HausaTv:
2025-05-05@18:30:15 GMT

 Kotun Duniya Ta Wanke HDL Akan Zargin Kisan Kiyashi A Sudan

Published: 5th, May 2025 GMT

Kotun duniya ta yi watsi da karar da Sudan ta kai Hadaddiyar Daular Larabawa tana mai zarginta da hannu a kisan kiyashin da aka yi wa al’ummar wannan kasa.

A yau Litinin ne kotun duniyar ta yi watsi da karar ta Sudan, tana mai wanke Hadaddiyar Daular Larabawa.

Ita dai Sudan ta zargi Hadaddiyar Daular Larabawar da cewa ta hada baki da dakarun kai daukin gaggaawa wajen yi wa mutanen yankin Darfur kisan kiyashi.

A nata gefen Hadaddiyar Daular Larabawan ta ki amincewa da tuhumar da Sudan ta yi mata  tana mai siffata ta da cewa; Farfaganda ce, kuma Sudan din ta yi hakan ne domin kawar da hankulan duniya daga kan laifukan da sojoji suke aikatawa.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Hadaddiyar Daular

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda ’yan fashi suka yi wa mafarauta kisan gilla a Bauchi

’Yan fashi sun harbe mafarauta da fararen hula kimanin 19 har lahira a Karamar Hukumar Alƙaleri ta Jihar Bauchi.

A yayin ziyarar da ya kai wurin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya ba da umarnin yin cikakken bincike da kuma tura karin jami’an tsaro yankin.

Mazauna kauyen Mansur sun ce an kashe ’yan farauta guda tara da kuma fararen hula guda goma, kuma an yi jana’izar ’yan bangar a kauyen Mansur kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Amma ’yan sanad da jami’an Ƙaramar Hukumar Alƙaleri ba su ce komai ba kan adadin mamatan ba.

Kakakin ’yan sanda na jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce kwamishinan ya tattauna da masu ruwa da tsaki a yankin, inda ya buƙaci jama’a kwantar da hankalinsa, ya kuma kasance a cikin shiri, tare da bai wa ’yan sanda goyon baya wajen gudanar da binciken su.

Kwankwaso: Abba ya mayar wa Baffa Bichi martani Umaru ’Yar’adua da shugabannin Najeriya da suka rasu a kan mulki NAJERIYA A YAU: Abin da ke kai matasan Najeriya ci-rani wasu ƙasashen Afirka

Wakil ya ce, “A ranar 4 ga watan Mayu, 2025 mun samu rahoto cewa tawagar hadin gwiwar mafarauta daga Duguri da Gundumar Gwana, da ke sintiri a kan hanyar Duguri, Mansur, da dajin Madam da ke kan iyakar jihar Bauchi da Filato, sun yi araba da ’yan fashi, inda a arangamar aka kashe mutane da dama daga bangarorin biyu.

“Mun tura tawagar jami’an tsaro wurin, inda suka gano gawarwakin jami’an tsaro da fararen hula daga kauyen Sabuwar Sara, wadanda ’yan fashin suka harbe su a yayin da suke kokarin tserewa daga harin suka mutu.

“Rundunar ta tura tawaga ta musamman domin kamo duk masu alaƙa da wannan aika-aika.”

Ya kuma ba da  tabbacin cewa za a yi bincike cikin gaskiya da adalci domin gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban ƙuliya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda ’yan fashi suka yi wa mafarauta kisan gilla a Bauchi
  • ’Yan fashi sun yi wa mafarauta kisan gilla a Bauchi
  • Kotu za ta rataye matashi kan kisan karuwa
  • Iran ta watsi da zargin Isra’ila da Amurka cewa ta na da hannu a harin ramuwar gayya na Yemen
  • Yau Kotun ICJ ke yanke hukunci kan zargin da Khartoum ke wa UEA
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce Masifar Yunwa Ta Kara Yin Kamari A Yankin Zirin Gaza Na Falasdinu
  • Maganin Kurajen Fuska
  • Sin: Adadin Tafiye-tafiye Yayin Ranakun Hutun Murnar Ranar ‘Yan Kwadago Ta Duniya Ya Kafa Tarihi 
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Tattauna Da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kan Zaman Tattaunawan Amurka Da Iran