An kashe mutum 6 a sabon hari a Filato
Published: 6th, May 2025 GMT
Akalla mutum shida ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani sabon hari Karamar Hukumar Barikin Ladi da ke Jihar Filato.
’Yan bindigar sun kuma jikkata mutane da dama a hare-haren da suka kai unguwannin Marit da Gashish a ranar Litini.
Aminiya ta samu labarin cewa an garzaya da wadanda suka ji raunin asibiti, bayan harin da aka kai a yayin da mutane suke tsaka da barci a cikin dare.
Shugaban Karamar Hukumar Barikin Ladi, Hon. Stephen Pwajok Gyang, ya bayyana cewa an riga an yi jana’izar mamatan yana mai yin Allah wadai da harin.
Hajj 2025: Maniyyatan Kaduna za su fara tashi ranar 14 ga watan Mayu Wata mata ta auri maza biyu a lokaci guda a Kano NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ‘Yan Gwagwarmaya Ke Shiga Tasku A Najeriya?A yayin ziyarar dubiya da ya kai Babban Asibitin Barikin Ladi, Hon. Pwajok ya nuna takaici bisa yadda bata-gari ke mayar da hannun agogo, duk da kokarin da hukumomi ke yi na tabbatar da zaman lafiya a karamar hukumar.
Ya yi wa majinyata addu’ar samun sauki da kuma rahama ga mamata, tare da jinjina wa kokarin ’yan banga da sauran jam’an tsaro a yankin.
Wannan hari na zuwa ne makonni kadan bayan makamancinsa a yankin Bassa da Bokkos inda aka kashe sama da mutum dari ciki har da mata da kananan yara.
Hare-haren dai sun biyo bayan rahoton harbe-harbe da kuma kashe dabbobi ta hanyar guba a yankunan kananan hukumomin Bassa da Riyom da kuma Mangu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Barikin Ladi hari
এছাড়াও পড়ুন:
An Kama Amarya Kan Zargin Kashe Mijinta Bayan Kwana 9 Da Aurensu A Kano
Lamarin ya tayar da hankali a unguwar, inda wasu matasa suka yi yunƙurin kai farmakar Saudat.
Amma jami’an tsaro sun isa wajen a kan lokaci, suka ceci amaryar tare da kai ta wajen hukuma.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp