Gwamnonin Tafkin Chadi Sun Yi Taro Karo Na 5 Don Magance Matsalar Yankin.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Za mu ci gaba da aikin haƙo ɗanyen mai a Arewa —NNPCL

Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya bayyana cewa zai ci gaba da aikin haƙa danyen mai a Arewa da ke yankin Kolmani.

Shugaban NNPCL, Bayo Ojulari ne ya sanar da aniyar kamfanin na ci gaba da aikin haƙar mai a yankunan arewa da gwamnatin Buhari da ta gabata ta fara.

Bayo Ojulari ya kuma addada aniyar NNPCL na kammala aikin bututun iskar gas da ya taso daga Ajaokuta a Jihar Kogi ya bi ta Abuja da Kaduna zuwa Kano (AKK).

A zantawarsa da kafar yaɗa labarai ta BBC, Injiniya Bayo ya ce, Za mu ci gaba da aikin haƙo mai a Kolmani da sauran wurare. Bayan aikin haƙo man, za mu kuma tabbatar da cewa mun gama aikin bututun man gas daga Ajaokuta zuwa Kano,” in ji shi.

An kama ɗan daba mai yin fashi a cikin shigar mata a Kano Boko Haram ta ƙwace makaman sojoji na tiriliyoyin naira —Majalisa

A cewarsa, ayyukan haƙar man da na bututun iskar gas ɗin AKK za su taimaka wajen farfaɗo da kamfanonin da aka rufe a baya domin su ci gaba da aiki sannan a buɗe wasu sababbi.

“Wannan zai amfanar da yankin Arewa ta yadda kowa zai ci moriyarsa saboda za a samu bunƙasar arziki,” a cewarsa.

Game da ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan naɗa, inda ake zargin Shugaba Tinubu da fifita ’yan yankin Kudu wajen rabon mukamai a gwamnatinsa, shugaban na NNPC ya ce, shi ma ɗan Arewa ne, kuma ya yi maganganu a lokacin da aka sanar da naɗa shi.

Don haka ya buƙaci al’ummar Arewa da ma ƙasar baki ɗaya da su ba shi goyon baya, kuma su taimaka masa da addu’a domin ya samu nasarar ciyar da yankin da ma ƙasar gaba.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Horas Da Likitoci Akan Magance Tsananin Zazzabin Cizon Sauro
  • Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe
  • Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka
  • Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Taro Na 4 Na Ministocin Dandalin CCF 
  •  An Bude  Taron Karawa Juna Sani Akan Makamashin Nukiliyar Iran Karo Na 31 A birnin Mashhad
  • Rikicin Ribas: Fubara Ya Ce Ya San Yadda Zai Magance Matsalar, Ya Gargaɗi Magoya Bayansa
  • NAJERIYA A YAU: Matsalar lantarki: ’Yan Najeriya sun yi tir da biyan diyya ga ’yan Band A
  • Za mu ci gaba da aikin haƙo ɗanyen mai a Arewa —NNPCL
  • Shugaba Xi Zai Halarci Bikin Bude Taron Ministoci Na Dandalin Sin Da CELAC Karo Na 4
  • Nijeriya Za Ta Karɓi Baƙuncin Taro Karo Na 4 Na Ƙananan Sana’oi Na Ƙungiyar AU