Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Janyo Shahadan Falasdinawa 50 A Yankin Zirin Gaza
Published: 6th, May 2025 GMT
Falasdinawa fiye da 50 ne suka yi shahada yayin da wani adadi da dama suka jikkata a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai Gaza a jiya Litinin
Rahotonni sun bayyana cewa: Fiye da Falasdinawa 50 ne aka suka yi shahada wasu adadi da dama kuma suka jikkata sakamakon hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila ke ci gaba da kai kan yankin Zirin Gaza na Falasdinu.
A wani labarin kuma, Falasdinawa a yankin Al-Karama da ke arewacin zirin Gaza sun farka da wani sabon kisan kiyashi da jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi bayan da suka kai hari kan wani ginin fararen hula, lamarin da ya yi sanadiyar shahadan Falasdinawa da dama da kuma jikkata.
A tsakiyar daren jiya ne jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai hare-hare kan wani gini mai hawa uku, inda suka yi sanadiyyar shahada Falasdinawa kusan 20, kuma har yanzu ba a gano wasu gawarwakin ba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila suka
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Hamas Ta Sanar Da Matsayinta Kan Shirin Dakatar Da Bude Tsakaninta Da Gwamnatin Mamayar Isra’ila
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta sanar da cewa: Ta gabatar da martani mai kyau ga shawarar dakatar da bude wuta tsakaninta da gwamnatin mamayar Isra’ila
Kungiyar Hamas ta sanar da kammala tuntubarta tare da gabatar da kyakkyawar amsa ga sabuwar shawarar neman dakatar da bude wuta, inda ta bayyana shirinta na nan take na yin shawarwari kan tsarin aiwatarwa.
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci a Falastinu ta Hamas ta sanar a yammacin jiya Juma’a cewa ta kammala shawarwarin cikin gida da kuma tuntubar wasu bangarori da dakarun Falasdinawa dangane da sabuwar shawara da masu shiga tsakani suka gabatar na dakatar da hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Falasdinu a zirin Gaza.
Kungiyar ta yi nuni da cewa ta mika martanin ta ga ‘yan uwanta da ke shiga tsakani, inda ta tabbatar da cewa martanin yana da kyau. Ta sake nanata cewa a shirye take ta gaggauta shiga wani zagaye na tattaunawa kan hanyoyin aiwatar da wannan tsarin.
A cikin wannan mahallin, kafofin watsa labaru na haramtacciyar kasar Isra’ila sun ba da rahoton cewa, an sami wasu muhimman sauye-sauye a daftarin na Witkoff, wanda dukkansu ke goyon bayan Hamas.