He Lifeng Ya Gana Da Babbar Jami’ar WTO Ngozi Okonjo-Iweala
Published: 13th, May 2025 GMT
Mataimakin firaminsitan kasar Sin He Lifeng, ya gana da babbar jami’ar hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala, a daren jiya Lahadi a Geneva.
Yayin ganawar tasu, He ya ce, kamata ya yi mabambantan bangarori su daidaita bambancin ra’ayi da takaddama bisa shawarwari, kuma cikin adalci karkashin ka’idar WTO.
A nata bangare, Iweala ta ce, dole ne mambobin WTO su kare tsarin ciniki tsakanin mabambantan bangarori bisa tushen bude kofa da ka’idar hukumar, da ma kara tuntubar juna da ingiza hadin gwiwarsu a bangaren ciniki a duniya, ta yadda WTO za ta bayar da karin gudunmawa wajen hanzarta yin ciniki cikin ’yanci da dunkulewar harkokin ciniki a duniya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Sha Alwashin Rarraba Fasahohinta Na Ainihi Da Dabarunta Na Kirkire-Kirkire Tare Da Sauran Sassan Kasa Da Kasa
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya ce, kasarsa a shirye take ta rarraba fasahohinta na ainihi, da dabarunta na kirkire-kirkire tare da sauran sassan kasa da kasa. Li Qiang ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa na bude taron shekara-shekara, na sabbin jagorori karo na 16, wato dandalin tattalin arzikin duniya na lokacin zafi na Davos a takaice, wanda aka bude yau Laraba a birnin Tianjin na kasar Sin.
Li ya kara da cewa, Sin na da karfin gwiwa, da ikon wanzar da ci gaban tattalin arzikinta, tana kuma kara kaimin zama kasa mai babban matsayin samun kudin shiga, yayin da ake kara daga matsayin sayayya bisa kyakkyawan yanayi a kasar, wadda ita ce ta biyu a girman kasuwar sayayya a duniya.
Firaministan na Sin ya kuma yi kira ga kasashen duniya, da su aiwatar da managartan matakan bunkasa hadin gwiwa a fannonin raya tattalin arziki da cinikayya. Ya ce hakan na nufin rungumar matakai na hakika, don kare tsarin cinikayya cikin ’yanci, da cudanyar mabanbantan sassa, da goya baya ga daidaitaccen tsarin raya tattalin arzikin duniya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp