Sojojin HKI Sun Sake Yin Kisan Kiyashi Mai Firgitarwa A Cikin Asibitin Gaza
Published: 14th, May 2025 GMT
A jiya Talata sojojin HKI su ka kai wani mummunan hari akan asibitin Gaza na “Turai” da kuma zagayensa da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai da kuma jikkata wasu da dama.
Sojojin mamayar sun yi amfani da jiragen sama wajen kai wadannan munanan hare-haren akan Asibitin da ake kir ana turai, da kuma gefensa a kudu maso gabashin birnin Khan-Yunus.
Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; jiragen saman na HKI sun kai hare-haren ne ta hanyar harba makamai masu linzami akan bangare da kuma kula da matsalolin gaggawa na asibitin da kuma bangaren dake kula da asibitin da gyara abubuwan da su ka baci.
Haka nan kuma jiragen yakin na HKI sun kai wasu hare-haren a cikin sansanoni dake cike da Falasdinawan da aka raba su da gidajensu saboda yaki da suke daura da asibitin.
Gwamman Falasdinawa ne dai su ka yi shahada,kuma wasu gwamman majiyyatan suna a karkashin baraguzan gininin asibitin da ya fada a kansu.
Masu ayyukan ceto sun sanar da tsamo shahidai 28 da kuma wadanda su ka jikkata su 70,kamar yadda mai Magana da yawun kungiyar Muhammad Basal ya ambata.
Jiragen yakin HKI sun harba makamai masu linzami guda 6, da hakan ya haddasa rusau mai yawa akan ginin asibitin.
Tuni dai masu tafiyar da asibitin su ka sanar da cewa, ba za su iya karbar wadanda su ka jikkata ba.
An dauki marasa lafiya da kuma wadanda su ka jikkata zuwa asibitin “Nasir” wanda shi ma bangarensa mafi girma ya rushe.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Bincike Ya Tabbatar da Cewa HKI Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 Tun Bayan Fara Yaki A Gaza
Masu bincike sun gano cewa sojojin HKI sun kashe Falasdinawa akalla 100,000 tun bayan fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara 2023.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kan cewa farfesa Michael Spagat da kuma Khalil Shikaki Bafalasdine masanin masanin fasahar siyasa a Jami’ar London na kasar Burtania suka jagoranci bincike wanda ya kai ga fitar da wannan sakamakon.
Labarin ya kara da cewa masu binciken sun kiyasta mutane a gidaje 2000 a birnin Gaza kadai wanda falasdinawa kimani 10,000 suke rayuwa, sannan suka yi lissafi suka kaim ga wannan sakamakon.
Bincike ya kara da cewa daga watan jenerun shekara ta 2025 falasdinawa 75,200 sojojin yahudawan suka kashe da makamai, sannan wasu kimani 8,540 sun mutu sabada yunwa da karancin magunguna da kuma wasu hanyoyi ba da wuta ba.
Amma ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta bayyana cewa daga watan Jeneru zuwa yanzu sojojin yahudawan sun kashe falasdinawa 10,000.
Ma’aikatar ta kara da cewa a baya bayan nan sojojin yahudawa suna kashe Falasdinawa a wuraren karban abinci da suka shirya a matsayin tarko ga Falasdinawa wadanda suke fama daga tsananin yunwa.