Dan takarar zaben maye gurbin Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Mazabar Chikum da Kajuru a jam’iyar APC Arc Sani A Abbas Sardaunan Chikum ya nada kwamitin mutane 7 domin raba tallafin karatu ga daliban yankin sa su 100 da suke karatun kimiyya da fasaha a manyan marantun Gwamnati.

Wannan wata manuniya ce game da kudurin Arc Sani Abbas na karfafa matasa ta bangaren ilimin don gobe su tayi kyau.

Babban aikin wannan kwamitin shi ne tantance daliban da suka cancanci amfana da wannan tallafin musamman wadanda babu ke barazanar hana su karatu. Wanda yin haka zai taimaka wajen tallafa musu su nemi ilimi don cike gibin da ake samu ta wannan bangaren.

Wannan tallafin kadan ne daga cikin irin manofofin da yake da su ba ga al’ummar sa ba, yana nuna cewa yana son ganin an sami al’umma mai ilimi.

‘Yan kwamitin sun hada da Hon. Dauda Abdulkadir Kujama a matsayin shugaba Sai wakilan kwamitin da suka hada da Hon Ibrahim Garba Danmajen Chikun da Hon. Ibrahim Umar.

Sauran su ne Mrs. Rebecca Akapson da Hon. Daniel Sisin Kobo

Saifu Adamu Bawa Kajuru sai Hon. Ganaka James Kogi da aka ba sakataren kwamitin.

 

Wanda ke bukatar samun wannan tallafi sai ya sauke wannan takarda ya cika ya kawo.

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Uwargidan Tinubu Ta Bai Wa Mata Manoma Tallafin Naira Miliyan 26 A Nasarawa

Ta ce tallafin zai taimaka wajen bai wa mata damar zama masu dogaro da kansu a fannin tattalin arziƙi.

An raba kuɗin ne ga kungiyoyin mata manoma daga ƙananan hukumomi 13 a faɗin jihar, inda kowacce ƙungiya ta samu Naira miliyan biyu.

Haka kuma, ƙungiyoyin matasa manoma su ma sun amfana da tallafin don bunƙasa ayyukansu.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Masarautar Hadejia Ta Raba Zakka Ta Kimanin Naira Miliyan 63 Ga Mabukata
  • Fitar Da Nama Zuwa Saudiyya: Mayankar Dabbobi Ta Jurassic Ta Yi Hadin-gwiwa Da Shirin CDI
  • Na Cire Tallafin Mai Ne Domin Kare Makomar Matasan Nijeriya —Tinubu
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [7]
  • Kudirin Hana INEC Yin Rajista Da Daidaita Lamuran Jam’iyyu Ya Tsallake Karatu Na Biyu
  • Gwamnatin Jigawa Da Bankin Duniya Sun Dauki Nauyin Dalibai 500 A Fannin Fasahar Zamani
  • Gidauniyar Dangote Ta Kaddamar Da Rabon Abinci Na Naira Biliyan 16 Ga Talakawan Nijeriya
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Hada Gwiwa Da Jami’ar Azman Don Inganta Ilimi A Jihar
  • Uwargidan Tinubu Ta Bai Wa Mata Manoma Tallafin Naira Miliyan 26 A Nasarawa
  • Gidauniyar Bafarawa Ta Rabawa Kananan ‘Yan Kasuwa Naira Milliyan 13 a Sokoto