Wasu ma’aikatan lafiya biyu sun rasu, wasu da dama sun jikkata bayan motarsu ta taka bom a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri a Jihar Borno.
Ana zargin mayakan Boko Haram ne suka dasa bom din a wani hari da kungiyar ta kai a kan babbar hanyar a ranar Litinin.
Shaidu sun bayyana cewa, wadanda suka mutun suna zaune ne a gaban motar jigilar mangoro, kirar Toyota Hiace da ta dauko su daga Damboa zuwa Maiduguri.
Sun kara da cewa tashin bom din ya haifar da sabuwar damuwa game da lafiyar matafiya a kan hanyar.
Yadda ISWAP ta kashe sojoji ta kwashe makamai a sansanin soji a Borno ’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 5 a Filato Ya kashe abokinsa saboda hula a KanoWata majiya a karamar hukumar Damboa ta tabbatar da cewa mamatan jami’an Hukumar Ilimi na Karamar Hukumar Damboa ne.
Tuni jami’an tsaro suka killace yankin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin gano ainihin yadda lamarin ya kasance.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram Damboa zuwa Maiduguri Ma aikatan Lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Zulum ya roƙi Gwamnatin Tarayya ta kai wa Marte ɗauki
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan da suka dace domin ganin cewa garin Marte bai koma hannun ’yan Boko Haram ba.
Zulum, ya kai ziyara garin Marte domin duba halin da ake ciki da kuma yadda za a tabbatar da zaman lafiya.
Mawaƙan APC sun zargi gwamnatin Jigawa da yin watsi da su Yadda Boko Haram ta kashe manoma 90 a Borno cikin wata 5Kafin zuwansa, ’yan ta’adda sun sake karɓe iko da Marte bayan harin da suka kai a ranar Juma’a, inda mutane da dama suka tsere zuwa garin Dikwa.
Gwamnan, ya ce mutane kimanin 20,000 ne suka tsere daga Marte, wanda hakan ka iya kawo matsala musamman ga matasa da za su iya shiga cikin harkokin ta’addanci.
Ya ce: “Muna da alhakin kare Marte. Idan muka rasa wannan gari, za mu iya rasa sauran ƙananan hukumominmu.
“Don haka ina roƙon Gwamnatin Tarayya da sojojin Najeriya su haɗa hannu wajen kare wannan gari.”
Zulum, ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro domin kawo zaman lafiya mai ɗorewa a Jihar Borno.