Iran Ta Mayar Da Martani Akan Zarginta Dangane Da Yemen
Published: 5th, May 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi watsi da zarge-zargen da aka yi ma ta dangane da kasar Yemen.
A wani bayani da ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran din ta fitar ta bayyana cewa: Abinda mutanen Yemen suke yi domin taimakawa al’ummar Falasdinu, mataki ne na kashin kansu da su ka dauka cikin ‘yanci saboda lamirinsu na ‘yan adamtaka da kuma taimako na musulunci ga ‘yan’uwansu Falasdinawa.
Bayanin ya kuma ci gaba da cewa; Jinginawa jamhuriyar musulunci ta Iran abinda mutanen na Yemen suke yi, ba shi da tushe, kuma manufar hakan ita ce, rufe laifukan da ‘yan sahayoniya suke yi a Falasdinu.”
Bayanin ya kuma ce; Jamhuriyar musulunci tana sake jaddada matsayarta akan wajabcin kiyaye da karrama kasashe da kasantuwarsu a dunkule a wuri daya, kamar kuma yadda muke yin tir da hare-haren sojan Amurka akan Yemen, domin hakan take dokokin MDD ne, da kuma dokokin kasa da kasa.”
Haka nan kuma ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta yi kira da a kawo karshen kisan kiyashin da ‘yan sahayoniya suke yi wa Falasdinawa da shi ne tuhsen rashin zaman lafiya a cikin wannan yankin na yammacin Asiya.
Wani sashe na bayanin na ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran din ya ce; al’ummar Iran a shirye suke, su kare kansu daga duk wata barazana akan manufofin kasa, kuma alhakin duk abinda zai faru yana wuyan hukumomin ‘yan ta’adda na Amurka da sahayoniya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: ma aikatar harkokin wajen
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Jaddada Cewa: Kungiyoyin Gwagwarmaya Ba Su Karbar Umarni Daga Wani Bangare, Gashin Kansu Suke Ci
Iran ta mayar da martani kan zargin da ake mata game da alakar ta da Yemen tana cewa; Taimakon da Yemen ke yi wa Falasdinu hukunci ne mai cin gashin kansa
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da wata sanarwa dangane da zargin da ake yi wa Iran dangane da alakar da ke tsakaninta da kasar Yemen, inda ta yi la’akari da wadannan tuhume-tuhumen a matsayin maimaita zargin karya da nufin karkatar da hankali daga laifukan yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya.
A sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ta ce: Wadannan tuhume-tuhume ne da maimaita zarge-zargen karya da ke alakanta matakan gwagwarmaya da al’ummar Yemen suka dauka na kare kansu da kuma goyon bayan al’ummar Falastinu ga Iran. Wannan cin mutunci ne ga al’umma masu yakar zalunci.
Sanarwar ta kara da cewa: Amurka ta hanyar goyon bayan kisan kiyashin da yahudawan sahayoniyya suke yi, ita ce ta shiga yakin da take yi da al’ummar kasar Yemen, kuma tana aikata laifukan yaki ta hanyar kai hare-hare kan ababen more rayuwa da farar hula a garuruwa daban-daban na kasar ta Yamen. Harkar Yemen na goyon bayan Falasdinawa wani mataki ne mai cin gashin kansa, wanda ya samo asali daga zurfin jin kai da kuma fahimtar Musulunci na hadin kai da al’ummar Falasdinu da ke da alhakin wannan mataki na Iran.