sun yi jigilar fasinjoji miliyan 112, adadin da ya karu da kashi 10.5 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, tare da tabbatar da zirga-zirga cikin aminci, kwanciyar hankali da kuma tsari.

A yau, yawan fasinjojin da ke kan hanyarsu ta dawowa daga hutun ta jiragen kasa na ci gaba da karuwa, inda a yau ake sa ran za a yi jigilar fasinjoji miliyan 21.1 ta hanyar jirgin kasa na kasar, yayin da ake shirin kara jiragen kasan fasinja 1896 a kan adadin jiragen da ake amfani da su a baya wajen jigilar fasinjoji. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Sin Sun Samar Da Sabuwar Hanyar Sufuri Ga Al’Ummun Kasashen Shiyyar Tsakiyar Asiya

A watan Afrilun bana, wata farar mota kirar bas mai tsawo mita 12, ta yi tafiya a kan titunan Ashgabat, hedkwatar kasar Turkmenistan. Bas din da kamfanin Yutong na kasar Sin ya kera ta dace da ma’aunin kiyaye muhalli da kasar ta tanada, kuma tana dauke da na’urar ba da jagorancin sufuri mai amfani da tauraron dan Adam, da na’urar biyan kudi ta yanar gizo, matakin da ya bullo da sabuwar hanyar zirga-zirga ga jama’ar wurin.

A wannan shekara, Sin za ta samar da irin wannan bas har 700 ga Ashgabat, matakin da zai biya bukatun zirga-zirgar jama’ar kasar da yawansu ya zarce miliyan 1.

Tun da aka bude taron koli na Sin da kasashen shiyyar tsakiyar Asiya karon farko a shekarar 2023, Sin da kasashen shiyyar Asiya, sun rika bullo da boyayyen karfin hadin gwiwarsu, sun kuma cimma nasarar fitar da sabuwar hanyar hada hannu ba tare da gurbata muhalli ba.

Daga cikin bangarorin hadin gwiwarsu, sana’ar kera motoci na kan gaba. Kamfanonin Sin da dama sun kafa sassansu a wuri, matakin da ya zurfafa hadin gwiwarsu, da samarwa jama’ar wurin wata sabuwar hanyar zirga-zirga, har ma ya samar da karin guraben aikin yi, da karawa jama’ar wurin kudin shiga, kana da horar da ma’aikata a wannan sana’a, matakin da ya kara bunkasa kwarewarsu. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Bikin Ranar Muhalli Ta Duniya: Akwai Babban Aiki A Gaban Nijeriya
  • Indomie Arewa Ta Ƙaddamar da AI Career Generator Domin Ranar Yara
  • Gwamnatin Tarayya Da Jamus Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Yuro Miliyan 20 A Ɓangaren Makamashi
  • Sin Ta Fadada Matakin Rage Haraji Ga Kasashe Masu Raunin Tattalin Arziki
  • Guguwar ruwan sama ta yi ɓarna a Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Kogi
  • Za a dawo da dukkan Alhazai gida ranar 28 ga Yuni – NAHCON
  • Kotun Amurka ta daure ’yan Najeriya 5 shekaru 159 kan aikata damfara
  • Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Sin Sun Samar Da Sabuwar Hanyar Sufuri Ga Al’Ummun Kasashen Shiyyar Tsakiyar Asiya
  • Sin Za Ta Samar Da Cibiyar Kasa Da Kasa Ta Gudanar Da Hada-hadar Kudin RMB Na Dijital
  • Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mutum 20 a Chadi