An kammala Bada Horo Ga Matan Sojojin Runduna Ta 8 Da Ke Sakkwato
Published: 4th, May 2025 GMT
Babban kwamandan runduna ta 8 ta sojojin Najeriya Manjo Janar Ibikunle Ajose ya shawarci matasa a yankunan su rungumi horar da sana’o’in hannu domin inganta zamantakewa da ci gaban tattalin arziki a kasar nan.
GOC ya yi nasihar ne a wajen bikin yaye kungiyar matan jami’an rundunar soja ta 8 a cibiyar koyar da sana’o’i ta jihar Sokoto.
GOC wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban ma’aikata da dabaru, Kanar Raphael Olugbenga Adeyemi, GOC ya bayyana cewa, a cikin saurin ci gaban fasahar kere-kere da ci gaba da kasancewa cikin al’umma ya ta’allaka ne kan koyon sana’o’i.
Ya kara da cewa koyon fasahohin sana’o’in zai kawo ci gaba da jajircewar matasa a cikin al’umma.
A nata jawabin shugabar kungiyar Misis Meg Ndidi Ajose, uwargidan GOC ta bayyana farin cikinta tare da yabawa daliban da suka yaye bisa jajircewarsu wajen ciyar da kansu gaba.
Shugabar wadda Misis Fatima Abass ta wakilta, ta bayyana cewa cibiyar koyar da sana’o’i tana kokarin taimakawa matasa su zama masu dogaro da kai da kawo sauyi ga al’umma a yankin.
Uwargida Ajose ta yi tsokaci ne ga malamai da masu gudanar da ayyukan bisa jajircewar da suka yi wajen karfafa mata da matasa a bariki da kewaye.
Gidan rediyon Najeriya dake Sokoto ya ruwaito cewa daliban da suka kammala karatun sun samu horon ne daga sashen kere-kere da kayan abinci da hada jakunkuna da kayan kwalliya da dai sauransu.
NASIR MALALI
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Sakkwato
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Sha Alwashin Inganta Kwazon Kananan Hukumomin Jihar
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na bada managartan shawarwari da za su yi wa kananan hukumomin jihar jagoranci wajen gudanar da ayyukan su kamar yadda yakamata.
Shugaban Kwamatin Kananan Hukumomi na Majalisar, Alhaji Aminu Zakari, ya bada wannan tabbacin lokacin rangadin kwamatin majalisar a sakatariyar karamar hukumar Birniwa.
Alhaji Aminu Zakari Wanda shi ne wakilin mazabar Gwiwa, yace ziyarar Kwamatin na daga nauyin da aka dorawa bangaren majalisa wajen bibiyar yadda Gwamnati ta ke aiwatar da manufofi da shirye shirye domin tabbatar da shugabanci nagari.
Alhaji Aminu Zakari yace haka kuma Kwamatin yana la’akari da batun zamantakewar jama’ar da tattalin arziki a matsayin ma’aunin ci gaban rayuwa da koma bayana domin baiwa bangaren zartaswa shawarwari dan bullo da manufofi da shirye shiryen da za su dace da bukatun Jama’a.
Yace , ziyarar na bada damar ganawa da bangaren zartaswa da na kansiloli da ma’aikata domin tabbatar da tsarin aiki tare ta hanyar kyakkyawar fahimtar juna.
A daya bangaren kuma, kananan kwamitocin da Babban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawan ya kafa, sun sami nasarar tantance ayyukan raya kasa da karamar hukumar Birniwa ta gudanar a sassan yankin daga watan Oktobar 2024 kawo yanzu.
Karamin Kwamati na daya, bisa jagorancin wakilin mazabar Alhaji Muhammad Abubakar Sa’id ya duba aikin Masallacin kamsissalawati na Kakori, da gyaran masallacin juma’a na Malandi, da sanya fitilu masu amfani da hasken rana a Taljari da shaguna da rumfuna a kasuwar Birniwa da wasu muhimman wurare da suka hada da gyaran gidajen karamar hukumar da gyaran kotun shari’a a Birniwa.
Karamin Kwamati na biyu bisa jagorancin wakilin mazabar Guri, Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari, ya duba aikin gina shago guda biyar a bakin Babban titin garin Birniwa da shaguna da rumfuna da cikon kasa a garin Kupsa da masallacin kamsissalawati a kauyen Garuba.
Kazalika, ziyarar Kwamatin ta duba batun daukar malaman duba gari 22 da Gina ajujuwa a makarantun ‘Yayan fulani.
Tunda farko, shugaban karamar hukumar Birniwa, Malam Shehu Baba Birniwa, ya bayyana aniyarsa ta aiki da shawarwarin Kwamatin domin cigaban karamar hukumar sa.
Malam Shehu Baba ya ce tun daga kama mulkinsa ya bar kofar sa a bude da nufin cusa dabi’ar aiki tare da masu ruwa da tsaki a matsayin turba mai sauki wajen gudanar da mulkin karamar hukumar.
Usman Mohammed Zaria