Ɗan shekara 19 da ya ƙirƙiro na’urar gano bam cikin daƙiƙa ɗaya
Published: 4th, May 2025 GMT
Khalifa Aminu, matashi ne mai shekaru 19 wanda ya ƙirƙiri na’urori da abubuwan ban mamaki waɗanda hatta mutanen da suka zurfafa karatu a fannin kimiyya da kere-kere ba su sami irin wannan nasarar ba.
A tattaunawarsa da Aminiya, Khalifa wanda ya ce da kyar ya iya kammala karatunsa na sakandare, ya bayyana yadda ya kirkiro wata sabuwar na’ura da ke iya gano ma’adinan karkashin kasa ko bam a cikin dakika guda, da kuma tabarau da ya kirkiro mai taimaka wa makafi wajen yin tafiya ba tare da sun yi karo ko sun fada cikin wani hadari ba.
Ɗan asalin Jihar Kano, a makon da ya gabata tsohon Farfesa a fannan fasahar tsaron intanet kuma tsohon Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, ya gayyace su ya tattauna da shi, kuma ya yaba da fasahar matashin da nagartar abubuwan da ya kirkiro da suka hada da gidan rediyo da na’urar manoma da na’urar tantance yanayin zafi ko sanyi da masu tantance wuta ko hayaki.
Khalifa Mai Gilashin Makafi, kamar yadda wasu ke kiran sa, ya bayyana mana yadda yake kwana yana gudanar da bincike, domin cika burinsa na kirkiro abubuwan da za su kawo wa al’umma sauki a rayuwarsu ta yau da kullum.
Ya kuma ba mu labain yadda ya faro wannan harka, sannan ya siffanta mana yadda sabuwar na’urarda ya kirkiro take aiki, da kuma burikansa a nan gaba da dai sauransu.
Za mu so ka gabatar mana da kanka da takaitaccen tarihinka
Sunana Khalifa Aminu, wanda aka fi sani da mai gilashin makafi. Ni dan Kano ne, an haife ni a unguwar Gobirawa da ke Karamar Hukumar Dala.
Tun ina karami na taso da sha’awar harkar kere-kere, har na zo na fara kirkirar wadannan abubuwan.
Bangaren karatu fa, a wane mataki kake yanzu?
Na yi makarantar firamare mai suna Abba Naliti, sai Sakandaren Gwamnati ta Gwammaja, a nan na yi karamar sakandare.
Na fara babbar sakandare ma a nan, amma saboda halin yau da gobe ban iya kammalawa ba a can. To tun a lokacin na ci gaba da kere-kere inda har na hada gidan rediyo.
Sannan tun a lokacin Gwamnatin Jihar Kano ta biya min kudin makaranta domin na samu na kammala sakandare.
Tun a lokacin Gwamna ya sa aka kai ni wajensa, ya zanta da ni ya ji dadi, har ma ya yi min wasu alkawura, ko da yake ba a samu cika su ba a lokacin sakamakon gwamnan na cikin hayaniyar shari’a a kotu.
Amma akwai wani Darakta da ya biya min wata makaranta mai zaman kanta da ke Airport Road a nan Kano, ita ma dai ban iya kammala ta ba saboda dawainiyar yau da kullum, sai da na sake samun wani ya biya min wata makarantar na samu na zana jarrabawa har na kammala a can.
Tun kana shekara nawa ka fara wadannan kirkire-kirkiren?
Gaskiya kusan ba zan iya cewa ga yawan shekarun ba, amma dai abu ne da na san kawai na taso na ga kaina ina yi.
La’akari da karancin shekarunka da yadda ka ce ka yi gwagwarmaya kafin ma ka kammala sakandare, mutane za su yi mamakin a ina ka koyi wadannan abubuwan?
Eh to, gaskiya kusan tun kafin ma na fara karatun nake yin wadannan abubuwan. Na fi mayar da hankali ne a fannin bincikebincike.
Duk abin da nake son yi nakan zurfafa bincike a kai har sai na gano na hada shi. Ban mu karanci harkar a aji ba, sai dai yanzu da nake kwadayin fara karantar ta. Ko lokacin da na kirkiri gilashin makafi ban fara karantar bangaren ba, bincike ya fi yawa.
Wadanne hanyoyi kake bi wajen yin wadannan binciken?
Sakamakon ci-gaban da aka samau yanzu, bincikena a yanzu ya ta’allaka kacokam da intanet. Nakan yi amfani da shafuka irin na su Google da fasahar AI da dandalin Youtube da sauransu. Lokacin da ka kera gilashin makafi kusan shi ne lokacin da sunanka ya yi tambari a duniya.
Kafin shi ko ka taba kera wasu abubuwan?
Tabbas, ko kafin wannan na kirkiri abubuwa kamar gidan rediyo da na’urar manoma da na’urorin da ke tantance zafi ko sanyi da wadanda ke tantance wuta ko hayaki, irin dai kananun na’urori kamar haka. Da su na fara. Bayan nan shi ne na kirkiri wannan gilas din makafin.
Yaya wannan gilashin makafin yake aiki?
Tabarau ne kamar wanda ake sanyawa a fuska, kawai dai bambancin shi ne shi yana da wasu na’urori da suke gano abubuwa sannan su ankarar da mai larurar gani cewa akwai wani abu a wajen ta hanyar yin kara, ta yadda idan ya tsaya sai karar ta tsaya.
Amma idan bai tsaya ba sai gilashin ya ci gaba da karar don kada mutum ya buge da abin da yake tunkara.
A nan gaba kuma wadanne abubuwan kake da burin kirkira?
Suna da yawa, amma sannu a hankali ina ta kokarin fito da su, musamman yanzu akwai abin da na yi na kirkiro na’urar da za ta gano bam da ma’adinan karkashin kasa.
