HausaTv:
2025-08-03@01:20:19 GMT

Iran : Araghchi zai ziyarci Pakistan da Indiya

Published: 4th, May 2025 GMT

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi yana shirin kai ziyara a kasashen Pakistan da Indiya a wannan makon a wani bangare na tuntubar juna tsakanin Tehran da kasashen yankin.

Ministan harkokin wajen Iran din zai isa Pakistan a ranar Litinin 5 ga watan Mayu, domin tattaunawa da manyan jami’an kasar.

Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da sabbin ci gaban yanki da na kasa da kasa, in ji kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, kafin ya tabbatar da cewa Mr. Araghchi zai kai ziyarar aiki a Indiya nan gaba a cikin mako.

Ziyarar na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun takun saka tsakanin Indiya da Pakistan, kasashe biyu masu makamin nukiliya.

Wannan tashin hankalin dai ya ta’azzara ne sakamakon harin  da aka kai a yankin Kashmir da ke karkashin ikon Indiya a ranar 22 ga watan Afrilu, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 26.

Indiya dai na zargin Pakistan da hannu a harin, zargin da Pakistan din ta musanta.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da firaministan Indiya Narendra Modi a ranar 26 ga watan Afrilu, shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da harin, yana mai jaddada bukatar hadin gwiwa da yaki da ta’addanci.

A wata tattaunawa ta daban ta wayar tarho da firaministan Pakistan Shehbaz Sharif a wannan rana, Mr. Pezeshkian ya bayyana matukar damuwarsa kan yadda ake kara samun takun saka tsakanin Indiya da Pakistan.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

INEC za ta fara rajistar ƙuri’a a ranar 18 ga Agusta

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), za ta fara rajistar ƙuri’a ta intanet a ranar 18 ga watan Agusta, 2025, domin tunkurar zaɓen 2027.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma da Hukumar NOA ta masa a hedikwatar INEC da ke Abuja.

Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansaninta a Kebbi Ɗaliban da aka sace a Binuwai sun kuɓuta 

Ya kuma ce sai a ranar 25 ga watan Agusta, 2025 za a fara rajistar ƙuri’a a zahiri.

“Za a fara rajistar ƙuri’a ta Intanet a faɗin ƙasa daga ranar 18 ga watan Agusta,” in ji Farfesa Yakubu.

“Rajistar ƙuri’ar a zahiri kuma za ta fara daga 25 ga watan Agusta, 2025,” a cewarsa.

Hukumar INEC na shirin fara wannan rajista ne domin zaɓen gwamnan Jihar Anambra da za a yi a ranar 8 ga watan Nuwamba, 2025, da kuma babban zaɓen 2027.

INEC da NOA sun amince da ci gaba da yin haɗin gwiwa a fannin wayar da kai game da harkokin zaɓe da amfani da ƙirƙirarriyar fasaha (AI) don bunƙasa harkokin zaɓe.

“Ayyukan gudanar da zaɓe ba za su yi tasiri ba sai an wayar da kan ‘yan ƙasa, kuma wannan shi ne babban aikin NOA a Najeriya,” in ji Farfesa Yakubu.

Shugaban NOA, Malam Lanre Issa-Onilu, ya ce suna kan aikin yin gyara da sabunta ayyukansu domin amfanar da dimokuraɗiyya.

Ya ce yanzu NOA na da sassa 16 da ke kula da shirye-shirye, ciki har da sabuwar Ma’aikatar Koyar da Darusan Dimokuraɗiyya.

“A yanzu muna da sassa 16, ciki har da sabuwar Ma’aikatar Koyar Darusan Dimokuraɗiyya,” in ji shi.

INEC ta buƙaci NOA ta ci gaba da amfani da kafafen watsa labarai da na zamani don jawo hankalin mata, matasa da nakasassu don shiga harkokin zaɓe.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Pezeskkian Ya Ce: Suna Fatan Musayar Kasuwancin Tsakanin Iran Da Pakistan Ta Haura Dala Biliyan 10
  • Araqchi: Abokantaka Da Ke Tsakanin Iran Da Pakistan Wata babbar Jari Ce Nan Gaba
  • Sin Ta Kadu Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Wa Hukumomi Da Jami’an Falasdinu
  • INEC za ta fara rajistar ƙuri’a a ranar 18 ga Agusta
  • Sin Ta Samarwa Sassan Kasa Da Kasa Damar Shigowa Ba Tare Da Bukatar Biza Ba
  • Shugaban Kasar Iran Zai Ziyarci Pakistan A Gobe Asabar
  • Ministan Harkokin Wajen Siriya Yana Rasha Don Bude Sabon Shafi Tsakaninsu
  • Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Ziyarci Jama’a, Ya Daina Sauraron Gwamnoni — ADC
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Mata
  • Tawagar Iran Ta Fice A Taron Majalisun Dokokin Kasashen Duniya A Lokacin Jawabin Wakilin Isra’ila