Iran Da Japan Sun Kara Zurfafa Dankon Zumunci Da Ke Tsakaninsu
Published: 14th, May 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya tattauna da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Japan na farko Hiroyuki Namazu a nan birnin Tehran a jiya Talata inda bangarorin biyu suka tattauna al-amuran da suka shafi kasashen biyu na harkokin kasuwanci da kuma wasu bangarori, sannan tare da tattauna irin sauye-sauyen da ake samu a yankin da kuma abinda ya zama lazimi ga kasashen biyu su yi a wannan halin.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasashen biyu sun kara jaddada bukatar kasashen su karfafa dangantaka da ke tsakaninsu.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Japan ya fada a taron kwamitin hadin guiwa na kasashen biyu kan cewa kasar Japan ta zabi zurfafa dangantaka da kasar Iran duk tare da matsalin lambar da Washington takeyi na nisansar kasar ta Iran.
Hamazu ya kammala da cewa Japan tana son fadada dangantakar tattalin arziki da JMI wanda suka hada da kasuwancin a bangarori daban-daban. Haka ma a bangaren tsaro da ya shafi yankin Asia gaba daya. Wannan dai yana faruwa ne a dai-dai lokacinda Washington ta kara kababawa kasar Iran sabbin takunkuman tattalin arziki a ranar litinin da ta gabata.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Direba ɗaya ya tsira a hatsarin tankokin dakon iskar gas a Zariya
A safiyar wannan Litinin ɗin ce aka wayi gari da wani mummunan hatsarin tankoki biyu na dakon iskar gas a Zariya, inda direba ɗaya kacal ya tsira da rai, yayin da wasu da dama suka ƙone ƙurmus.
Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe tara na safe, a kusa da shatale-talen Jirgin Sama Mota da ke titin Kaduna zuwa Zariya, daura da sabuwar Kasuwar Ɗan Magaji.
An kama mutumin da ake zargi da kashe jami’in sibil difens a Jigawa Ya ba wa alaramma kyautar motarsa saboda daɗin karatun Alkur’aniRahotanni sun nuna cewa motocin biyu sun gogi juna ne yayin da ɗaya ke ƙoƙarin wuce ɗaya, lamarin da ya haddasa kamawar wuta nan take.
An ji wata ƙara mai ƙarfi da ta tashi a lokacin haɗarin, lamarin da ya tayar da hankalin mazauna yankin.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, mutane da dama sun yi ta tserewa daga gidajensu domin guje wa abin da ka iya zuwa ya komo, yayin da kuma hayaƙi mai yawa ya mamaye hanyar da ya daƙile zirga-zirgar ababen hawa.
Jami’an tsaro da na kashe gobara sun kai ɗauki wurin domin ceto mutane, amma ƙarfin wutar ya hana su samun damar kaiwa kan motocin.
Shugaban Sashen Kula da Hatsari na Ƙasa (FRSC) reshen Zariya, Nasir Abdullahi Falgore, ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon goguwar motocin dakon gas ɗin biyu, saɓanin raɗe-raɗin cewa tsautsayin ya rutsa da wasu ƙananan motoci ƙirar Golf.
“Direban ɗaya daga cikin motocin ya tsira, kuma mun kai shi asibiti domin samun kulawa. Shi kaɗai ne zai iya ba da cikakken bayani idan ya samu sauƙi,” inji Falgore.
Shugaban Ƙungiyar Direbobi a Zariya, Malam Sa’idu Haruna, ya bayyana cewa ana yawan samun hatsari a wurin saboda yanayin kwana da titin yake da shi.
“Kusan duk wata biyu zuwa uku sai an sami hatsari a nan. Muna kira ga hukumomi su kawo ɗauki,” inji shi.
Haka kuma, shugaban bayar da agajin gaggawa na ƙaramar hukumar Sabon Gari, Abdul Malik Aminu, tare da na Zariya, Abdul’muminu Adamu, sun tabbatar da cewa ba a gama tantance adadin mutanen da suka rasu ba saboda akwai fasinjoji a motocin da ba a gano su ba tukuna.
DPO na ofishin Ɗan Magaji, CSP Auwalu A. Sani, ya ce aikinsu shi ne sanya ido don kare rayukan masu wucewa, amma bai bayar da ƙarin bayani kan hatsarin ba.