NAJERIYA A YAU: Matsalar lantarki: ’Yan Najeriya sun yi tir da biyan diyya ga ’yan Band A
Published: 13th, May 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Wasu ’yan Najeriya sun yi Allah-wadai da umarnin da Hukumar Kula da Harkar Wutar Lantarki a Najeriya (NERC) ta bai wa kamfanonin rarraba wutar da su biya diyya ga abokan huldarsu da ke rukunin Band A.
NERC ta bai wa kamfanonin wannan umarni ne sakamakon rashin samar wa ’yan Band A ɗin wutar lantarki na aƙalla sa’a 20 a kullum a watan Afrilu.
A cewar waɗanda suke kan rukunin Band B zuwa ƙasa, matsalar wutar ba ta keɓanci ’yan Band A kaɗai ba, galibi ma su suka fi ɗanɗana kuɗarsu saboda rashi wutar.
Ko me ya sa rukunin Band A ne kawai za su amfana da wannan diyya?
NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A NajeriyaWannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai bincika.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: diyya Lantarki Wutar Lantarki
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kwara Ta Yi Gargadi Ga Manoman Ruwan Malka Na Wata Agusta
Gwamnatin jihar Kwara ta gargadi manoma da mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa da su dauki matakan kariya cikin gaggawa domin ceto jarin da suke zubawa.
A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar noma da raya karkara, Ashaolu Omotola ya fitar, ya ce. Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya NIHSA, ta yi hasashen yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar Kwara tsakanin ranakun 7 zuwa 21 ga watan Agustan bana.
A cewar hukumar ta gano al’ummomi da dama a jihar daga cikin wurare 832 a fadin kasar da ke fuskantar hadarin ambaliya a wannan lokaci.
Ta ce ambaliyar ruwan da ake sa ran za ta iya tarwatsa hanyoyin sufuri tare da yin barazana ga filayen noma, amfanin gona, da kuma dabbobi.
Sanarwar ta yi gargadin cewa ambaliya na da matukar hadari ga noma da samar da abinci a fadin jihar.
Yana ba manoma shawara da su girbe amfanin gona da aka shirya cikin gaggawa, su mayar da dabbobi, injunan gona, da kayan aiki zuwa wuri mafi aminci, wurare masu tsauni, da tabbatar da kula da magudanan ruwa a gonakinsu don ba da damar kwararar ruwa.
Ta bukaci jami’an aikin gona da su kasance a shirye don tallafa wa manoma da kare kadarorin noma da rayuwa a tsawon wannan lokaci.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU