HKI Ta Tabbatar Da Halakar Sojojinta 2 A Yankin Rafa Na Zirin Gaza
Published: 4th, May 2025 GMT
Gwamnatin HKI ta bada sanarwan halakar sojojinta biyu da kuma jikatan wasu alokacinda suke bincike da kuma kokarin shiga wani rami na karkashin kasa a inda wani bom ya tashi ya kashe su ya kuma raunata wasu.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakafen yana labaran yahudawan na fadar haka a safiyar yau kuma wadanda aka rutsa da su sun hada da Captain Noam Ravid, dan shekara 23 a duniya da kuma Staff Sergeant Yaly Seror, dan shekara 20 a duniya.
Labarin ya kara da cewa hatsarin ya faru ne a jiya asabar, sannan wasu sojoji biyu daga rundunar Yahalom sun ji rauni.
Tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ne aka fara yakin tufanul Aksa, inda sojojin yahudawan tare da taimakon kasashen yamma suka fara kisan kiyashi ga Falasdinawa a yankin, wanda ya kaiga shahadar mutane 52,495 ya zuwa yanzu. Sannan wasu 118,366 suka ji rauni.
An dan tsaida yaki daga ranar 19 ga watan Jenerun wannan shekara har aka kai wata marhala sai HKI ta tsaida aiwatarda yarjeniyar. Sannan ta sake komawa yaki.
An kashe sojojin yahudawa fiye da 850 daga ciki har da sojojin kasa 414 a yankin na Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Uganda Ta Jinjinawa Gudummawar Sin Ga Manufofin Wanzar Da Zaman Lafiya A Yankin Kahon Afirka
A nasa tsokaci game da batun, wakilin musamman na kasar Sin a yankin kahon Afirka Xue Bing, ya ce Sin ta dade tana goyon bayan matakan wanzar da zaman lafiya da ci gaba a yankin. Ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa ta fuskar shawo kan tarin kalubale dake addabar duniya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp