Zabe Babu Hamayya: Isma’il Dutse Ya Karbi Ragamar NUJ Jigawa
Published: 13th, May 2025 GMT
An zabi Comrade Isma’il Ibrahim Dutse na ma’aikatar yada labarai a matsayin sabon shugaban kungiyar ‘yan jaridu NUJ ta kasa reshen jihar Jigawa ba tare da hamayya ba.
A lokacin da yake sanar da sakamakon zaben, mataimakin shugaban kungiyar na kasa mai kula da shiyya ta daya wato Zone A, Comrade Tukur Umar Muhammad ya ce an kuma zabi Nura Sani Bello da Najib Umar da Aminu Umar Shuwajo ba tare da hamayya ba.
Tukur ya ce Aisha Abba Ahmed ta kamfanin dillancin labarai na kasa NAN dake Dutse ta samu nasara da yawan kuri’u 46, shi kuma Abdullahi Mukhtar ya sami kuri’u 34, yayin da Larai Musa na NTA ta sami kuri’u 14.
Tukur Umar, ya bayyana Aisha Abba Ahmed a matsayin wacce ta sami nasara a zaben da ta zamo sakatariyar kungiyar NUJ a jihar Jigawa.
Kazalika, Auwal Muhammad Kazaure ya samu nasara da kuri’u 69 akan Habibu Yusuf Adamu Babura wadda ya sami kuri’u 27.
A don haka, Mataimakin Shugaban na NUJ ya bayyana Auwal Muhammad Kazaure a matsayin ma’ajin kungiyar.
Sakataren kungiyar na shiyyar Zone A, Comrade Abdulrazak Bello Kaura ne ya rantsar da sabbin shugabannin nan take.
A jawabinsa, sabon shugaban kungiyar NUJ reshen jihar Jigawa, Isma’il Ibrahim Dutse ya bayyana zaben sa ba tare da hamayya ba a matsayin wani babban karimci da aka nuna masa.
Ya kuma yabawa masu ruwa da tsaki ciki har da Gwamna Umar Namadi bisa gudummawar da su ka bayar wajen samun nasarar zaben da aka gudanar cikin kwanciyar hankali da lumana.
Wakilinmu ya aiko mana da rahoton cewar, wadanda su ka halarci taron, sun hada da kwamishinan yada labarai, al’adu da matasa, Alhaji Sagir Musa Ahmed, da tsoffin shugabannin kungiyar, Alhaji Sabo Abdullahi Guri da Alhaji Mati Ali da wakilan sakataren Gwamnati da na shugaban ma’aikata da kuma Shugaban gidan Radiyon Tarayya Horizon FM, Dr Musa Idris Barnawa.
Kungiyar dai ta gudanar da taro karo na 8 wanda ya wakana a sakatariyar kungiyar da ke Dutse, babban birnin jihar.
Bayan kammala zaben, Shugabannin Kungiyar ta kasa, sun kai ziyarar ban girma gidan gwamnatin jihar domin gabatar da sabbin shugabannin kungiyar na jihar ga babban jami’in yada labarai na Gwamnan Jihar, Hamisu Mohammed Gumel.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
An Yi Girgizar Kasa Mai Daraja 5 A Ma’aunin Richter A Kasar Habasha
An yi girgizar kasa mai karfin daraja 5.7 a ma’aunin Richter a kasar Habasha a jiya Asabar.
Cibiyar dake kula da ilimin kasa ta kasar Jamus ta bayyana cewa, an yi girgizar kasar ne da zurfin kilo mita 10 a karkashin kasa.
Girgizar kasar ta Jiya dai tana cikin jerin girgizar da aka yi ne a cikin kasar ta Habasha a lokuta mabanbanta a wannan shekarar. Sai dai kuma a wannan loakcin ana tsoron cewa za a iya fuskantar aman duwatsu a cikin yankunan da girgizar kasar ta afku.
Daga farkon wannan shekarar zuwa yanzu an yi girgizar kasa har sau 29 a cikin kasar ta Habasha, da karfin wasu daga cikinsu ya wuce daraja 5.
A ranar 3 ga watan Janairu an yi girgizar kasa har sau 11 a rana daya sannan kuma dutsen Dopin ya yi aman wuta.
Yankin Fantali na kasar Habasha yana cikin wuraren su ka fi fuskantar aman duwatsu a tarihin kasar. A 1820 an yi wasu jerin girgizar kasa wanda ya aman wuta ya biyo baya.
A halin yanzu dai hukumomin dake kula da kasa, suna ci gaba da sa ido akan abubuwan da suke faruwa tare da yin gagradin ga mazauna yanki da su kasance cikin fadaka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta October 12, 2025 An Yi Musayar Wuta A Tsakanin Masu Tsaron Iyakokin Kasashen Afghanistan Da Pakistan October 12, 2025 Afirka Ta Kudu Ta Ce Babu Wata Makarkashiya A Mutuwar Jakadanta A Kasar Faransa October 12, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Yunkurin Balair Na Yiyuwar Shiga Gwamnatin Gaza. October 11, 2025 Cuba Ta Bayyana Bada Kyautar Noble Ga ‘Yar Kasar Veunzuelas machado A Matsayin Abin Kunya. October 11, 2025 Kasar Indunusiya Ta Hana Tawagar wasan Jiminastik din Isra’ila Visar Shiga Kasarta October 11, 2025 Ammar Hakim Ya Gargadi Kasashen Yamma Da su Kiyayi Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Kasar. October 11, 2025 Sarkin Morocco Ya yi Magana Tun Bayan Barkewar Zanga-zanga A Kasar . October 11, 2025 Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Iran Ya Ja Kunnen Amurka Kan Taba Jiragen Dakon Man Kasa October 11, 2025 Bayan Yakin Kwanaki 12, Kifar Da Gwamnatin JMI Ya Fita Daga Zabin Makiya: Aref October 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci