An Yi Kira Da A Dauki Kwakkwaran Matakin Magance Rashin Tsaro
Published: 4th, May 2025 GMT
Bishop Joseph Osifuwa, Bishop na jihar Kwara, ya ce Nijeriya za ta iya magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a sassan kasar nan idan har ta dauki matakin magance masu tada kayar baya.
Bishop Osifuwa ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen babban taron cocin karo na 35 a Ilorin.
A cewarsa, magance rashin tsaro bai kamata ya zama matsala ga kasar da ta hada karfi da karfe a ayyukan wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa domin murkushe ‘yan tawaye ba.
Ya kuma shawarci gwamnati da kada ta rinka yi masu tada kayar baya ta hanyar yi musu afuwa, ya kara da cewa kada gwamnati ta tausayawa ‘yan tada kayar baya da ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane.
Bishop Osifuwa ya bukaci gwamnati da ta rufe idanunta ta magance su, inda ya ce su mutane ne ba basu da imani.
Ya zargi gwamnonin jihohi da tabarbarewar tattalin arzikin ‘yan kasa, yana mai cewa gwamnonin na rashin adalci ga jama’arsu.
Malamin ya ce gwamnonin na karbar makudan kudade a kowane wata daga Gwamnatin Tarayya ba tare da wani tasiri da ya yi daidai da rayuwar mutane ba.
Bishop Osifuwa, ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu kan sakin kudi ga gwamnonin jihohi.
Ya yi kira ga shugabannin siyasa da na addini da su inganta hadin kai, yana mai gargadin cewa kabilanci ko addini na iya kawo barazana ga zaman lafiya da ci gaba.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
Gidauniyar TY Buratai Ta Yi Kira Ga Tinubu Ya Ƙarawa Ma’aikata Albashi
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp