Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Matsayin Kasarsa Na Rashin Sallama Hakkinta Na Makamashin Nukiliya
Published: 12th, May 2025 GMT
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata taba yin watsi da haƙƙinta na makamashin nukuliya na zaman lafiya ba a kowane yanayi
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Iran da gaske take yi wajen gudanar da tattaunawa domin neman cimma matsaya da zata gamsar da kowane bangare, amma neman yin watsi da cibiyoyin nukiliyarta ba abu ne da za a amince da shi ba.
A yammacin jiya Lahadi ne jami’an gwamnatin kasar Iran suka gudanar da wani taro karkashin jagorancin shugaban kasar Masoud Pezeshkian, inda ya jaddada aniyar gwamnatin kasar na kare nasarorin da Iran ta a fagen ayyukanta na zaman lafiya, yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taba neman mallakar makamin nukiliya ba, kuma ba ta nemansa a yanzu, kuma ba za ta nemi mallakar makamin nukiliya a nan gaba ba.
Shugaban na Iran ya kara da jaddada matsayar Iran kan wannan lamari: Suna da matsaya na akida, kuma a cewar fatawar Jagoran juyin juya halin Musulunci, neman makamin nukiliya haramun ne a addinance, to sai dai abin da ake gabatar da shi dangane da yin watsi da dukkanin cibiyoyin nukiliyar Iran abu ne da ba za a taba amince da shi ba, ire-iren gagarumar nasara da Iran ta samu a fagage ilimummuka masu yawa misalin, samar da magunguna, harkar noma, kyautata muhalli, da bunkasa masana’antu, kuma zata ci gaba da ayyukanta na nukiliya na zaman lafiya da cikakken karfi.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Shugaban kasar
এছাড়াও পড়ুন:
Putin Na Rasha Ya Gana Da Shugabannin Afirka Akan Batun Tsaro
Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya karbi bakuncin shugabannin kasashen Afirka da su ka hada na Zimbabwe da na Burkina Fasa, inda su ka tattaunawa hanyoyin karfafa alaka a tsakanin kasashen nasu.
Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da na Burkina Faso Ibrahim Taraore sun isa birnin Moscow domin halartar bikin cika shekaru 80 da samun nasara akan ‘yan Nazi na Jamus a lokacin yakin duniya na 2.
Bugu da kari shugaban kasar ta Rasha ya kuma gana da shugaban gwamnatin kwarya-karyar Falasdinawa Mahmmud Abbas Abu Mazin,inda su ka yi musayar ra’ayi akan yadda za a kawo karshen kisan kiyashin da HKI take yi wa al’ummar Falasdinu.