Yemen Ta Kai Wa HKI Hari Da Makami Mai Linzami Na “Falasdinu 2”
Published: 3rd, May 2025 GMT
Sojojin kasar ta Yemen sun sanar da kai wa yankin Yafa hari da makami mai linzami da ya fi sauti sauri mai suna ” Falasdinu 2″, tare da tabbatar da cewa, ya fada inda aka harba shi.
A yau Asabar ne dai sojojin na Yemen su ka kai wa HKI harin da makami mai linzami mai tsananin sauri bisa abinda su ka kira da cewa; Mayar da martani ne akan ci gaba da yakin da yakin da ‘yan sahayoniya suke ci gaba da kai wa Gaza, da kuma jefa yankin cikin yunwa.
Kakakin sojan kasar Yemen, janar Yahya Sari, ya bayyana cewa; Makami mai linzamin da aka yi amfani da shi sunashi; “Falasdinu 2” kuma ya isa inda aka harba shi.
Janar Yahya Sari ya kuma ce: Dukkanin al’ummar musulmi ne suke da alhakin yin shiru akan abinda yake faruwa a Gaza, da kuma kin taimaka musu, sannan kuma ya ce: Ko ba dade-ko bajima, samamakon yin shiru akan wuce gona da irin ‘yan sahayoniya zai isa cikin sauran kasashe.”
Janar Sari ya kuma ce; Gaza, tana kare dukkanin al’umma ne a wannan lokacin, domin taimaka mata shi ne ya fi dacewa da a tsumayi lokacin da sharri zai isa gidan kowa.”
Da safiyar yau Asabar ne dai jiniyar gargadi ta kada a yankuna da yawa na HKI da su ka hada yankin Kudus, Tel Aviv da kuma ” “Dead Sea” bayan da aka harbo makami mai linzami daga kasar ta Yemen.
Makamin na dazu dai ne karo na uku da sojojin Yemen su ka harba a cikin sa’o’i 24.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rundunar PLA Ta Yi Sintiri A Yankin Tekun Kudancin Sin Cikin Shirin Ko Ta-Kwana
Rundunar sojin kasar Sin (PLA) ta yi sintiri a yankin tekun kudancin Sin daga ranar 3 zuwa 4 ga wata.
Kakakin rundunar PLA ta kudancin kasar Tian Junli ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin ta dauki matakin ne biyo bayan matakan Philippines na sanya kasashen dake wajen yankin cikin abun da ta kira da sintirin hadin gwiwa, wanda ke neman lalata zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin.
A cewarsa, dakarun rundunar ta kudancin kasar za su ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana da kare ikon kasar kan yankunanta da muradunta na teku ba tare da yin kasa a gwiwa ba, yana mai cewa za a dakile duk wani matakin soja dake nemen tada hankali da rikici a yankin. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp