Sharhin Bayan Labarai: Ranar Malami A Kasar Iran
Published: 4th, May 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana ne a kan Aya. Shahid Mttahari, shahidi na farko daga cikin malamai jagororin juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran a shekara 1979.
A jiya Jumma ce 2 ga watan Mayu na wannan shekara ta 2025 aka yi juyayin shahadar malami na fadrko wanda ya kai ga shahada bayan nasaral juyin juya halin musulunci a nan iran.
Aya. Murtadha Muttahari, malami marubuci sannan jagora mai farkar da mutane a Iran da sauran kasashen duniya ta hanyar alkalaminsa da kuma jawabansa na shekaru masu yawa.
Kafin juyin juya halin musulunci a nan Iran shekaru 46 da suka gabata, Aya, Muttahari ya zama fitilla ga mutane da dama a nan kasar Iran, musamman daliban Jami’I’oo a nan Iran kuma musamman daliban Jami’ar Tehran wadanda ya dauki shekari kimani 23 yana karantar da ilmin addinai da kuma falsafa.
Shaida Muttahari ya rubuta littafai a fannoniun ilmi da dama , kama daga Fikihu, akidu, falsafatarihi da sauransu kuma ya karantar da su. Banda haka shi jagora ne na fada da azzaluman shugabannni a karni na 20 da ya gabata.
Sanaiyyar wadannan al-amura da Shahid Muttahari aka sanya ranar 2 ga watan Mayu na ko wace shekara tun bayan shahadarsa a matsayin ranar Malami.
Aya. Mutahhari ya barman littafan da ya rubuta fiye da 100 kuma an tarjama wasunsu zuwa harsuna da dama a duniya. Wadannan littafan sun zama fitila wadanda suka farkar da mutanen da dama a ko ina a duniya.
Wani mai tarjamar Littafai a kasar Malasiya Seyyed Sheikh ibn Seyyed Mostafa, ya ce shi kadai ya tarjama littafan Shahid Mutahhari har guda 70, amma har yanzin ana bukatar littafan sa, a kasuwan. A bangaren ikida wasu malaman addini sun bayyana cewa ba wanda masana a kasahen yamma suka fahinci falsafan addinin musulunci kamar yadda suka fahinta a littgafan shaida muttahari.
Wata kungiyar batacciya a lokacin a nan Iran wacce ake kira Furkan ne ta sa daya daga cikin mabiyanta ya zo ya bindige shahid Muttahiri a kusa da gidansa a nan Tehran kwanaki 80 kacal da samun nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran a shekara 1979. Da wani dalili wannan kungiyar ta kasheshi, Al..ya sani. Da fatan All..ya hasakak kabarinsa ya sa mu kara fahintar ilmin da ya bara mana.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: juyin juya halin musulunci a nan
এছাড়াও পড়ুন:
Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Zurfafa Dunkulewar Kasuwannin Kasa Ta Bai Daya”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp