Syria: A Karon Farkon Jirgi Mai Saukar Angulu Na HKI Ya Sauka A Yankin Suwaidah
Published: 3rd, May 2025 GMT
Ana ci gaba da yin kiraye-kiraye ga HKI da ta kawo karshen hare-haren da take kai wa kasar Syria,jim kadan bayan da sojojin HKI su ka sanar da cewa; a karon farko jirgin sama maras matuki na ‘yan sahayoniya ya sauka a Suwaidah.
A daren jiya Juma’a ne dai HKI ta kwana tana luguden wuta akan yankuna mabanbanta na kasar ta Syria da su ka hada da birnin Damascuss har da daura fa fadar shugaban kasa.
HKI tana kai wannan hare-haren ne dai da sunan bayar da kariya ga ‘yan Duruz domin hana sojojin Syria ci gaba da kai musu hare-hare.
Jami’in diplomasiyyar MDD mai kula da kasar Syria Geir Otto Pedersen ya rubuta a shafinsa na X sakon yin tir da keta hurumin kasar Syria da Isra’ila take yi da su ka hada da birnin Damascus.
Haka nan kuma jami’in na MDD ya yi kira da a kawo karshen wadannan hare-haren akan Syria, da kauce kai wa farafen hula hari. Bugu da kari ya bayyana kai harin da cewa keta dokokin MDD ne da kuma kokarin hana tarwatsewar hadin kasar da ‘yancinta.
HKI ta bude kai hari ne akan kasar Syria da sunan kare ‘yan Duruz, da hakan yake kama hanya ce ta tarwatsa Syria da mayar da ita kananan kasashe.
Dama dai tun farko-farkon faduwar gwamnatin Syria, HKI take aiki tukuru domin ganin kasar ba ta ci gaba da zama a dunkule ba, ta tarwatse ra koma kananan kasashe.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Syria
এছাড়াও পড়ুন:
Pakistan Ta Yi Gwajin Makami Mai Linzami Mai Cin Tazarar Kilo Mita Fiye Da 400
Sojojin kasar Pakistan sun sanar da yin nasarar gwajin makamai mai linzami da ake harbawa daga kasa, wanda yake cin Zangon kilo mita 450.
Sanarwar sojojin kasar ta Pakistan ya kunshi cewa; Sun yi gwajin ne dai domin tabbatar da zama cikin shiri na sojoji, da kuma tabbatar da ingancin aikin makamin.
Gwajin makamin na sojojin Pakistan ya zo ne a daidai lokacin da ake zaman dar-dar a tsakaninta da kasar Indiya, bayan wani harin ta’addanci da aka kai a yankin Kashmir.
A ranar 22 ga watan Afrilu ne dai aka kai wani hari akan masu yawon bude ido a yankin na Kashmir wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane 26. Da akwai fargabar cewar kasashen biyu za su tsunduma cikin wani sabon yaki,bayan da Indiya ta zargi Pakistan da cewa tana da hannun a wancan harin.
Pakistan dai ta kore cewa tana da hannu, tare da yin kira ga Indiya da ta kaucewa tsokana, domin za ta mayar da martanin da ya dace gwargwadon harin da za ta kai mata.
Mahukuntan kasar Pakistan sun gargadi Indiya akan cewa, su kwana da sanin cewa; Islamabad tana da makaman Nukiliya.
A yau Asabar an yi musayar wuta a tsakanin sojojin kasashen biyu a tsawon yankin da ya raba su a yankin Kashmir.
A jiya Juma’a mahukunta a yakin Kashmir sun yi kira ga mazauna yankin da su tanadi abincin da zai ishe su na tsawon watanni biyu,saboda tsoron yiyuwar barkewar yaki a tsakanin kasashen biyu masu karfin Nukiliya.