‘Yansanda Sun Daƙile Yunƙurin Yin Garkuwa Da Mutane A Katsina
Published: 5th, May 2025 GMT
“A ranar 2 ga Mayu, 2025, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne dauke da makamai sun kai hari kan wani Abu Iro, wani matashi dan shekara 23 a karamar hukumar Faskari, inda suka Sara masa Adda a kokarinsu na tafiya da shi.
“Bayan samun rahoton, cikin gaggawa tawagar jami’an ‘yansanda tare da kungiyar tsaro ta cikin al’umma ta jihar Katsina (KSCWC), karkashin jagorancin babban jami’in tsaro na Faskari, suka amsa kira, inda suka dakile yunkurin yin garkuwa da mutane, tare da samun nasarar kubutar da wanda aka sace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Zulum ya roƙi Gwamnatin Tarayya ta kai wa Marte ɗauki
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan da suka dace domin ganin cewa garin Marte bai koma hannun ’yan Boko Haram ba.
Zulum, ya kai ziyara garin Marte domin duba halin da ake ciki da kuma yadda za a tabbatar da zaman lafiya.
Mawaƙan APC sun zargi gwamnatin Jigawa da yin watsi da su Yadda Boko Haram ta kashe manoma 90 a Borno cikin wata 5Kafin zuwansa, ’yan ta’adda sun sake karɓe iko da Marte bayan harin da suka kai a ranar Juma’a, inda mutane da dama suka tsere zuwa garin Dikwa.
Gwamnan, ya ce mutane kimanin 20,000 ne suka tsere daga Marte, wanda hakan ka iya kawo matsala musamman ga matasa da za su iya shiga cikin harkokin ta’addanci.
Ya ce: “Muna da alhakin kare Marte. Idan muka rasa wannan gari, za mu iya rasa sauran ƙananan hukumominmu.
“Don haka ina roƙon Gwamnatin Tarayya da sojojin Najeriya su haɗa hannu wajen kare wannan gari.”
Zulum, ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro domin kawo zaman lafiya mai ɗorewa a Jihar Borno.