Yaya wannan na’urar take aiki ita kuma?
To wannan ita ce irinta ta farko da aka kirkira a Najeriya kamar yadda yanzu ake ta magana a kanta. Ana iya amfani da ita wajen gano abin fashewa kamar bam ko kuma ma’adinan karkashin kasa irin su zinare, kuma a cikin dakika daya kacal.
Idan aka yi amfani da na’urar, muddin akwai ma’adinin karkashin kasa ko kuma an dasa bam a wajen, za ta iya ganowa.
Tun farko me ya ja hankalinka har ka yi tunanin kirkirar wannan na’urar?
Babban abin da ya ja hankalina shi ne yadda wasu masu hakar ma’adinai a Najeriya ke shan wahala sosai wajen gudanar da harkokinsu, ita kuma na’urar turawa tana da matukar tsada, ba sa iya saye.
Wata takan kai kusan miliyan uku zuwa biyar. Amma na kuma zan iya samar da ita a kasa da haka, sannan tana iya gano abin da ake nema a cikin dakika daya.
Yanzu a wanne matakin kammalawa wannan na’urar take?
Na riga na kammala kuma tuni ma na gwada ta kuma ta bayar da abin da ake nema.
Banda abubuwan da ka kirkira ya zuwa yanzu, nan gaba kuma me kake burin kirkira?
Akwai abubuwa da yawa, har irin na’urar watsa shiryeshirye ta gidajen rediyo da sauran abubuwan da za su kawo wa al’umma sauki ina da burin kirkira.
Har kullum babban burina shi ne na kirkiro abubuwan da za su kawo wa al’umma sauki a rayuwarsu ta yau da kullum.
Yaya kake iya raba lokacinka tsakanin kirkira da sauran ayyukan gida musamman kasancewarka matashi?
Gaskiya Alhamdulillahi, a gida ana ware min lokacin bincikebincikena ba tare da takura ba, musamman yanzu da nake wannan binciken, an ma ware min wajen da nake zama ina harkokina da bincike a ciki.
Wani lokacin har kwana nake yi ina bincike. Gaskiya a yanzu ba ni da wani aiki da ya wuce ko dai ina kan littafi da biro ina bincike can, kirkiri nan, hada wancan da wannan da dai sauransu.
Ke nan akwai wani wuri da aka ware maka da kake kebance kanka domin yin aiki a gidanku?
Eh, gaskiya a gida dai babu, amma akwai wanda na samu ya bude min wani kamar ofis da nake zama a ciki ina harkokina a can, da kayan aiki da komai domin ci gaba da ayyukana.
Shin kai kadai kake harkokin naka ko kana da wasu yara ne ko abokan aiki da suke taya ka?
Tun farkon da na fara har zuwa yanzu gaskiya ni kadai nake komai nawa. Ko shawara zan nema nakan yi amfani da intanet ne ko AI kawai, kuma suna taimaka min sosai, amma dai ni kadai nake yi.
Tun da ka ce ba karantar harkar ka yi ba, ko kana da burin komawa makaranta domin zurfafa bincike a kai?
Sosai ma kuwa. Kuma abin da nake son karanta idan Allah Ya yarda shi ne fasahar kere-kere, wanda ake kira da Mechatronics a turance. Ina son na karance shi domin fanni ne da ya kunshi harkar Electronics da kuma Engineering.
Ko akwai kalubalen da kake fuskanta ko a gida ko kuma daga al’umma?
Dole duk wata harka ta rayuwa ba za a raba ta da kalubale ba. Babban kalubalen da nake fuskanta dai bai wuce na rashin kayan aiki ba. Idan aka samu kayan aiki za a yi abubuwa masu yawa.
To babban kalubalen gaskiya shi ne rashin samun manyan kayan aiki, wanda ina fatan idan na same su, abin da zan yi zai iya wuce haka.
A gida fa? Ba sa yi maka kallon kamar kana bata lokacinka?
A’a gaskiya babu wannan, suna ma taimaka min daidai gwargwado.
Wadanne irin nasarori ka samu tun bayan fara wannan harkar?
To Alhamdulillah, an samu kyaututtuka da dama na girmamawa musamman daga kamfanoni, ina alfahari da hakan.
Ko a kwanan nan na je Babban Birnin Tarayya Abuja domin kara samun shawarwari domin bunkasa harkokina domin na dada samun ci-gaba, ta yadda za a yi wa kere-kerena kira ta musamman domin sayar da su a kasuwanni.
Wanne sako ko shawara za ka ba wa matasa masu shekaru irin naka?
Babbar shawarata gare su ita ce, matuƙar mutum ya san yana da wata baiwa da al’umma za ta amfana da ita, to ya yi ƙoƙari ya bayyana ta, domin ya taimaki kansa kuma ya taimaki al’umma har ya gina kansa da ita.
Musamman la’akari da yanayin kasar tamu da za ka ga mutum yana da baiwa amma bai damu da ita ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: karkashin kasa da ya kirkiro abubuwan da
এছাড়াও পড়ুন:
Layukan Dogo Na Kasar Sin Sun Gudanar Da Sufurin Miliyoyin Fasinjoji A Ranar Farko Ta Hutun ‘Yan Kwadago
Layukan dogo na kasar Sin sun gudanar da sufurin kusan fasinjoji miliyan 23.12 a jiya Alhamis, ranar farko ta bikin ranar ‘yan kwadago ta duniya da aka saba yi duk shekara a watan Mayu, kamar yadda kamfanin sufurin layin dogo na kasar Sin ya bayyana.
A cewar alkaluman da kamfanin ya fitar a yau Jumma’a, wannan adadi ya nuna karuwar kashi 11.7 cikin dari na adadin da ake samu a mizanin shekara-shekara. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp