Kawancen Jam’iyyun Adawa A Kasar Ivory Coast Ya Bukaci Gyara Wa Tsarin Zabe Kasar
Published: 6th, May 2025 GMT
Kawamcen jam’iyyun siyasa na kasar Ivory Coast ya bukaci a sake lalen yadda aka tsara yadda ake ristar jam’iyyu a hukumar zaben kasar, ganin yadda ta hana rijistar wasu jam’iyyun saboda dalilai daban daban.
Shafin yanar gizo na labarai Afirka news ya bayyana cewa an kafa kawancen ne wanda aka sanyawa suna CAP-CI a farkon wannan shekarar, don tunkarar zaben shugaban kasa wanda za’a gudanar a ranar 25 ga watan Octoban shekara ta 2025 da muke ciki.
Kawancen CAP gamayyar jam’iyyun adawa da dama ne na kasar, in banda Jam’iyyar da Lauranta Bagbo a kafa don tunkarar zaben na watan Octoba. Har’ila yau kawancen na zargin hukumar zaben kasar da rashin adalci a yadda take amincewa da yan takara a zaben. A ranar 31 ga watan Mayun da muke cikin ne kawancen jam’iyyun adawar zasu gabatar da taronsu na farko don tattauana wadan nan matsaloli, da kuma yadda zasu tunkari gwamnati mai ci da kuma hukumar zabe don warwaresu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan Trump
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya November 3, 2025
Ra'ayi Riga Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki November 3, 2025
Manyan Labarai Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro November 3, 2025