HausaTv:
2025-05-14@15:21:06 GMT

Falasdinawa Sun Harba Wa HKI Makamai Masu Linzami

Published: 14th, May 2025 GMT

Rundunar “Sarayal-Kudus” ta kungiyar jihadul-Islami ta harba makamai masu linzami akan sansanonin ‘yan share wuri zauna na “Asqalan” da “Ushdud”.

A jiya Talata ne dai rundunar ta Sarayal-Qudus’ ta sanar da harba makamai masu linzamin kaan sansanonin ‘yan share wuri zauna, a matsayin ci gaba da mayar da martani ga hare-haren wuce gona da irin na HKI akan al’ummar Falasdinu.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta kunshi cewa: Harin nata yana a matsayin mayar da martani ne akan kisan kiyashin da HKI take yi wa al’ummar Falasdinu a Gaza.

A wani labarin na daban, rundunar “Kassam” ta kungiyar Hamas ta sanar da cewa ta yi taho-mu-gama da sojojin mamaya a unguwar “Shuja’iyya” dake gabashin birnin Gaza.

Sojojin HKI suna ci gaba da yi wa al’ummar Gaza kisan kiyashi, haka nan kuma killace yankin da hana shigar da kayan agaji da su ka hada abinci da magani.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Tawayen Sudan Sun Kai Hari Kan Gidan Yarin Al-Obeid Tare Da Kashe Fararen Hula Masu Yawa

Wani hari kan gidan yarin Al-Obeid yayi sanadiyyar mutuwa da jikkatan mutane da dama a kasar Sudan

Ministan al’adu da yada labarai, kuma kakakin gwamnatin Sudan, Khaled Al-Aiser, ya tabbatar da cewa: Mutane 20 ne suka mutu, yayin da wasu 50 na daban suka jikkata a wani harin da ‘yan ta’addar Daglo na  kungiyar Rapid Support Forces masu aikata laifuka suka kai hari kan gidan yarin Al-Obeid.

Al-Aiser ya bayyana cewa: Harin da aka kai ya hada da asibitin birnin, inda ya yi sanadin mutuwar mutane musamman majinyata masu yawa tare da raunata wasu kimanin 50, wadanda dukkansu fararen hula ne, yana mai cewa wannan yana daga cikin manyan laifukan yaki.

Ministan ya kara da cewa: “Abin da ya faru a gidan yarin Al Obeid, babban laifin yaki ne, wanda ya kara tabbatar da cewa: Dakarun Kkai daukin gaggawa na Rapid Support Forces da magoya bayansu ‘yan ta’adda ne da suke cin zarafin fararen hula a Sudan.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojojin HKI  Sun Sake Yin Kisan Kiyashi Mai Firgitarwa A Cikin Asibitin Gaza
  • ‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 239, Sun Ƙwato Makamai Da Alburusai A Kogi
  • Sin Tana Kara Kwatar Wa Kasashe Masu Tasowa ’Yanci
  •  Falasdinawa Da Dama Sun Yi Shahada A Yau Talata
  • Sin Ta Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Da Ake Iya Sarrafawa Daga Nesa
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Gudanar Da Kisan Kiyashi Kan Falasdinawa A Jabaliya Da Khan Yunus
  • ‘Yan Tawayen Sudan Sun Kai Hari Kan Gidan Yarin Al-Obeid Tare Da Kashe Fararen Hula Masu Yawa
  • NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC
  • Borrell : Rabin bama-baman da aka jefa a Gaza sun fito ne daga Turai