Rundunar Yemen Zata Kakaba Takunkumi Kan Jiragen Saman Fasijan Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Published: 5th, May 2025 GMT
Sojojin Yemen sun sanar da killace sararin samaniyar Falasdinawa da yahudawan sahayoniyya suka mamaye
Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Lahadi cewa: Za su kakaba wa haramtacciyar kasar Isra’ila cikakken takunkumi ta sama, yayin da kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa suka yi gargadin hadarin da ke tattare da zirga-zirga daga filayen jiragen saman yankunan Falasdinawa da aka mamaye.
Kakakin rundunar sojin Yemen, Birgediya Janar Yahya Sari’e, ya ce za su kakaba takunkumin ne ta hanyar kai hare-hare akai-akai kan filayen jiragen saman haramtacciyar kasar Isra’ila, musamman filin jirgin sama na Ben Gurion.
Sanarwar ta yi gargadi ga dukkan kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa kan hadarin da ke tattare da hakan, inda ta yi kira gare su da su “soke dukkan tafiye-tafiyen jiragen da ke zuwa filayen jiragen sama na gwamnatin ‘yan mamaya masu tafka muggan laifuka domin kare lafiyar jiragensu da na kwastomominsu.”
Birgediya Janar Sari’e ya jaddada cewa: Kasar Yemen ba za ta amince da ci gaba da keta hurumin da makiya ke kokarin aiwatarwa ta hanyar kai wa kasashen larabawa irinsu Lebanon da Siriya hari ba, yana mai jaddada cewa “wannan al’ummar ba za ta ji tsoron bullar duk wani fada ba, kuma za ta ki mika wuya da rusuna wa azzalumai.”
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: jiragen sama
এছাড়াও পড়ুন:
Gaza : Kungiyar Euro-Med ta bukaci a binciki harin Isra’ila kan jirgin ruwan Freedom Flotilla
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-Mediterranean (Euro-Med) ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai kan wani jirgin ruwan Freedom Flotilla da ke dauke da kayan agaji zuwa zirin Gaza da aka yi wa kawanya.
An kai harin ne a ruwan kasa da kasa kusa da Malta.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Euro-Med ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa da gaskiya a karkashin ikon Malta, tare da halartar Majalisar Dinkin Duniya.
Kungiyar mai hedkwata a birnin Geneva ta jaddada cewa dole ne a hukunta wadanda suka aikata irin wannan ta’asa.
Kungiyar ta kara da cewa “Hare-haren da aka kai kan jirgin ruwan farar hula da gangan a cikin ruwa na kasa da kasa, ya zama cin zarafi ga Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya, da dokar teku da kuma yarjejeniyar Roma, wadda ta haramta kai hare-hare kan abubuwan jin kai,” in ji kungiyar, inda ta kara da cewa rashin daukar mataki zai kara karfafa kai hare-hare kan ayyukan jin kai da kuma kara ta’azzara bala’in da ke kunno kai a Gaza.
Wannan harin dai wani bangare ne na yin amfani da karfi da aka saba yi, domin hana jiragen ruwan jin kai isa zirin Gaza, tun ma kafin su tunkari gabar tekun.
A halin da ake ciki kungiyoyin gwagwarmayar Palasdinawa na Hamas da Islamic Jihad sun yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan jirgin ruwan na ‘Freedom Flotilla’, suna masu bayyana hakan a matsayin na ‘yan fashin teku da kuma “keta dokokin kasa da kasa.”