Aminiya:
2025-05-13@00:08:50 GMT

Kwalara ta yi ajalin mutum 4 a Filato

Published: 13th, May 2025 GMT

Ɓarkewar cutar kwalara ta yi ajalin mutum huɗu yayin da wasu gommai suka kwanta jinya a yankunan Ƙaramar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato.

Aminiya ta ruwaito cewa yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Hurti, Bokkos ta Yamma, Bokkos ta Tsakiya da kuma Mangol.

’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 5 a Filato Jami’ar Maryam Abacha ta rufe ɗakunan kwanan ɗalibai a Kano

Galibin waɗanda ake zargi sun harbu da cutar an killace su a cibiyoyin lafiya a matakin farko daban-daban da kuma Asibitin Cottage inda suke samun kulawar gaggawa.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Bokkos, Mista Amalau Samuel Amalau wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce suna aiki tare da mahukuntan asibitin domin daƙile ƙalubalen

A cewarsa, wasu daga cikin waɗanda ke fama da rashin lafiyar sun fara samun sauƙi yayin da tuni an sallami wasu daga asibiti.

Sai dai shugaban ƙaramar hukumar ya gargaɗi mazauna da su riƙa taka-tsan-tsan wajen kiyaye dokokin da mahukuntan lafiya suka shar’anta domin kaucewa kamuwa da cutar musamman tsaftace jiki, muhalli da kuma uwa-uba abinci.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Filato Kwalara

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisar Kaduna Za Ta Sanya Mutane 700 Cikin Tsarin Kiwon Lafiya Na Jiha

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Liman Dahiru, ya kaddamar da wani shiri na kiwon lafiya domin inganta kula da lafiya ga mazauna gundumar Makera.

 

Shugaban majalisar zai sanya mutane 700 da suka fito daga gundumar cikin Tsarin Kiwon Lafiya na Hadin Gwiwa na Jihar Kaduna (KADCHMA), matakin da ake sa ran zai kara yawan mutanen da ke da inshorar lafiya a yankin.

 

An yi hakan ne da nufin bai wa jama’a damar samun kula da lafiya mai inganci cikin sauki, domin inganta jin dadinsu baki daya.

 

A shirye-shiryen kaddamar da shirin, Shugaban Ma’aikata na Shugaban Majalisar, Honarabul Bashir Adamu Nababa, ya gana da Darakta-Janar na KADCHMA, Mallam Abubakar Hassan, inda suka tattauna kan muhimman matakai na aiwatarwa, sannan aka mika fom din rajista domin raba su ga wadanda aka zaɓa a cikin gundumar Makera.

A bayaninsu, jami’an shirin sun jaddada kudurin shugaban majalisar na ganin al’umma ta amfana, inda suka bayyana wannan tsarin kiwon lafiya a matsayin wata shaida ta jajircewarsa wajen yi wa al’umma hidima.

Ana sa ran cewa shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki na gundumar za su taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da gudanar da rajistar cikin sauki da gaskiya a cikin makonni masu zuwa.

 

Shamsuddeen Munir Atiku 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Kaduna Za Ta Sanya Mutane 700 Cikin Tsarin Kiwon Lafiya Na Jiha
  • ’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 5 a Filato
  • Cutar Cholera Ta Ɓarke A Filato, Mutane 4 Sun Mutu
  • NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO
  • Matakan da gwamnonin Arewa suke so a ɗauka kan matsalar tsaron yankin
  • Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Daban-Daban A Moscow
  • Sauya sheƙa bayan cin moriyar jam’iyya butulci ne — Kwankwaso
  • Jagora: Ma’aikata Su Ne Jari Mafi Girma Domin Cimma Manufar Bunkasa Tattalin Arziki
  • Noman 2025: Dole Ne Manoma Su Kiyaye Hasashen Hukumar NiMet